Page 11

135 4 0
                                        

📗📗BURINA📗📘
PAGE 11

Da safe muka tashi muna hada hadar daurin aure , kowa tayi wanka ta saka Kaya tunda yau amarya kawai za ayi wa makeup , dukada haka Raina a jagule yake na ki sakin fuska, bakin cikina kudina Dana kashe Aman ba biyan bukata, su yesmen har sun gaji da tambayata sun yi shiru sunfi halakanta shirun nawa da mood swings ne

Karfe sha daya dai dai aka daura aure , abokanan ango suka zo aka sha hoto , Raina bai gama bacci ba Saida naji ankira kusan 1m a mastayin sadakin Zee , Nima da tuni nasamu wani mai kudin da nanda watani Nima haka za ayi bikina na kece raini sanan a mikamun makudan kudi a masayin sadaki na Aman kash inaji Ina gani mafarkina da BURINA Yana Neman tarwastewa.

Ko jira a kai amarya banyi ba nace ma su Zee banjin dadi zan koma gida , sunyi sunyi dani na zauna har a Kai amarya Aman nace ni su barni banajin dadi . Hka suka hakura Akan zanje wani lokacin .

Na hada kayana na tari napep sai gidan Anty saratu, a titi mai napep y ajiye ni kasancewa layin ko mota bata iya shiga saidai mashin ko ke ke , hka na tako har gidan ina tsaki, gidan madaidaicine Aman kana gani kasan suma lalaba rayuwa sukeyi yan gidan , naja tsaki ina mita yanzu kowa Yana Zuwa gidan yan uwansa masu arziki ya yi weekend Aman Kai saidai kazo gida kmar kejin kaji, Allah y sauwaka , gidan na shiga tareda da saallam, Anty saratu na tsakar gida tana yankan salad na ta amsa fuska a sake , kyakyawar mata kasancewa mamansu maman mu Fulani ne na asali, na kalleta Allah sarki Aman tazo ta auri talaka mama ma hka wlh Nikam bzan aura ba duk a cikin zuciyata nake fada , gaisawa mukayi sanan tace na shiga da Kayan ciki Tana tambyata y makaranta, Lfy qlw na bata amsa ina shige wa dakin yarta sa ar rahma suwaiba, ya yanta 2 kawai suwaiba yar shekara 16 sai umar dan shekara 6,

Anty ina su suwaiba na tamabaya ina fitowa daga dakin bayan na ajiye Kayan , sun tafi islamiyya yanzu nan , oh na manta Ashe yau lahadi, murmushi kawai tayi ta cigaba da yankan salad dinta muna dan taba hira , can tace mun Yauwa zaituna Ina usman kuwa , y kamata y fito a saka muku ko rana ce , yaron Yana kokari sosai ,Anty wasila wato mamanmu tace da gaske yake , usman kuma Anty na fada da sauri , eh mana shi ko yanada aibu ne, Kai na girgiza aa Aman aibun sa daya Anty , Toh Ina jinki Yana da wani dabi un ne da bashida kyau ? Ta tambya, still Kai na girgiza Aa aibun sa shine bashida kudi Anty , takala ne, bai ajiye ba kuma bai bada ajiya ba shine kawai , sakin Baki Anty tayi Tana kallona sanan tace haba zaitun Ina kaloon ki mai hankali Ashe bkida wayo , da arziki da rashin sa ae duka na Allah ne, da kike maganar bai Tara ba zance yayi karatu kuma Insha Allah saiki ga ysamu aiki y tara kuma y kula Dake , Nidai shawarata shine ki daina zancen yanada kudi ko aka sin haka ki bashi dama , juma ar da zatayi kyau tundaga laraba  ake ganeta usman Yana kokari akan ki ykmata ki nustu kiyi tunani Tom

Rausayar da kaina nayi alamun na ji Aman har a zuciyata banajin zan auri usman , babu abinda nake hasko wa sai auren mai arziki ba fakiri kaman usman ba

A dadafe na yi kwana 2 , ranar talata da yamma na hada. Kayana na tafi , nagaji da cin yar tsala da kunu da safe , shinkafa da wake da mai da yaji da rana sai tuwon masara da dare

Rnar laraba lectures din safe ne Dani tun safe na shirya na Kama hanyar makaranta, naira 200 baba yabani yau sabanin da yake bani 500 , Dan haka da baccin rai na fita Ina mita.

Usman nayi wa text da ina bukatar kudin mota yau baba bai bani ba , ae kuwa da sauri y kirani, yace Insha Allah zai kawo mun school kafin mu tashi , nace masa Toh Aman ya tabbatr y kirani kafin yazo ya amsa da Toh

12 na rana muka fito daga lectures din farko, muka biya cafeteria don samun abunda zamuci, ko sisi bnida shi sai naira 50 , gashi Zee din da take biya mana yau bata zo ba Tana amarci, hka Ina gani su yesmin suka bada order nikuwa nace ae na koshi yau breakfast mai nauyi nayi, sabanin yunwar dake damuna kmar naci babu

Kiran usman nagani y shaida mun da Yana gate , wani relief naji Saidai kuma yaya zanyi nayi excuse din kaina na fita batare da su yesmen sun bini ba Dan banso suka usman , bai Kai mastayin dazan nuna nasa a wajen kawayena ba nace saurayi na ne, Toh ni ya anyi ma yanzu , tashi nayi nace kafin ku gama bara na Dan je yin photo copy , no inji yesmeen jira mu zan karbi Abu Nima a cafe , yanzu zan gama , daram jikina ya bani , hka na zauna duk narasa mai ya kemun dadi .

Shikuwa usman y gaji ba zaitun ba dalilinta y kira taki oick haka y shigo ko Allah zaisa g ganta, Saidai Aa , tuna wa yayi da department dinsu dan haka y karasa can , wasu yan mata y gani suna hira da salama y karasa gurin su , amsawa sukayi sanan ya tambyesu dan Allah idan a department din library science suke suka amsa da level dinsu, da yar ce ta nuna dayar yarinyar eh ni library science nake a level 100 nke, Yauwa dan Allah wata zaitun nake tambaya , kana nufin zaituna muhd , yace eh , yeah I know her naganta da cafeteria itada friends dinta Ina tunanin Tana can , godiya y musu sosia sanan y nufi cafeteria din , y isa cafteria din sukuma su zaitun na fitowa

Sosai zuciyar zaitun ta buga da taga usman y masto gab da su , ta juya zata koma cafteria din don batasan yadda zatayi introducing din usman ba as what , talaka bayan. Ta yi musu karya da saurayinta mai kudi ne kuma a abroad ,

Suannta usman y kira zaituna Wanda yasaka ta tsaya cak , sukuma su yesmen suka shiga kalon kalon, waye wanan yake kiran kawar tasu haka .....

BURINA(HAUSA NOVEL)Where stories live. Discover now