📗📘BURINA📗 written by Khadija Mustapha
PAGE 22
Kaloon yussuf nayi idona cike da kwalla , yussuf Kai wanene kafadamun daman mamakin da kake cewa zaka bani daman abunda zan gani kenan , kallona yayi sanan yace rufe mun Bakin ki ke har zaki bude baki kina wanan maganar ba Wanda bai San kwdayi ne yasa kika yarda kika aure ni ba , meyasa Baki taba tambayata mahaifiyata ba eh ko Kane na, na kalle shi sai sai lokacin na tuna da wauta ta son kudi da burin auren mai kudi yasaka na manta hakan , yussuf ne ya cigaba da magana saboda son kudi ko da kwadayi ? Shiru nayi Ina kallonsa tabbas nayi babban kuskure , kallonsa nayi sanan nace masa komai zaka fada ka fada yussuf Aman wlh saika fdamun kai ko waye bazan yarda ba , kins so kisan ko ni waye , na gyada Kai eh , Toh zaki ji yau
Labarin yussuf
Ni dai sunana yussuf rabiu , mu yan asalin maiduguri ne ,bayan rasu war mahaifina maihaifjyata ta Debo mu ni da kanena mata uku muka dawo Kano , bara mahaifiyar mu ta fara yi damu ita da yar autar mu su ne suke zama cikin kasuwa mukuma mu shiga cikin gari bara , idan dare yayi mu je wani kango mu kwana washe gari mu cigaba da Baran mu , a haka mahaifiyata ta Tara kudi muka siya gida dan karami mai dauke da daki daya , Kap cikin mu daga ni har kanena Karima , badariya sai shamsiyya babu mai Zuwa makaranta daga boko har islamiyya, Ana hka mahaifiyar mu ta fara siyar da awara a bakin kasuwa , da sasafe zamu fita da yamma kuma mu dawo , abokina daya wani dan makotan mu muntari shi Aman yanz Zuwa makaranta kuma private , haka idan ydawo da yamma bayan mun dawo daga tallah zai zaunar Dani yana koya mun karatu dake inada saurin daukar Abu nan da nan na gane har na fara iya turanci da lissafi,
Islamiyya kuwa baban muntari ne y saka mu har kanena aman mamanu tace ba Wanda zaije ta gode , da kyar ta yarda ni kadai nake zuwa
A haka muka taso ba tarbiyya ba kwaba , komi girman mutum zamu masa rashin kunya babu abinda ya Dame mu , lokacin da nazama saurayi saina taso da kwadayin Tara abun duniya BURINA na tara kudi masu yawan gaske , nan nafara neman aiki a gidan manya nasha wahala kafin nasamu aikin gadi, a wani katon gida , nan nafara tunanin yadda zan samu kudi na masu gidan dan haka na yanke hukuncin fara soyaya da yarinyar gidan bintu , ba tareda da nasha wahala ba ta yarda dani muka fara soyaya ba tareda kowa ya sani ba , Saida na fuskanci bintu ta Kamu da sona komai na sata nasan zata mun nace inason na bar aikin gadi na fara nawa business din , Dana fadama bintu kuwa kin yarda tayi Saida da mata dadin Baki Akan idan gadi nake babanta bazai taba yarda muyi aure ba Aman idan nafara nawa business din na Tara nawa kudi zai yarda , haka na nayimata dadin Baki ta sato mun kudin mahaifinta 500k daya ajiye a dakin sa takawo mun Akan zan fara sana a, ranar da tabani kudin cikin dare na hada kayana nagudu navar gidan daga ranar bata kuma gani na ba har rana irin ta yau .
Bayan bintu tabani wanan kudin na Koma gida na fara tunanin samun wasu kudi nan dai na nemi shawara gurin muntari Akan wani kasuwanci zan fara Aman ban fada masa jarina nawa bane ko Wanda ya bani jarin
Muntari ne ya bani shawarar siyarda kayan mai na mata , sosai na Yaba da shawarar muntari , haka naje har Lagos na saro Kayan mai da supplement na fara siyar wa a sabon gari, a hka ba kalar yah matan da bana gani saikuma kwadayin auren mace mai kudi ya darsu mun a Raina ,
Nan dai ana nan watarana Allah ya hada ni da Hajiya Jamila wace take da gidan nan da muke ciki, ranar farko da tazo siyan mai muka yi exchanging contact Dan kowa ya Yaba da kowa , kafin wani lokaci muka kula soyaya , ranar da naje gidan hajiya Jamila naga irin gidan ta na alfarma Saida na tsorata, nanfa na rikice na , kwadayina ya tashi , hajiya Jamila ta dinga kashe mun kudi , a hka ta bijiro mun da magnar aure ae kuwa na amince, naje na sanar da mahifiya ta a farko taki yarda Aman Dana fadamata irin arzikin Hajiya Jamila , nan itama ta rikice ba Dan ba laifi mama ta har ta fini son kudi , haka akayi auren mu da hajiya Jamila ,
Nan da ya bude mun bakin aljihun ta , kasuwar ma na daina Zuwa daga baya ma na siyarda komai na shagon na saki shagon bnida aiki sai bacci da yawo da motocin hajiya jamila, a haka na hadu Dake , nasha Zuwa naga yadda kike ma usman tun kafin na fara Zuwa gurin ki , danayi bincike Akan ki aka sanar ni irin kwdayin ki na son auren mai kudi ,sainaga kece kika dace Dani don daga ni har ke gold diggers ne , duk kudin da nake kashe miki na hajiya ne , ranar da nace zan kawo kudi gidanku ranar munyi tafiya da Hajiya' ne sabanin Dana ce mki da mahaifina ne mukayi tafiya , ba wani company da nake dashi bana aikin fari bare na baki, can nabar Hajiya's Jamila a London dan haka na samu na aure ki nakawo ki gidanta ba tareda ita ta sani ba but thanks to you yanzu kinsa ta kore mu Aman bara kiji wlh saikin biya kuma na manta ban fadamki ba wanan da suka zo neman aure da kawo lefe kaf babu yan uwana a ciki hayan su nayi kuma yanzu dai bukatata ta biya .wanan shine tarihi na
Back to the story
Rawa jikina ya shiga yi , na Dora hanaye na a Kai na saki ihu da kuka , wlh bazan taba yafe maka ba yussuf azalumi kawai kuma wlh daga yau auren mu yazo karshe , na dau wayata zan kira mama , fusge wayan yayi ya cire layin ya karya , sanan y saka wayan a aljihun wandon sa , ya nuna ni da yasta zaitun ae keda ganin iyayen ki sai kin biya ni duk kudin Dana kashe a kanki bazan yi biyu babu ba , fita yayi ya barni gamida rufe dakin da key , gumi ne ya shiga karyo mun nafara salati gani komai nakeyi kamar a mafarki, wayoo Allah na ni zaituna wani irin rayuwa nsa kaina sabida kwadayi , can sai gashi da wasu mutane haka inaji Ina gani akayi cinikin Kayan daki na harda gadon aka bashi kudinsa y dana a aljihu, suka kwashe Kayan , mukuma yasa yara suka kwashe mana Kayan sawan mu da dan abun amfanin mu na yau da kullum suka saka a mota muka nufi hanyar barin gari har lefe na yussuf bai barmun ba haka ya siyar dagani sai kayana na sawa suma ba dayawa ba , kallon karshe nayi ma gidan Ina tunanin yadda rayuwa ta Chanza mun ni zaitun a cikin kankanin lokaci .

YOU ARE READING
BURINA(HAUSA NOVEL)
Viễn tưởngThis novel is about a young lady zaituna who was came from a poor background and Tries her possible means to fit in just to be with her friends who happens to be rich Sit back and enjoy 🩷