📗📗BURINA 📘📘written by Khadija Mustapha
Page 12
Cak na tsaya ni ban juyo ba kuma ni banyi gaba ba , yau nasan mutuncina sai y zube , kalon kalon su yesmen suka hau yi , zaitun what's wrong naji yesmen na tambaya na , juyowa nayi duk jikina na rawa , nace Ina Zuwa , karasa wa nayi Inda usman yake tsaye, zaitun Inata kita kinki picking , haka mukayi dakai na tambayeshi cikin fushi , Dan ji nake kamar na rufe shi da duka , sorry zaituna y a kuma maimaitawa , yanzu saboda ka bani kunya usman shine zaka zo nan bazaka ka jirani na Kiraka ba , zaka zo ka zubar mun da mutunci a gun kawaye na manyan yara haba wlh ni Baka kyauta mun ba , ban rufe bakin a ba su yesmen suka karaso hakan yasaka nayi shiru , ah Wai meyake Faruwa ne naji muryar ihsan na tambya, Aa na daburce daman yaran babanmu ne ne shine yazo Neman alfarma Wai yayi ma daddy laifi na bashi hakuri , mamaki ne ya cika usman Wanda y hanasa ma yin magana, mamaki duk ya cika shi , oh Nidai nace me kikeyi da wanan ta fada Tana kaloon sa kaloon raini da kaskanci, murmushin takaici usman ya saki , zaituna ce ta kalli usman sanan tace ya muje na Raka ka Insha Allah zan bashi hakuri , na kalli su yesmen zan dan salame shi zanzo na same ku , Kai suka gyada suna kare masa kallo tundaga kan sa har takalmin sa , muje nace sanan muka jera har gate , dagani har shi ba Wanda yayi magana har muka kusa karasa wa Gate sanan nace kaga usman don't take take it personal , kishi ne y saka nace ga yanda kake s gareni , kallona usman yayi idonsa yayi ja, na tababata baiji dadin abinda nayi masa ba , for the first time naji tausayin sa , hakuri na sake bashi, Kai kawai ya gyada alamun yaji, muna isa gate y fito da kudi a aljihu y mikamun gashi ya fada da muryarsa Wanda kana ji kasan Yana cikin baccin rai, karba nayi gamida godiya , sai anjima ya fada sanan yayi hanyar titi don samun abun hawa .Kirga kudin nayi 5k , nayi aji yar zuciya dan duk na tsorata duk zatona asiri na yau zai tonu, komawa cikin school nayi na tarar da su yesmeen , yesmen ce ta ke ta Yaba kyawun usman nikuwa ko a jikina , Kinsan da guy dinan yanada ya yan Baki da ba abunda zai hanani gwada sa a na but sadly I hate broke guys , bana kaunar talakawa Sam ta fada Tana bata rai kamar taga abun kyankyami,ihsan ce tace yes babes da ace yanada kudi Toh saina yaba A-man Yana fama da Kansa ba abunda zan gani sai talaucinsa suka tafa suna dariya ko ke zaitun kina ganin kyaun guy din , murmushi nayi lna girgiza Kai no Allah ya sauwake , dariya muka kwashe dashi su ihsan na yima Kayan jikin sa dariya da wayansa da suka gani dayashi jiki duk ya kode (Allah sarki Bawan Allah )
A bangaren usman kuwa tunda ya bar school din su zaitun , ya wuce gida baima biya makarantar da yake koyarwa, he left everything he was doing just to make zaitun happy Aman ta masa rashin mutunci, ta kirasa da dan aiken baban su , sosai ransa ya baci kuma ya kudiri niyya daga yau zai hakura da zaitun Saidai kuma me zuciyar sa taki basa Hadin kai , maimakon ya ji ya tsane ta saima sonta yaji ya karu kuma Yana Neman excuse din dazai bata Akan abunda tayi masa .
Lokaci yaja har munyi exams din first semester mun tafi Hutu ,bangaren usman kuwa tun ranar da nayi ma usman rashin mutunci , ya dan ja baya dani , da zai kirani kmar sau 5 a rana Aman yanzu baifi ya kirani sau 1 ba , nikuwa ban damu ba rayuwata nake kuma har yau ban cire ran samun saurayi mai arziki ba .
Yau tun da wuri na tashi sabida yau mukayi zamuje gidan Zee , daman ni ban taba zuwa ba Dan haka sai zumudi nakeyi , Na kagu naga irin dukiyar da aka zuba mata a gidan
Karfe 2 na fito cikin wani Atamfa mai kyaun gaske Dana Yiwa Maryam amarya karyar ta aramun style din , nikuwa saka wa zanyi sabida kayana duk sun fara fading , naci kwaliyya sosia idan ba Wai kasan ni bane saikace ni yar gidan wasu masu dashi ne ,
Na dade Ina tsaye a titi Ina jiran napep Amman ba sa a , daga Wanda Zai ce ba hanyar xaiyi ba , dai Wanda xai yanko mun kudi masu yawa , tsaki naja Ina tunanin da yanzu saurayina mai kudi ne da ya siyamun mota ko ya turo driver dauka na, bangama zancen zucin ba wata mota kirar Benz ta faka a gabana, Sannu yan mata na cikin Motar ya fada Yana kallona da idanuwansa masu kyaun gaske,kamar mafarki naga abun , rufe idona nayi na bude hakan ya tabbaatar mun da ba mafarki nakeyi ba gaske ne, yau ni zaitun a ce mai shirin yin saurayi mai arziki , kamar nayi ihu dan dadi duk da bansan abinda yasaka ya tsaya ba Yana mun magana.
YOU ARE READING
BURINA(HAUSA NOVEL)
FantasyThis novel is about a young lady zaituna who was came from a poor background and Tries her possible means to fit in just to be with her friends who happens to be rich Sit back and enjoy 🩷