Chapter 27

6.1K 473 4
                                    


             Luβπα Sufyαπ

        
*Ina godiya mai yawa ga masoyan da suke mun addua ako da yaushe. Allah ya biya muku bukatunku na alkhairi. Amin*


Ganin yanayin fuskar shi yasa husna girgiza shi ta dawo dashi daga dogon tunanin da yake yi.

Dafe kanshi yai cikin hannuwanshi yana maida numfashi da sauri da sauri.

Wayar shi ya dauko. Baisan me zaice ma su mumyn Nas ba.

Husna ya kalla idanuwanshi bayyane da duk tsoron da yake ji muryarshi na rawa yace mata.

"I don't know what to tell them, mumyn nas ta dauka zan kula dashi........"

Kasa karasawa yai ya dafe kanshi kawai yana jin kaman ace kasa ta bude ya shige ya huta da wannan nauyin da yake kanshi.

Husna bata san me zatace masa ba ko kuma taya zata rage masa abinda yake ji.

Wayarshi ta soma ringing. Ya duba umman shice. Kai ya shiga girgizawa kaman tana ganin shi.

Hakan yasa husna duba wayar ta ga wayake kira. Dagawa tai ta mika masa.

"Kai mata magana kawai. You can do this"

Jikinshi babu wani kwari ya kara wayar a kunnen shi yai shiru.

"Babana kana lafiya?"

Umman ta fada da rauni a muryarta. Sai yaji ya samu wani dan karfi kadan jin muryarta.

Cikin karfin hali yace.

"Mungode ma Allah umma...... Mumy fa?"

Yanajin ajiyar zuciyar data sauke sannan tace.

"Tun dazun kamala ya fada mana abinda ya faru. Mai martaba yace adan dagata tukunna muzo saboda yanayin tsaro. Ita tace tunda kana tare da Nas tabar ma Allah komai"

Lumshe idanuwanshi yai yanajin kaman mumyn Nas a gabanshi tai maganar. Yana kuma jin nauyin girman da ta dora masa.

"Allah yasa umma. Kuyita addu.a shi kadai Nas yake bukata a yanzun...... "

Yanda yai maganar ne yasa tace masa.

"Ya Naseer din?"

Yasan ma.anar tambayarta saboda yajita a muryarta. Bataso kai tsaye ta tambaye shi idan su saka rai da tashin Nas ko kuma su soma shiryama zuciyarsu hakuri dashi.

"Umma zan kiraki in an sami wani ci gaba"

Ya fadi yanajin yanda ta furta.

"Ya Allah.... "

Kamun ya kashe wayar. Dan yana tsoron tambayar datai masa.

Tun da suka shigo asibitin nan yake kokawa da zuciyarshi kan wannan tambayar.

Jiyai cikinshi ya wani kulle ya gyara zaman shi ya dora kanshi a cinyar husna yai shiru kawai.

Kyale shi tai. Tunda batada hanyar da zata rage masa abinda yake ji. Wacece ita da zata hana shi yin abinda yaji zai iya ya samu saukin zuciyar shi.

*

A asibitin sukai sallar isha.i. Duk yanda likitoci suka bashi magana kan cewa yanayin Nas a yanzun stable ne.

Suna kuma addu.a da fatan ya tsaya haka a kuma samu ci gaba kin yarda yai.

Da kanshi ya dudduba Nas din dabai masan duniyar dayake ba. Har lokacin bugun zuciyarshi ba wani karfi.

Saidai yana dan karuwa da uku zuwa hudu kan dazun sai kuma ya sauka. Amman yaki yarda daya tafi yabar Nas din.

Kallo daya zakai masa kasan cewar shi kanshi yana bukatar hutun amman yaki yarda ya tafi gida.

WATA BAKWAI 7Where stories live. Discover now