Chapter 30

5.1K 461 11
                                    


             Luβπα Sufyαπ

Ranar da Nas ya cika sati uku a asibiti. Sun dawo gida wajen zuhr.

Prince ishaq ya fita yace mata akwai abinda zaiyi.

*

Kallo take sanda ya dawo. Ya zauna kusa da ita yana wani langabewa.

"Gajiya ko?"

Ta bukata. Ya daga mata kai. Kallon shi take akwai abinda ya canza mata yau.

Fuskar shi tai wani fayau.

"Meye babu a fuskarka?"

Ta tambaya tana kallon fuskar.

Dariya yai. Tajima bataji dariyar nan tashi ba.

Itama sai abin ya bata dariya.

"Aski nayi fa"

Ya karasa maganar yana dariya. Shiru husna tai masa. Haba shisa taga fuskar tai wani fayau.

Suna zaune aka kira la.asar. Ya tashi ya nufi masallaci. Itakuma husna tai nata bangaren.

Tana yin sallar la.asar tasan zasu iya komawa asibiti don haka ta mike.

Wanka ta fito tana kwallia a gaban mirrow ammar ya kirata. Daga wayar tai tasa earphone.

Cikin muryarsa mai sanyi yace mata tawan

"kaman bakyason kashe auren nan ne ko?"

Murmushi tai kaman yana ganinta tace

"Nawan ba haka bane.Ka yarda dani wlh na rasa hanyar da zanbi ne har yanzun na kashe auren nan. Kai kasan ina sonka.

*

Sallah ya dawo. Baiga husna a falon su na sama ba. Dan haka ya nufi bangarenta ya fada mata yai waya da doc din Nas.

Komai yana nan yanda suka barshi dazun. Bayajin zasu koma yau saidai zuwa safe inyaso su kwana a wajen shi.

Kwankwasawa yai har sau biyu shiru. Ya dauka ma sallah take ya tura dakin da sallama ya shiga.

Tana zaune kan stool tana shafa mai jikinta sanye da doguwar riga.

Kan kunnenshi take furta komai.

*

Sam bataji shigowar prince ishaq.

Da duk kalma daya da zata fito bakinta sai zuciyarsa tai wani irin dokawa.

Lokaci daya ya tuno maganar huddy a wani lokaci can baya
"Yayana ka zama mai haquri sai dai karka yarda a wulaqanta mana darajarka ta ko wanne fanni"

Yau shi prince ishaq matar da take cikin gidansa da igiyar aurensa ukku a kanta ce take waya da wani qato.

Har take fada mishi maganganu iri wa.annan. Inalillahi wa ina ilaihi raji.un yame ta maimaitawa a zuciyarshi.

Yana fatan dai-dai ta hankalin shi kamun zuciya tasa shi aikata abinda bashi kenan ba.

Husna kam hankalinta kwance taketa wayarta. Tashi tai dan ta dauko dankwalin rigar jikinta.

Tana juyawa taganshi tsaye jingine da qofa............!

#WataBakwai

WATA BAKWAI 7Where stories live. Discover now