Luβπα Sufyαπ
In dedication to billy galadanchi, safiyya, ummie, dimples, jidderh and all the members of ummie jay novels.
Tun wajen karfe tara ya gama shiryawa Sai dai baisan ko ita ta shiryaba ko bata shirya ba.
Fitowa yai babban falo ya sami hadima daya dabai san sunanta ba don ba damuwa yai da hakan ba.Har qasa ta tsugunna kanta a sunkuye tace
"fatan yarima ya tashi cikin qoshin lafiya?"
Lafiya ya amsa a taqaice mulkin na motsa masa.
Yana son ya tura a ce mata ta fito sai dai yana gudun zata iya fadar magana a gaban hadimansa.
Baya qaunar yarfi da harkar yada girma duk da bawai son matsayin nasa na yanzun da na gaba yake ba.
Da kansa ya taka zuwa bangaren ta ya nufi dakinta. A hankali ya qwanqwasa.
*
Husna kam tunda ta tashi taji jikinta babu zazzabi sam. Tadai yi wanka ne tasa aka kawo mata soyayyen dankali tadan ci.
Tasha magungunanta dan bata da bukatar natacce yazo ya maimaita abinda yai jiya.
Dan ta kula namiji ne shi da yake yin abinda yaso babu kuma wanda ya isa ya hana shi inya tashi.
Chatting suke da ammar a whatsapp dan jiya da dare ya sata tai downloading sabo.
Taji an kwankwasa kofar. A zatonta asabe ce ta dawo kwashe kayan data kawo dan haka tace
"Shigo"
Tura qofar yai tana kwance da wayarta a hannu ta dago.
Saurin sadda kanta qasa tayi tana ci gaba da danna wayarta.Wannan nataccen nema sai dai ya gaji da tsayuwarsa a wajen ya shigo ko ya koma.
Chatting din da take da ammar ya fiye mata komai na gidan nan.Shi kullum yaita fama da kaya kaman wani dan sarki. Duk da tsanarsa da tai baya hana mayyar zuciyarta ganin yayi kyau.
"Ki fito mu tafi."
Ya fada cikin wannan muryar tasa ta yanga. Sai lokacin ta tuna yaune yace mata zasu tafi abuja.
A kasalance tace
"ba zani ba aina fada maka"
Wani abu yaji ya tsaya masa a wuya.
Inda ba.ai masa umarnin ya tafi da itaba sai dai kawai taga bata ganinsa.
Zuciyarsa ta dibe shi ta watsa wani lokaci can baya.
**** ****
"Yayana ni fa saina bika......yai dariyarsa
"huddy kiyi haquri ba dadewa zanyi ba kwana uku kawai Kuma zamuyi waya"
Ta sake goge hawayen dake bin fuskarta
"bana so kanamin nisa."
Sauke numfashi yai
"huddy ke kinmin nisa ai"
ya fadi a zuciyar tasa.
A fili kuma yace
"banson jan magana ko bacin rai. Umarni ne na cewar na tafi dake.Ki shirya nan da 15 minutes. I don't want to drag you myself, don't tempt me "
Ganin bata da niyyar cewa komai yasa shi ficewa.
Ita yanzun kam me zai bata mata rai bayan tana manne da ammar a whatsapp....wuni suke hira ko yana office ma haka da dare suna manne yana rikitata da voice notes dinsa.
Da batai niyyar shiryawa ba sai wata zuciyar tace yanzun in ma baki tashi ba dawowa zaiyi.
Kuma ta tabbata tsaf zai aikata abinda ya fada.
Maganar ma da take yi dashi lokacinta take bashi.
Tashi tayi ta sake kayan jikinta. Wani karamun akwati ta dauka badan tasan menene a cikin shi ba.
Gara ma ta bishi abuja din dan ya sake tabbatar da baya gabanta.
Mayafi kawai ta dora kan kayan jikinta taja akwatinta zuwa falo...inda wata daga cikin masu aikin tai saurin zuwa ta karbar mata. Fita akai dashi.
Natacce ne ya fito daga side dinsa sanye da alkyabba ruwan hanta mai cizawa da wata irin hula akansa. Bata so ta tsaya zuciarta ta misalta mata kyawunsa.
"Ungo"
ya fadi.....hannunsa ta kalla daya miqo mata batare data yarda ta kalli fuskarsa ba.
Alkyabba ce mai kalar tasa sai dai wannan akwai ado na mata a jikinta.
"Ki saka saboda zamu fara biyawa ta gida sannan mu wuce."
Karba kawai tayi. Bata son magana mai tsaho na hadasu inba dole ba.
Tanajin idanuwansa na binta har ta saka ba tare data kalle shi ba tace
"muje"
Gaba daya kamshinsa ne cike da alkyabbar jikinta. Ta kuma tsani yanda hancinta ke jin dadin kamshin.
Gaba ya shiga ta bishi a baya har zuwa wajen motar (Range Rover) wata fara mai kyau.
Bude musu akai ta shiga shima ya shiga baya.
Har suka isa gidan babu wanda yacewa kowa komai.Ita tana ta chatting da ammar abinta. Dan haka bata kula da komai ba sai tsayuwar motar data ji.
Aka zo aka bude musu qofa suka fito. Ya zo kusa da ita ya tsaya.
"Na iya lokacin da zamuyi a cikin gidan nan kiyi pretending komai normal ne a tsakaninmu."
Ya fada cikin muryar da takanji yaima yan aiki.
Cike da mamaki ta kalle shi.
Bata dai bashi amsa ba duk inda yai nan take binsa suna tafiya.
Tana kallon yanda mutanen cikin gida suke tsugunnawa tun kamin ya qaraso inda suke suna gaishe dashi amman ko kallon arziqi balle taji ya amsa.
"Ana gaishe dakai ko baka ji?" Ta buqata.
Bai bata amsa ba.. Taji haushin kanta ma datai masa magana.
Wani irin daki suka shiga da saita wuni a tsaye a wajen bata gama qarema kyawunsa kallo ba.
Ya zauna kan daya daga cikin manyan kujerun dakin.
"Ki zauna"
ya furta a hankali yana nuna mata waje a kusa dashi. Bata musa ba ta zauna.
Wata kyakkyawar mata ce magidanciya ta shigo dakin cikin shiga ta alfarma.
Sai taga matar ta mata wani irin kwarjini.Kasa taga ya sakko ya tsugunna itama bata san lokacin databi yanda yai ba.
Saida matar ta zauna tukunna ya gaishe da ita cike da girmamawa...itama gaishe tan tayi....da fara.a ta amsa musu sannan taga ya koma kan kujerar ya zauna...itama tayi hakan."Babana an shirya kenan?"
Ta buqata. Cikin tausasawar murya yace
"yanzun zamu wuce nace saimun biyo ta nan mun gaishe dake."
"Aikam ka kyauta sosai ba zaka je da ita taci wani abu ba kuma kudan zagaya ciki?"
"Uhm uhm umma sai dai ko inmun dawo muna sauri ne kinsan ba jirgi zamu bi ba"
ya fada yana miqewa..
Saita tsinci kanta da sake tsugunnawa tace mata mun tafi.Addu.a tai musu sosai. Kamun su kama hanya su fita.
Motar suka koma. Daga su sai driver din.
Tun dazun take mamakin yanda cikin motar yake.
Ba ta inda driver din zaiga me sukeyi saboda akwai barrier a tsakaninsu.
Hannu prince ishaq yakai ya taba goshinta. Ya sake taba kumatunta sanna ya koma cikin kujerar ya zauna sosai.
Husna kam batai mamaki ba. Kadan da aikin wannan bakin nataccen.
#WataBakwai
BINABASA MO ANG
WATA BAKWAI 7
SpiritualKaman yanda kaddara ta hada aurensu bayan ta rabata da wanda take so. Haka yake tunanin kaddara zata sa dole ya cika alkawarin daya dauka bayan cikar WATA BAKWAI. #Love triangle #HausaNovel