Luβπα Sufyαπ*Last page*
Ringing din wayarshi ya dawo dasu hayyacin su.
Saida yai kokarin saita kanshi tukunna ya daga. Mumyn Nas ce tana nemanshi kan maganar komawar Nas makaranta.
Saida ya sake sumbatar husna sosai sannan ya fita badan yaso ba.
A wajen ta kwanta tana jin wani yanayi na daban. Son shi na kara shigarta.
*
Bai dawo gidan ba sai yamma likis. Yana shigowa ana sallar magrib dan haka ya fita masallaci bai dawo ba sai dayai isha.i.
Jan husna yai dakinshi. Yasa ta sake yin alwala suka gabatar da nafila raka.a biyu.
Wanka ya shiga. Ya fito husna ma ta shiga.
Mai ta dauka zata shafa ya taso ya rike hannunta.
"Nafi sonki haka please"
Ajiye man tayi ya jata zuwa kan gadon.
Hannunshi ya dora saman kanta ya karanto Addu.ar da Manzon Allah S. A. W yace ayi.
‘Allahumma Inniy as’aluka khayraha wa khayra ma jabaltaha alayhi, wa a’uzu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alayhi.’
Itama husna yana sauke nashi ya dora nata akanshi tana fadin.
‘Allahumma inniy as’aluka khayrahu wa khayra ma jabaltahu alayhi, wa a’uzu bika min sharrihi wa sharri ma jabaltahu alayh.’
Hannuwanta ya riko ya kalleta sosai yace.
"Ina addu.a da fatan gina zama da rayuwa ta amana dake husna. Bana bukatar komai daga gareki da ya wuci yarda da aminci"
Sauke numfashi tai tace
"abu biyu nake rokonka gentle. Ka zama abokina ka zama mijina. Ina son duk randa nake da matsala da mijina inyi magana ta fahimta da abokina"
Kai ya jinjina yana fahimtar duk maganarta
"Bazan miki alkawarin komai ba husna. Zan iya kokarina"
Bai bari tai magana ba ya hade bakinshi da nata.
Daren ranar tasha addu.a da albarka. Ya samar musu da wata nutsuwa taban mamaki.
*
Shi fa yace ta tashe shi karfe goma.
Zaije wajen mai martaba. Gashi yanzun shigowarta daki na uku kenan tana tashin shi yaki tashi.
Zama tai kusa dashi. Sumba take manna masa ta ko ina na fuskarshi da wuyanshi.
Bude idanuwa yai ya fisgota ta fado kan gadon tana dariya.
"Gentle dan Allah yi hakuri. Tun dazun inata tashinka kaki ka tashine fa"
Bai saurareta ba ya soma aika mata da saqonni cikin salon shi dake tsaya mata a rai.
Tun tana masa magiya harya kashe mata bakin magana.
*
Sanda ya fito wanka tana kwance.
"Hussy ki tashi. Yunwa fa nake ji"
Tana jinshi gaba daya yagama gajiyar da ita. Tai shiru kaman tana bacci.
Gefen gadon ya zauna.
"Bara mu kara wani round din....."
Kamun ya karasa ta duro daga gadon ta nufi toilet ya kwashe da dariya.
Bedsheet din ya cire ya dauko wani ya sake.
YOU ARE READING
WATA BAKWAI 7
SpiritualKaman yanda kaddara ta hada aurensu bayan ta rabata da wanda take so. Haka yake tunanin kaddara zata sa dole ya cika alkawarin daya dauka bayan cikar WATA BAKWAI. #Love triangle #HausaNovel