Chapter 29

5.6K 470 5
                                    


             Luβπα Sufyαπ

Sati biyu kenan cif. Komai ya sauya musu.A asibiti suke kwana da kusan yini.

Ana samun ci gaba a fadar likitoci dan ita kam husna idanuwanta baya ganar mata haka tunda har yanzun nas bai bude idanuwanshi ba.

Motsi ma bata ga yayi ba. Harta da numfashi da taimakon na.ura yake yinshi. Abinci sai ta hanci.

Husna zatai magana da prince ishaq. Zasu danyi hira tun tanajin wani abu inya riqeta jikinsa harma ta daina. Saboda ba yanda zatayi dashi.

Takanji kaman bata kyautawa ammar sai dai a sati biyu harta saba tunda ba wani abun yake mata daya wuce riqeta a jikinsa ba.

Kuma ta gaji da qaryata zuciyarta hakan na mata dadi.

Tana son qamshinsa da duminsa duka. Ta nemi inda tsanarsa take a zuciyarta ta rasa.

Gaskiya mutane da yawa sunyin gaskiya. Karka yanke hukuncin yanda kake ji akan mutum saika zauna dashi tukunna.

Ta kula shi din mutum ne mai bala.in yanga. Saidai baya so ai masa.

Baya son gaddama. Komai nashi da tsari yake yinsa. Bata san me take ji game dashi ba.

Dan yansun komai rudani yake sakata. Tunaninta da yanayin komai.

Abu daya take da tabbas a kansa son ammar. Yana nan.

Duk da yanzun bata tunaninsa ko da yaushe sai dai da taji muryarsa komai yake dawo mata sabo.

Kalamansa nakaita wajaje da yawa da suka kai a soyayya.

Danma fadan da suke yawan yi kwana biyu. Ta mishi uzuri saboda ita kanta ta rasa dalilin dayasa take biyo prince ishaq asibitin.

Inhar zasu koma gida saiya mata tayin ta zauna itace take kiyawa.

Ammar kuma gani yake kaman zai rasata ne. Tsoronshi karta soma kulawa da su.

*

Prince ishaq kam zai iya cewa abinda ya faru da nas ya tuna masa da alqawarin daya daukar ma huddy a maganarsu ta qarshe a rayuwarta.

Yama zai manta. Huddynsa zata so ya samu farin ciki sai dai ko bai mata alqawari ba ba zata mantu a gurinsa ba.

Darajar so da en uwantaka ta wuce hakan.

Husna baima san me zaice da zuciyarsa a kanta ba. Yakan jima bai yarda ya shaqu da mutum ba.

Ko abokai yawanci na karatu ne. Sai na asibitin shi da ya dade da barma Dr.Hashim ragamar komai tun bayan rasuwar huddy.

Banda kamala bai yarda da kowa ba da sirrikansa. Shima baban shine sarkin fada. Kusan tare suka taso da prince ishaq din.

Zuciyarsa tana da rauni mai yawa ta wannen fannin.
Tana da saurin sabo.

Koya zakai masa karamci baya mantawa.

Yanzun ya saba da hussy kam. Bazaiyi qarya ba sabon da har mamaki yake bashi inyai hange zuwa wasu lokutta can baya.

Yanzun aurensu haryana kusan tasarwa wata na biyar.

Rayuwar babu wahala. A haka muke ta cinye kwanakinmu.

*

Sun dan koma gida su huta. Nan husna tabarshi ta shiga ciki abinta. Sai da ta kwanta ta huta sukai waya da ammar sannan.

Har zata fito ta tuna. Kausar ta kira ta fada mata abinda ya faru. Ta sha mita cewar batada kirki. Atleast ko da basu zoba zasuyi addu.a.

*

Yana zaune babban falo yana kallon yanda duniyar take a tashar aljazeera husna ta shigo.

Gefensa ta zauna batare data ce masa komai ba. Ya sauke numfashi.

Yanayin fuskarsa ta kalla tace mishi.

"Yadai?"

"Meyasa baki taba kiran sunana bane hussy?Tunda yanzun ana kallon fuskana sunan kuma ya gagara"

Ya buqata yana qarasa maganarsa da murmushi.

Tun rannan ya soma ce mata Hussy din nan. Sai taji sunan ya mata dadi.

Idanuwanta nakan kafet din dakin sai takejin wani iri. Sau uku tana bude baki sai taji sunanshi ya makale akan harshenta.

Ba zatai mishi qarya ba dan haka tace

"Sunanka yanamin nauyin fadane"

Ya wani yatsine fuskarshi mai kyau sannan yace

"Nikuma na gaji da zama nameless a wajenki."

Murmushi tai bata dago da kanta ba dai.

Yanajin dadin yanda yake da tasiri akanta. Koma wanne irine.

Muryarshi can kasan makoshi yace.

"Uhum inajinki. Ko sunana ko ki zabarmin wani"

Iya zaman sun nan tana karantar halayyarsa. Inba abinda ya bukata tayi ba bawai zai barta bane.

"Gentle"

sunan ya subuce mata da sauri ta dora da

"zan kiraka gentle yayi?"

Murmushinsa ne ya bata amsa.

Bai sake cewa komai. Jingina yai sosai da kujerar yaci gaba da kallon shi.

Yanzun harta soma sabawa da wasu halayen nasa. Yanzun zai mata magana kaman zasuyi hira mai nisa sai kuma yai shiru abinsa.

Prince ishaq akwai yanga. Wasu lokuttan sai suyi awa biyu zaune baice mata kanzil ba.

Yana magana saita kama ne. Ranar cayai mata su kwana a gida. Yai waya yace koya aka samu canji a kirashi.

Taji dadin hakan dan hakurin ammar ya kusan karewa. Aikam har sha biyun dare suka kai suna hira.

Charge dinshine ya dauke da basu hakura ba

*

Badan wannan abin daua faru ba da tuni sun koma kano dan wata daya da yan kwanaki kamata ace sunyi a garin abuja

Amman yanzun har suna shirin dosarwa wata uku.

Taji dadi sosai da kausar tazo har asibiti ita da mijinta suka duba Nas.

Dan kam ya zama qani a wajenta.

#WataBakwai

WATA BAKWAI 7Where stories live. Discover now