Luβπα SufyαπWayar ya dauka. Mumyn Nas ce hakan ya tabbatar mishi da isowarsu.
Dan haka yace ma hussy ta dauko alkyabbarta ta saka su jira qarasowarsu.
Sai bayan ta fito ne ya kalleta yace
"me kikaci?"
"Bana jin yunwa"
ta fadi.
Lokaci daya fuskarsa ta sauya zuwa yanda ta saba ganinsa farkon aurensu kamin ta san fara.arsa.
"Muje dining room din"
Ya umarta. Yanayinsa ya nuna mata ba zai karbi wani uzuri ba dan haka tai gaba yana binta har suka qarasa.
Zama yai yace mata
"Maza ci wani abu da sauri kamin su qaraso"
Babu yanda zatai haka dolenta ta danci plantain da dankalin turawa.
Ga kunyarsa da ta tsinci kanta ciki saboda kallon da yake mata.
A hankali tace
"kai ba zakaci komai ba"
"Na sha malt banjin saka ma cikina wani abune"
Ya furta yana miqewa.
Binsa tai a ranta tana fadin. Wato shi baya son sakama cikinsa wani abu. Sai ita yai ma dole.Suna fita babban falo sukaji sallama.
Tare suka amsa.Da fara.ar prince ishaq ya qarasa ya tarbo su yana fadin
"mumy sannunku da isowa"
Cikin sanyin murya husna tace musu
"barkanku da isowa"
Mumyn nas ta kalleta tace
"Ma shaa Allah. Sannu in-law"
Dan bata taba ganinta ba. Sanda akai auren tana england dubo kanwarta da akaima dashen koda.
"Ku qaraso ciki mana"
prince ishaq ya fadi.
Yana shirin juyawa yaji an taho da gudu ana fadin
"yayaaaaaa"
Kamin ya qarasa juyowa ta ruqunqume shi kaman zata karya shi.
Ya lumshe idanuwansa ya budesu a hankali. Wanni aikin sai auta.Baisan da ita za.azo ba.
Wani son kanwarshi yaji ya cika masa zuciya fal. Yayi kewarta sosai.
"Auta saikin karya shi ke yaushe zaki natsu ne bakya ganin antynki tsaye"
mumyn nas ta ke fadi tana murmushi.
Auta ta sake prince ishaq tana dariyarta cikin tabara tace
"mumy ai na dade banga yaya bane shisa. Laaaa antyyy wlh kin hadu"
ta qarasa wajenta tana riqo mata hannu.
Shafa kanta husna tai tana murmushi farat daya yanayin yarinyar harya shiga ranta.
Tai bala.in kama da nasir. Waisu haka suke da shiga raine? Ta tambayi kanta.
*
Bayanda prince ishaq baiba ko hutawa su danyi. Mumyn Nas taqi tace suje asibitin dan da sun ganshi ba jimawa zasuyi ba komawa zasuyi.
Husna tace
"Haba mumy da wuri haka na dauka zaku kwana ne ai"
Wai ai kam yau zamu juya in-law. Ba zamanmu nasir yake buqata ba. Addu.a ne. Tunda duk gaku anan din. Da munga yanayin jikin nasa zamu koma in shaa Allah"
Haka suka haqura tunda mumyn nas sam taqi jinsu. Suka nufi asibitin.
*
Suna bayan mota zaune ita da prince ishaq kasancewar mota daban daban ce data su mumyn Nas tace mishi
"kana ganin ya kamata auta taga Nas kuwa. Kaman shekarunta sunyi qanqanta taga tashin hankali har haka"
Dan autar kam duka bata fi shekaru bakwai ba.
Murmushi yai. Hannunta ya riqo.Ya hada yatsun su waje daya. Yace
"ki yarda dani hussy a rayuwa irin tamu auta taga abubuwa da yawa. Wannan ba komai bane."
Saita tsinci kanta da sake riqe hannunta cikin nasa sosae. Tana mamakin hargitsi dake cikin sarauta.
Lallai mutane na kuskure kan mulki. Daga nesa saikaita sha.awarsa har kana jin dama kaine matsayin.
Sai yanzun take lura babu komai cikin mulki musamman na sarauta banda rashin kwanciyar hankali da tarwatsar farin ciki.
*
Har suka qarasa asibitin suna riqe da hannun juna saida suka fito ne sannan.
Nas yanata bacci a fadar likitansa. Daqyar ma suka barsu suka shiga gabaki daya da sunce ba.a son hayaniya ta tashe sa anfi so ya farka da kanshi saboda magungunan da ke aiki.
Sunkai mintina ashirin zaune shiru kawai.
Kamin mumyn nas ta miqe."Allah ya bashi lafiya"
ta furta a sanyaye.
Su duka suka amsa da amin.
"Is he gonna be okay?"
Auta ta tambaya muryarta can qasa.
Tsugunnawa prince ishaq yai yanda tsahonsu yazo dai dai.
Ya dafa kafadunta cikin taushin murya yace mata"we don't know yet. Amman muna masa addu.a."
Husna ta faki ido tadanyi qasa ta mintsine shi a baya.
Yaji zafi ya dake kawai ya miqe.Ta riqo hannun auta da idanuwanta suka cika taf da hawaye. Tajata jikinta. A hankali tace
"karki damu zaiji sauqi in shaa Allah. Kinga bacci yake. Daya tashi zan kira mumy a waya ku gaisa."
Kai kawai auta take daga ma husna saboda kukan da yake neman cin qarfinta.
Hada ido sukai da prince ishaq ta galla mishi harara. Duk shi yaja.
Wannan yar yarinyar saboda Allah.
*
A wajen mota sukai sallama da su prince ishaq aka tafi a mayar dasu airport subi jirgin dazai koma kano qarfe 12.
Saida suka shiga mota su kadai sannan ta juyo ta kalle shi sosai a dake tace
"meke damunka?"
"Me nai maki zaki mintsine ni"
Ya buqata shima a dake.
"Saboda me zaka fada ma auta cewan ba lallai bane nas ya tashi. Baka ga tai qaranta ba?"
Husna take fadi ranta a bace.
Shi sai yaga ta qara kyau yanda ta dage tanata masifa. Baisan sanda dariya ta kubce masa ba.Ta sake hade rai duk da kyau da taga ya qara mata. Inyai dariya takan bayyana farin cikin a fuskarsa da wani kwarjini naban mamaki.
Bata san lokacin data ja mishi hanci ba. Ya ture hannunta yana fadin
"oww hussy da zafi fa"
Ammar! Zuciyarta ta furta a hankali.
Dannewa tai ta kalli prince ishaq dake gabanta. Tace
"abinda kai baka kyauta ba sam"
Da yanayin muryarta yace
"ni bazanyi qarya ba"
Dariya ya bata sosai.
Ya tsaya yana kallonta. Komai nata yasha ban ban dana huddy.Komai da yake ji a kanta dabanne da yanda yaji akan huddy.
A lokaci daya kuma su dukansu sunyi tarayya a zuciyarsa wajaje daban daban.
#WataBakwai
ESTÁS LEYENDO
WATA BAKWAI 7
EspiritualKaman yanda kaddara ta hada aurensu bayan ta rabata da wanda take so. Haka yake tunanin kaddara zata sa dole ya cika alkawarin daya dauka bayan cikar WATA BAKWAI. #Love triangle #HausaNovel