Luβπα Sufyαπ*2nd to the last page*
Da gudunta ta ruga ta sameshi a dakinshi yana kwance yasaka laptop a gaba yana aiki bayanshi ta dare ta zauna abinta ta sakalo hannayenta ta wuyanshi ta kwanta ta furta
"Gentle kausar ta haihu ansa mu baby boy"
Laptop din ya janye gefe daya. Ya kamo hannunta ta sakko daga bayanshi. Ta zauna gefen shi.
Wani yanayi yakeji. Daman ace babyn nan nasu ne. Da ba karamun dadi zaiji ba yau.
Da murmushi a fuskarshi ya ce.
"Ma shaa Allah. Allah ya raya babyn da mumynshi"
Ta amsa da amin kamun yace
"Yaushe ne suna?"
"Yau aka haihu kaga Friday suna ze kama" bata fuska yayi yace
"To yaushe zaki tafi saboda nasan Wanan satin me zuwa ayyukane kaina barkatai bazan samu damar binki abj ba"
"Thursday zantafi indawo Sunday"
Zaro ido yayi yace
"Hussy kwana uku kenan fa ko?"
Rau-rau tai da idanuwanta.
"Please gentle. Kausar ce fa"
"bazan hanaki tafiyaba kinsani, amma hussy kwana uku fa. Ko dan ke ba zakiyi kewata ba?"
Murmushi tamasa tana dora kanta a kafadarshi. Ita kanta tasan a daddafe zatai kwanakin nan.
Ko bikin gidansu da akai. Dadewa take batai bacci ba. Ta saba duk juyin da zatai ya gyara mata kwanciya a jikinshi.
"Gentle kayi hakuri zan dawo saturday.Wallahi nima zan kewarka sosai."
Matseta yayi tamkar wani zai kwace masa ita. Yai shiru kawai. Kwanakin daya rage musu yake kirgawa.
Yanajin da husna ta soshi da bata soshi ba. A karo na farko a rayuwarshi zai karya alkawari. Da bazai taba iya hakura da ita ba.
Koda kuwa ba za.a samu wani ci gaba ba a zamansu.
*
Da kanshi yaje yai mata booking tun kamun ranar tafiyarta abuja.
Ta gama shiryawa tsaf. Shi zai kaita airport ya wuce gidansu. Ya wani tsaya jikin bango ya tabare fuska.
"Gentle please. In kana haka da fuska yazan in tafi"
Takawa tai ta karasa inda yake tsaya. Hannuwanshi ta riko bai hanata ba. Kawai ya zuba mata idanuwanshi ne.
"Gentlee manaa..... "
"Kawai bana so ne. Bana sonki da nisa haka har kwana biyu"
Ji tai harya kanta ya soma ciwo. Ita kanta badan kausar bace bamai ja mata tafiyar nan.
"Ginger dinka na fridge"
Ta fadi kaman ginger din data hada mishi zai rage masa missing dinta.
"Ki aika mata da ginger din ni ki zauna"
Dariya ya bata. Shima kuma sai abun ya bashi dariya. Janta yai jikinshi yau hugging sosai.
Ji yake kaman ya maida ta cikin jikinshi kawai ya boyeta. Dakyar ta lallabashi suka fita.
*
Tana isa abuja ta samu ana jiranta a airport. Saida ta shiga mota sannan ta kira prince ishaq din.
VOUS LISEZ
WATA BAKWAI 7
SpiritualitéKaman yanda kaddara ta hada aurensu bayan ta rabata da wanda take so. Haka yake tunanin kaddara zata sa dole ya cika alkawarin daya dauka bayan cikar WATA BAKWAI. #Love triangle #HausaNovel