Luβπα SufyαπAnyi ma Nas aiki cikin nasara. Komai na tafiya yanda ake so da yardar Allah.
*
Yau satin su daya kenan a india.
Suna zaune a hotel room dinsu prince ishaq yai zaune shiru.
Husna na cin cookies tana game din datai downloading a tablet dinshi.
Taga shirun shi ya wuce misali ta dago tace
"yadai?"
Da wani yanayi a idanuwanshi da ta kasa fahimta yace.
"Kinsan sai yanzun nai tunanin kasar nan babu wanda yasanni. Banida wani matsayi sai na koma tawa kasar......"
Kallon shi take da mamaki ya ci gaba da fadin
"Zan iya kome nake so. Zan iya rayuwata free hussy"
Yanayin da yake maganar ya sata fadin.
"Me kake sonyi? Kamun mu koma?"
Murmushin nan nashi yai mata har dimple din fuskarshi ya fito.
"I wanna have fun. Naseer is ok. Ina son living sauran days dina kamun in koma gida to the fullest"
Wayar husna ta saka a key. Ta ajiye cookies din gefe tana fadin
"Tashi ka shirya to. Muje wajen Nas mu tafi yawo"
Mikewa yai ya nufi bathroom.
Ta girgiza kai. Yanda yanayinsa yake cike da farin ciki ya mata dadi.
Kome yake sonyi ita kam zata taya shi. Kaman yanda ya bata kwarin gwiwa ta kira iyayenta.
Dan jiya tai bacci wanda ta jima bata yishi ba. Taji muryar iyayenta. Ta gaisa da kowa.
Sun sa mata albarka. Har kuka sai da tai dan farin ciki. To name ita ba zata taya shi ya samu nashi farin cikin ba.
Tana nan zaune ya fito. Itama ta tashi tayo wanka.
Doguwar riga ta saka loose tai rolling mayafin akanta. Duk da babu kwalliya a fuskarta ta mishi kyau sosai.
Fita zasuyi tazo gabanshi ta tsaya. Hannuwanshi ta riko ta sauke idanuwanta cikin nashi.
So take yaga yanda tai nadamar abinda tai masa. Muryarta na rawa tace
"Har yanzun baka ce ka yafemun ba gentle. Nayi kuskure mai girma nasani amman.......... "
"Na yafe miki husna. Na yafe miki tun kamun ki rokeni"
Batasan lokacin sata rungume shi ba. Dan ji tai kaman ya sauke mata wani katon nauyi.
Hannuwanshi yasa ya rungumeta na wasu dakikai kamun ya sake ta.
*
Sai da suka biya wajen Nas. Dakyar ma yake musu magana saboda magunguna sun fara dibarshi.
Saida yai bacci tukunna suka fito. Su kansu basu san inda zasu je ba.
Hannun ta na cikin nashi. Hanya kawai suka diba.
Duk titin dayai musu su bi. Wani ad husna tagani na poster din wani film.
"O. M. G wallahi ina mugun son actor din can..... "
Ta fadi tana nuna ma prince ishaq. Kallon guy din yai.
"Vijay yayi fa. Kyanshi wani nutsatse ne. Kaga inyai dariya..... "
KAMU SEDANG MEMBACA
WATA BAKWAI 7
SpiritualKaman yanda kaddara ta hada aurensu bayan ta rabata da wanda take so. Haka yake tunanin kaddara zata sa dole ya cika alkawarin daya dauka bayan cikar WATA BAKWAI. #Love triangle #HausaNovel