Two

4.1K 423 36
                                    

®Fikrah Writers Association 🖊

       ©Jeedderh Lawals

                ‘... And now that we're here, feeling so good.. Abt all the things that we went through... Knowing that God is pleased with us too, is not a dream, this is so true...
                Feeling the peace all around, seeing things we could never imagine, hearing the sounds of rivers flow.. And we know, we'll be here forever, the feeling is indescribable, knowing that this is our reward!...’
                Paradise! By Maher Zain.
        May we all meet there, one day. In shaa Allah!

                          °•02•°

                        ☆☆☆☆☆☆

       Babban ofishi ne mai fadi, duk da cewa bai yi kama da sauran ordinary offices da idanu suka saba gani ba. Amma kallo daya zaka mishi ka tabbatar da cewa ofishin likita ne.

Kyakkyawar matashiyar budurwar ta dago daga rubutun da take yi ta kalli matar dake gabanta. Sanye take da jallabiya baka kirar kasar Oman, ta dora farar lab coat akai ta yane kanta da mayafi. Dan madaidaicin farin gilashi ne a idanunta wanda ya kara fitar mata da kwarjini da kamalar ta. Idan ba da kunnen ka kaji tayi Hausa ba, ba zaka taba iya yarda zata yi wani yare wanda bai danganci larabci ba.

Murmushi ta sakar mata mai kwantar da hankali, ta mika mata katin data gama rubutu akai tace,
“wadannan magungunan su zaki siya kina sha. Sai dai don Allah a kiyaye lokutan shan su, sannan ki kiyaye yawan shan gishiri, ki daina jinkirta shiga bandaki, idan da hali duk ruwan da zaki sha ya kasance akwai lemun tsami a ciki. Kin ga kina da hawan jini, idan ciwon kodar yafi karfinki, abin zai yi muni sosai. Zai iya kaiwa matakin da dole sai anyi miki aiki, idan kuma hakan ya faru hawan jinin zai iya kawo matsala. Don haka ki kula don Allah”.

Matar ta gyada kanta cikin nuna alamun fahimta, tace “to likita, in Allah ya yarda zan kula“. Likitar ta gyada kanta, “to shikenan. Allah ya ba da lafiya. Da kinji alamun dawowar ciwon kada ki jinkirta dawowa gare mu“ matar ta mike tana godiya, ta mata sallama ta fita. Ita kuma ta maida kanta ga rubuce-rubuce.

Ba'a jima ba landline dake bisa desk din ya dauki kara, ta daga. Daga can nurse tace “Dr. This is room 32, patient din ya tashi yanzu" tace “ok, gani nan zuwa".  Ta ajiye kiran ta fita daga ofis din cikin sauri-sauri.

Duk inda tayi tana cin karo da nurses da likitoci, cikin fara'ah take gaisar dasu ko su gaishe ta ta amsa, har ta dangana da daki na talatin da biyu inda nan ne aka kwantar da patient din da tayi wa dashen koda jiya.

Ta shiga ta duba shi taga babu wata matsala, tayi hamdala tare da duban nurse din dake tsaye tana rubutu cikin files din patient din. Tace ”ki kawo min file din nashi ofis dina" nurse din ta amsa da "yes, dr".

Office din Dr. Samairah tayi knocking shiga, ganin tana ganin patient yasa ta juya baya tare da ce mata zata dawo.

A bakin kofar pharmacy din dake cikin asibitin suka ci karo da dattijuwar data bar ofishinta, hannunta dauke da leda mai dauke da tambarin pharmacy din. Ta murmusa tare da karasawa gabanta, tace “na manta ban rubuta miki prescription din magungunan ba, ko zaki kawo in rubuta miki?" matar ta mika mata ba musu.

Ta ciro kwalin magani daya ta mika mata a maimakon hudu. Ta kalli maganin na yan dakikai, ta maida dubanta ga saurayin dake gefen matar wanda take tunanin dan ta ne, tace "me ya faru da sauran magungunan? Baku same su bane?" saurayin yayi kasa da kan shi, sai matar ce tace "akwai likita. Kudin dake hannunmu wannan maganin ne kadai zasu iya siya, shi yasa muka sayi guda dayan. Dama kudin auren shi ne da yake tarawa ya ciro ya kawo ni asibitin dasu, to tun a wajen sayen kati kudin suka tafi, balle sauran kananun abubuwa. Sauran kudin ne muka tatuke muka sayi maganin, haka nan idan Allah ya taimaka, sai ki ga an samu lafiya".

Doctor Sheerah! (SAMPLE ONLY)Where stories live. Discover now