Eighteen

2.5K 276 60
                                    

®Fikrah Writers Association🖊

                 ©Jeedderh Lawals

                            DOCTOR SHEERAH!

 

                           ***

              'Let the darkness lead us into the light.
               'Let our dreams get lost, feel the temperature rise.,
                 'So baby, tell me one more beautiful lie., one touch and I ignite!.
                  'I feel the heat as we collide,
                  'Like a fever that feels so right...!'
                Ignite-Alan Walker.


                                      •°18°•

                        "Me kake yi anan?".

Abinda ta fara tambaya kenan data isa inda yake tsaye. Ya daga kai ya kalleta, fuskarshi dauke da wani irin murmushi kamar bakinshi zai rabe biyu. Yace "ai nayi zaton ba zaki sauko ba. Har na fara tsoron ta yadda zan iya kai washegari a tsaye anan!".

Ta nade hannuwanta a kirji, "me kake so kayi proving da ka biyo ni wajen zama na?". Ko hesitating bai yi ba, yace "that kin damu dani!".
Ita abin sai ya ma bata dariya. It's either tsabar yarda da kai ne ya mishi yawa, ko kuma tsabar ji da kai.

Tace "ni ban damu da kai ba. Me yasa zan damu da kai kuwa?". Yace "da ban damu dake ba, da ba zan biyo ki har nan ba. Da baki damu dani ba, da baki sauko kasa kinzo wajena ba. It's a fact, believe it or not". Ta gyara tsayuwarta sosai, "me kake bukata da ni ne?".

Yace "zuciyarki nake so ki mallaka min, gabadayanta!". Tace "Anyi mun miji a gida". Duk da kokarin boye razanarshi da yayi, sai data karanci hakan akan fuskarshi. Yace "an daura auren?" ta girgiza kai. Yace "kudin aure fa? An kai gidanku?" nan ma ta girgiza kai. Yace "then we are all good. Dama kawai zaki bani, sosai nake so in nuna miki yadda nake jin zafin soyayyarki a cikin zuciyata!". Ta girgiza kai, "ba ka tunanin abinda zai zo ya faru, idan muka biyewa zuciyoyinmu, daga baya kuma mu zo burinmu bai cika ba?".

Ya tashi daga jikin motar daya jingina, ya kara taku biyu zuwa kusa da ita. Kai ta daga tana kallonshi. Yace "ban yarda da love at first sight ba, ban yarda da coincidence ba, amma na yarda da kaddara. You attracting me a ranar farko dana dora idanu akanki, kasancewarmu yare daya, kabila daya, masu addini daya, a wannan kasar, na tabbata Allah ne ya kaddara haduwarmu. Kallo daya na miki a rayuwata, jikina ya bani cewa you are that woman. Wadda zan kira matata, kuma uwar 'ya'yana! Jikina bai taba bani ba daidai ba, me yasa zan ji tsoro?".

Murmushi take yi a tausashe, tunda ya fara magana har ya gama. She liked him already.

A hankali, kamar mai rada, tace "Sheerah!".
Ya kwantar da kanshi yana kallonta cikin alamun tambaya.
Ta sake cewa "Mubassheerah! Sunana!".

Ya lumshe ido, yana jin can kasan zuciyarshi fari tas kamar ance an mallaka mishi ita gabadaya. Yace "what a nice name, for a nice young lady like you!... Moustapha!".

Suka tsaya suna kallon juna cikin murmushi daya nuna aminci, yarda da kuma kauna.

***

Wani karamin coffee shop anan kusa da gidan nasu suka shiga. Aka kai musu fruit yoghurt a cikin wani glass bowl babba, da cokula guda biyu a ciki.

Sheerah ta kai spoonful bakinta tana kallon fuskar Moustapha kamar wani madubi, tace "so, kana da yammata? Ko kuma ka taba yin yammata? If yes, nawa?". Ya jefa mata murmushi cikin tsokana, "uhmm, my jealousy jealousy girlfriend!!". Ta jefa mishi harara cikin wasa, "ina kokarin saninka ne kawai, you know". Ya kada idanu kawai. Ta kara harararshi, "da gaske fa!". Yace "ban taba yin budurwa ba tunda nake".

Doctor Sheerah! (SAMPLE ONLY)Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon