®Fikrah Writers Association🖊
©Jeedderh Lawals
DOCTOR SHEERAH!
•°24°•
Ramlah ce ta tashe su suka yi sallar asubahi, bayan nan komawa barci tayi abinta. Bata tashi ba sai misalin karfe tara na safe, Allah yasa da asubar ta kira Doctor Taheer ta sanar dashi ba zata shiga asibiti da wuri ba ranar. Ganin Fadima da Ramlah basa dakin, yasa tayi tunanin suna falo. Don haka wanka ta shiga tayi, ta shirya cikin riga blouse mai dogon hannu da pencil skirt. Ko hoda bata murza a fuskarta ba, turare oudul-abyadh ta fesa kawai a jikinta tare da goga na sahli a hannu da gabbanta. Ta dauki duk wani abinda zasu bukata ta zuba a cikin jaka ta fita.
Ramlah da Fadima na zaune akan kujera suna hira, abin ya ba Sheerah mamaki ganin yadda Fadima ta dage tana kwasar dariya. Abinda bata taba gani game da ita ba idan dai tazo ga maganar baki. Kodayake, surutun Ramlah ma kadai ya isa ai.
Suka bita da kallo suna murmushi har ta zauna a kusa dasu. Hannu ta basu duk suka gaida. Ramlah ta gaisheta ta amsa. Ramlah tace "dama ke muke jira, akwai abinci akan dinning". Sheerah tace "kada dai ke kika dafa?".
Ramlah ta girgiza kai, "a'ah. Mommy ta turo daga gida tun dazu". Sheerah tace "to ai da kunci naku kawai, ba sai kun jira ni ba".
Ramlah ta girgiza kai, "cin abinci cikin mutane yafi dadi da lada, yana kuma kara karfafa zumunci, sosai. Na riga na saba cin abinci tare dasu Mommy, shi yasa ko ina jin yunwa bana jin dadin abincin sai ina tare dasu". Sheerah ta jinjina kai kawai. Bata san komi game da hakan ba, zata iya kirga iya lokutan da suka ci abinci ita da iyayenta a tare a kan yatsun hannunta, and they were not even memorable. Lokacin da suna tare da Moustapha dai, kusan a kowane lokaci tare suke cin abinci, musamman ranar data kwana a gidanshi. Su kan zauna suci abinci tare. Ba kuma zata yi karya ba, those times were the best, very memorable.
Gabanta taji ya fadi, zuciyarta tana bugawa fiye da yadda yakamata. Moustapha!! Bata san me haduwa dashi yake nufi ba a wannan lokacin. Bayyanarshi kwatsam, ba zato ba tsammani, ya dauketa unexpected. Amma koma dai menene, Good or bad, she can deal with it, at least abinda take fata kenan.
Ganin tana nema ta dilmiya cikin duniyar tunanin baya, yasa ta kama hannun Fadima suka nufi karamin dinning dinsu. Suka zauna. Ramlah ce da kanta ta zuba musu abincin, romon kan sa, masa, shayi, soyayyen kwai, da chips. Ta gama ta koma ta zauna. Sai data ga su Sheerah sun dauki cokali sun fara cin abincin sannan itama tayi bismillah ta fara cin nata. Sheerah ta kalleta tana murmushi, kwarai dabi'u da tarbiyar yarinyar suke burgeta.
A hankali suke cin abincin, babu wanda yayi magana, har suka gama cin abincin. Ramlah ta tattara kayan waje guda ta maida su cikin kwandon da aka kawo su. Sauran abincin kuma ta juye a plastic rubbers ta saka musu cikin fridge. Sheerah tayi magiyar ta bari su wanke, tace direba yana waje yana jiranta. Dole ta kyaleta.
Dunguma suka yi zasu fita, Ramlah ta kara kallon Sheerah, tace "kada dai kice mun a haka zaki fita?". Sheerah ta kalli kayan jikinta, "what? Kayana suna da matsala ne?". Ramlah tace "a'ah. Zo ki gani". Ta kama hannunta ta zaunar da ita akan kujera. Jakar hannunta ta bude ta dauko hoda da janbaki. Sheerah ta zare ido, "inaa! Bana shafa hoda Ramlah!". Tace "baki ga fuskar ki bane shi yasa zaki ce haka. Kinyi wata iri, circles sun fito miki, ga idanunki sunyi ja". Sheerah tayi shiru don bata da bakin musu, ta kalli fuskarta a madubi a toilet taga yadda ta kumbura. Tasan rashin barci ne, gajiya, da damuwar ganin Moustapha. Tana ji Ramlah tana goga mata powder din, ta shafa mata lip balm don taki yarda tasa janbaki. Ramlah ta kare mata kallo tana murmushi, "Yauwa, yanzu kika fito kamar mutum. Muje!". Suka dunguma suka fita.
YOU ARE READING
Doctor Sheerah! (SAMPLE ONLY)
SpiritualRayuwarta, farincikinta, damuwarta, tashin hankalinta, komi nata ya ta'allaka ga mutanen nan su biyu ne kacal! Su kadai take kallo taci gaba da rayuwa kamar babu wata damuwa a ranta, her world revolves around them!! Me zai faru lokacin da abubuwa s...