Three

3.4K 361 16
                                    

®Fikrah Writers Association🖊

                  ©Jeedderh Lawals

                              •°°•

 
                      Yana fitowa daga cikin masallacin dake manne da gidansu bayan sallar isha, ya fada gidan. A garejin ajiye motoci yaci karo da wasu manyan Ferraris bakake guda biyu a fake. Yayi rolling idanunshi, "woahh! Dad yazo mana weekend kenan!".

Cikin sassarfa ya fada falon. Akan dinning table ya hange su su duka suna dinner. Hajiya Aina'u mahaifiyar su, na hakimce a gefen Dad dinsu Alhaji Abdul-Qadeer. Taci kwalliya cikin wani tsadadden Swiss material maroon color mai sakar leaves a jiki na kalolin zare, wuyanta da hannunta har da yatsu sun sha adon sarka, warwaro da zobban daham, sai sheki take. Idan ka ganta a lokacin, ba zaka taba cewa ita ta sauke gandamemen d'a kamar Kamal dan shekaru talatin daga jikinta ba, tafi kama da yan shekaru talatin da biyar zuwa da shida. Sai karairaya take tana tarairayar Dad abinta, ko kunyar diyar su Ramlah dake gefen su bata ji.

Shima kai tsaye dinning din ya nufa. Ya mikawa Dad din nasu hannu, suka yi musabiha kafin yaja kujera ya zauna a gefen kanwar shi, Ramlah. Ya zamana yana fuskantar Dad din, yace "Dad, zuwa babu sanarwa?". Ya kai spoon din fried rice bakin shi, ya tauna, "well, ni kaina ban san cewa na zo ba sai dana ganni a tsakiyar falon nan. Ina tunanin wata ta janyo ni ba tare da sani na ba!".

Mom ta jefa mishi hararar wasa, Kamal ya sadda kan shi kasa yana dan murmushi, yayin da Ramlah ta kyalkyale da dariya. Ya kwashi fried rice cike da cokali ya watsa mata a baki. A fusace ta dinga hadiye shinkafar, ta kwala ihun "Ya K!!" a saitin kunnanshi, yayi saurin ja da baya daga gareta yana dafe da kunnenshi. Daddy ya kame baki, "Ramatu, kurumta shi zaki yi ne?" ta turo baki gaba, cikin shagwaba tace "Dad, baka ga abinda yayi mun bane?".
Mom tace "gaskiya fa! Idan da ta kware fa?". Kamal ya kamo hannunta, "naji nayi laifi, am sorry!" tayi murmushi tare da gyada kai. Mom tayi serving din shi ta mika mishi, yasa cokali ya deba ya kai baki. Hankalin shi ya mayar ga Abban nasu, yace "Dad, ya aiki?" Alhaji Abdul-Qadeer yayi ajiyar zuciya, kafin ya amsa mishi da "da sauki kawai" su duka suka saki dariya a hankali. Ya kalle su, "wato dariya ma na baku koh? Saboda baku san irin wahalar da muke sha bane. Ina kaza, da kaza..." ya shiga zuba musu labarin abubuwan da suke yi har suka gama cin abincin. Mommy da Ramlah suka hada kan kaya suka tafi kicin, Dad da Kamal suka koma kan kujeru suna ci gaba da hirar wajen aikin Daddyn.

Washegari ranar Asabar, karfe shida na safe Kamal na cikin gym akan treadmill yana motsa jikin shi. Sanye yake da sports Jersey navy blue masu ratsin fari duk ya hada zufa. Muscles duk sun fito a wuyan shi da kafadunshi, ga wasu gurayen karfi da suka dabaibaye arms dinshi. Ramlah ta shigo gym din cikin fararen sports, riga armlet da 3-quarters, kafarta sanye da farin canvass. Wankan tarwada ce gabadayan ta, tafi Kamal hasken fata. Dad dinsu ta dauko wanda ya kasance wankan tarwada, yayin da Mommyn su take ja-jawur. Su kan ce Kamal bakin kakan su, mahaifin Dad ya dauko. Ba laifi tana da sumar ka mai yawa, baka-kirin mai tauri. Ta kama kanta da babu kitso, a tsakiyar kanta tayi kalba daya dashi, ya kuwa sauka har doron wuyanta, don tun asali Ramlah bata son kitso ko kadan.

Ta hau kan keken motsa jiki itama na kusa dana Kamal. Cikin siririyar murya tace "morning Ya K."
Ya kashe injin ya sauka, ya fara push and pull a tsakiyar dakin. Sai da yayi pushing kamar guda biyar kafin ya saurara, ya dubeta da tayi nisa a gudunta. Yace "wai ba ba kya jin dadi bane Ramlah?" tace "to bana jin dadin jikina ne Yaya". Yace "duk da haka, ki sauka kawai" ta rausayar da kai, "please mana Yaya, kaji?" yayi sighing, "ok. Minti goma" tayi dariya, "done!" tare da kara karfin gudun keken.

Minti goman yana cika, ta kashe injin ta sauka. Ya tare ta da dan karamin towel yana goge mata mata zufar fuskarta.
Tare suka fita daga cikin gym din, a falo suka ci karo da su Daddy suma sun dawo daga morning strolling da suke yi a cikin gidan. Suka durkusa suka gaishe su, suka amsa. Daga nan kowa ya wuce dakin shi, Mom taja hannun Ramlah suka shiga kicin don shirya break fast.

Doctor Sheerah! (SAMPLE ONLY)Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt