®Fikrah Writers Association🖊
©Jeedderh Lawals
DOCTOR SHEERAH!
•°14°•
Fairoz ta zauna akan gado, hannunta daya dafe da kumatunta tana kallon Sheerah dake faman shiryawa cikin wandon jeans da rigar blouse mai fadi wadda ta sauka har tsakiyar cinyoyinta. Tayi ajiyar zuciya tare da kara kallon agogo, karfe tara na dare.
Sheerah ta yana veil a kanta da wuyanta tare da daukar facing cap, wayar hannu da handbag. Tayi juyi a gaban Fairoz din, "na fito ko Ukhty?". Fairoz ta jinjina kai cikin rashin sanin abin cewa, tace "wai da gaske fita zaki yi yanzu Ukhty? Kin kuwa duba lokaci kin gani?" Sheerah ta kada idanu, "karfe tara ne fa! And Sister, JB ne fa a Dubai!! Naaaah!! Kin ma san ta yadda aka yi na samu tikitin zuwa concert dinnan kuwa? Gaskiya sai na je".
Fairoz tace, "idan fa Ummie ta leko bata ganki ba? Me zan ce mata?". Sheerah ta daga kafada, "sai ki gaya mata na shiga wanka, ina kicin, ina study room or whatever. Kin san dai ba zata matsa akan lallai sai ta ganni ba".
Haka Fairoz tana ji tana gani Sheerah tasa kafa ta tura kofar dakin ta fita tare da maidata ta rufe. Ta girgiza kai gabadaya ta rasa abin cewa. Daidai lokacin Fadima ta turo kofar dakin ta shigo. Tun da rana itama data sa kafa ta bar gidan bata dawo ba sai lokacin, ko Islamiya bata je ba ranar. Fairoz ta kalleta da manyan ledojin data shigo dasu, tace "ina kika je haka Fadim?". Tayi murmushi, "oh, mun je yawo ne cikin gari ni da friends dina". Daga haka ta fada bayi tayi wanka. Ta fito ta shirya cikin kayan barci, ta janyo ledojin ta bude. Kayan makulashe ne dana kwalliya iri-iri. Ta zauna ta fara ci. Fairoz kam da cikinta yake a tsure, cike da tsoron a gane cewa Sheerah bata gida, ta kasa cin komi duk da favorites desserts dinta data gani.
Fadima ta nuna mata robar ice cream din da take so, "har ice cream dinma ba zaki ci ba?". Fairoz ta kada kai da sauri, Fadima ta daga kafada tana muttering "kin yiwa kanki".
Daidai lokacin Hana ta turo kofar dakin ta leko tana daga waje, kanta ne kawai ya leka dakin. Sau tari sai a irin wadannan lokutan suke ganinta. Ta kan leka ta tambayesu yadda suka wuni. A tare suka gaidata ta amsa, tace "har yanzu baku yi barci bane?". Suka gyada mata kai, tace "to sai da safenku ko?", nan ma suka amsa a tare. Har ta maida kofar ta rufe, ta sake budewa ta leka, "ina Mubassheerah ne?" ta tambaya curiously.
Fairoz ta daga baki cikin in-ina da faduwar gaba tace "tan... na kkk... kicin!". Bata yi mamakin abinda ya kai yarinyar da babu abinda ta iya sarrafawa a kayan kicin, kicin ba, idan ma abin sha ne suna da fridge a cikin dakin ai wanda yake shake da drinks iri-iri. Ta daga kafada tace "to a gaidata". Daga haka ta maida kofar dakin ta rufe. Fairoz ta saki wata irin doguwar ajiyar zuciya. Sai lokacin tayi tsalle ta dira akan kayan da Fadima ta shiga dasu. Bayan sun gama cin abubuwan, kan gadonta ta koma ta kwanta, yayin da Fadima ta dasa sabuwar hira da abokanta a waya.
Sai washegari da duku-dukun safiya Sheerah ta koma gidan. Fairoz ta kamo hannunta taja ta toilet, a kidime take tambayarta, "me ya faru ne? Ya aka yi kika kwana acan? Ta yaya ma aka yi kika shigo nan bayan sai karfe shida ake bude gate din gida?". Sheerah tayi dariya ganin yadda ta tsure, "haba ukhty, chill mana. Ba'a fara da wuri bane, shi yasa na kwana. Kuma ni bata gate na fita ba ai, kuma ba ta can na dawo ba". Fairoz ta zare ido, "ta ina kika bi? Kar dai katanga kika hau?".
Sheerah ta harareta, "am I crazy? Ta kofar baya na bi". Ta nuna mata makullan kofar bayan gidan data dauka a dakin Mommynsu. Sai kawai Fairoz ta hau gyada kai cikin tsananin mamaki. Lamarin na Sheerah ya tsallake tunaninta.
CZYTASZ
Doctor Sheerah! (SAMPLE ONLY)
DuchoweRayuwarta, farincikinta, damuwarta, tashin hankalinta, komi nata ya ta'allaka ga mutanen nan su biyu ne kacal! Su kadai take kallo taci gaba da rayuwa kamar babu wata damuwa a ranta, her world revolves around them!! Me zai faru lokacin da abubuwa s...