®Fikrah Writers Association🖊
©Jeedderh Lawals
DOCTOR SHEERAH!
•°13°•
Fadima, Fairoz da Sheerah sun taso kai a hade. Very bright and smart. Babu wanda ya musu fadan hade kai, kasancewar tare suka taso a waje daya, ya sanya musu shakuwa sosai. Yayin da Fadima ta kasance very distant kuma secretive person, Sheerah da Fairoz sun kasance masu kazar-kazar da hayaniya. Shi yasa kusancin Sheerah da Fairoz yafi karfi. Yawancin hutunsu a Bahrain wajen Amtou Siddiqa suke yi. Abin zai ba mai karatu haushi idan yaji cewa sai acan ne suke samu suke halartar islamiya shima saboda tursasawar Zaid ne, kullum yake saka su a gaban mota ya kaisu makaranta kuma yaje ya dauko su. Idan suka koma gida kuma shikenan.
A shekaru na takwas, Sheerah ta san sunayen manyan yan wasan kwallon kafa data kwando, ta hardace wakoki fiye da a kirga a kanta. Amma a lokacin da zaka tsareta ba zata iya jero maka sunayen annabawa guda goma ba. Don ta Fadima ma ba a magana, Fairoz ce kawai mai dan kokarin rike addini don zuwa lokacin sun daina binta gida hutu. Karatun da taje gida ta koya, shi take zuwa ta zaunar da Sheerah har ma da Fadima din ta koyar dasu.
Haka suke rayuwarsu cikin tsananin duhu, ba tare da sanin su ba.
Sheerah nada shekara goma, Fadima kuma sha uku. Abdul ya daukesu ya kaisu Kazaure, a karo na farko kenan. Ba karamin dabi da tashin hankali suka sha da Hana ba kuwa. Tace bai isa ya dauki 'ya'yanta ya kai mata su can wata uwa duniya ba. Shi halin nata ma bayan mamaki, sai ya koma yana bashi dariya. Ya kalleta shekeke yake "yadda kike takamar cewa su yayanki ne, nima nawa ne. Dangi basu fi dangi ba. Lokacin da suke zuwa wajen naki dangin banyi magana ba, saboda haka kema haka zaki saka min ido ki kyaleni Hana. Kin sani sarai na fiki iko da yarannan. Me kike musu? Me kike musu da har zaki bugi kirji ki kira su da yaranki ke kadai? Ke yanzu baki ji kunyar kanki ba ma?". Sai tayi mukus ta koma gefe, shi kuwa ya kada kan yaran shi suka yi gaba.
Kwata-kwata canjin wajen da suka samu bai hanasu kin sakewa ba. A Kazaure suka sauka wajen Adama, wadda ta dinga ina taka saka-ina-taka tsare da yaran. Ta cancada musu girki na tsofi a matsayin abincin tarbar su, kwado tun daga na rama ne, na yakuwa, ga alale da dambu. Daga karshe dai sai Abdul ne kadai ya ci, su kuwa ya tura aka siyo musu wani abu daban.
Basu ga wani babban canji daga wajen da suka baro ba, bayan na yanayi da abincin ci. Shima abincin idan suka kasa ci sai Abdul ya bayar a siyo musu wanda suka saba ci shikenan. Zainabu ce ma mai mitar bai kamata yana sangartasu ba, ya kyalesu su saba da cin abincin. Tun ranar data damki Fadima ta dura mata faten tsakin masara yaran suka yi kaura da shiga sashenta, sai ta bisu har sashen Adama sannan take ganinsu. Kullum ya kan saka su a gaban mota ya yawata gari da dangi dasu, cikin kwana biyu idan ka gansu a Kazaure sai kayi zaton sun saba da garin ne sosai. Matsalarsu daya rashin jin Hausa. Bayan yan kananun kalmomi na gaisuwa da sauransu, babu abinda suka iya.
Kwanansu biyu anan Aina'u taje Kazauren ita da danta Kamal dan shekaru goma sha biyar. Cikin kankanin lokaci suka saba da Sheerah don bata da wahalar sabo kamar Fadima. Shine dan rakiya idan za'a je siyowa Sheerah Cupcakes. Tunda suka je abinda tafi ci kenan, safe, rana dare shine abin cinta. Dalili kenan da Kamal ya fara kiranta da cupcakes.
Aina'u ta yiwa Abdul fada sosai ganin yadda rayuwar yaran tashi take. Sam babu tarbiya a tare dasu, magana duk yadda tazo bakinsu basa tauna ta ko suyi tunani haka suke furzar da ita. Bata tashi mamaki bama sai da taga tunda taje gidan babu daya daga cikin yaran data kalli gabas da niyyar yin sallah. Cikin turanci ta kalli Sheerah dake kwance akan kujera tana cin cupcakes, Fadima kuma na ta shakar barci.
CZYTASZ
Doctor Sheerah! (SAMPLE ONLY)
DuchoweRayuwarta, farincikinta, damuwarta, tashin hankalinta, komi nata ya ta'allaka ga mutanen nan su biyu ne kacal! Su kadai take kallo taci gaba da rayuwa kamar babu wata damuwa a ranta, her world revolves around them!! Me zai faru lokacin da abubuwa s...