®Fikrah Writers Association🖊
©Jeedderh Lawals
'...So put your arms around me tonight..,
Let the music lift you up..,
Like you've never been so high..,
Open up your heart to me..,
Let the music lift you up..,
Like you've never been this free..,
'Til you feel the sunrise..,
Let the music warm your body..,
Like the heat of a thousand fires..,
The heat of a thousand fires!!'
-Camilla Cabello_Crying in the ClubGarin Al-Ain, babban gari ne a nahiyar Abu Dhabi. Tafiyar awa ce daya ce daga Abu Dhabin zuwa Al-Ain, amma a yanayin gudun da Sheerah tayi, da kuma rashin cunkuson ababen hawa akan titi, cikin mintuna arba'in da biyar ta shiga cikin garin. Lokacin da tayi tozali da katon sign board mai dauke da haruffan 'Marhaban ilal Al'Ain', ta murmusa sosai. A karo na farko in a while, taji wani sukuni ya ratsa ta.
Khalifa Street Apartments, Central District nan ta nufa. Tayi parking din motar ta a garejin da aka tanada saboda ajiye motoci. Ta dauki jaka a hannunta, su duka suka fito, Aafreen tsalle take yi tun karfinta, Sheerah da Sisi suna mata dariya. Gida na dari da daya suka tsaya, wanda yake a hawa na farko a cikin 20 storey building din dake unguwar. Sheerah ta danna intercom tana sanar da masu gidan cewa suna da baki. Ba jimawa suka ji ana kokarin bude kofar, daga can ciki suna jiyo hayaniyar yara da karan sautin TV. Kofar ta bude, ta bayyana balarabiyar matar. Kyakkyawa ce, kana ganinta kasan cewa kaga jinin Sheerah, musamman Doguwar fuskarta da kyawawan idanunta, banbancin kawai shine nata akwai sirkin ash sabanin na Sheerah da suka kasance zallan blues.
Jug din hannunta ta saki ya fadi kasa, ta dafe bakinta, kafin ta saki ihu tare da yin tsalle a lokaci guda ta rungume Sheerah. Dama tayi zaton haka, kara rungumeta tayi, suka shiga juyi a wajen suna dariya. Sai da suka fara jin jiri sannan suka saki juna, matar ta kalli Sheerah sosai tana murmushi. Tace "look at you Ukhti! Kullum kara kyau kike yi kamar wadda ake wankewa a inji!" Sheerah ta harareta cikin wasa, "ban san yaushe zaki ajiye wannan lame compliments din naki ba, Fairoz. Zaki barmu mu shigo ne, ko mu juya?" tayi dariya, "manta dani, Wallah murna ce ta cika min ciki... Ta'al!". Sheerah ta raba ta gefenta ta shige cikin gidan. Sai lokacin Fairoz ta kula dasu Aafreen. Ta rungume Sisi tana murmushi, "Fadim!", ta kama hannun Aafreen, suka shiga cikin gidan, ta maida kofar ta rufe.
Kan fararen leather seats dake jere cikin falon suka zauna, ita kuma ta shiga kicin da sauri ta dauko musu tatacciyar madara da ruwa, ta kawo ta zuba a cups duk ta mika musu. Aafreen tayi murmushi bayan ta sha ruwa ta ajiye cup din akan table. Tace "Assalamu Alaikum, Amtu Fairoz".
Tayi murmushi tare da rungume yarinyar tana shafa kanta, "Wa alaikumussalam little one. Well, aren't you getting prettier each time I see you?!". Sheerah ta kada idanu, Aafreen kuma ta sadda kanta kasa tana murmushi, a kunyace.
Ta maida kallonta ga Sisi wadda idanunta suka fara rufewa alamun barci, tayi dariya sosai tace "ki shiga daki ki kwanta mana, idan kin tashi daga barcin naki sai mu gaisa sosai ko?" ba musu ta mike ta wuce bedroom.
Ta daga murya tace "Mahboobi! Yallah, ku zo ga Amtu da Aafreen!". Ai ba bata lokaci yaran suka fado falon a sukwane, kyawawan yara maza, dan kimanin shekaru tara, biyar da mai daya wanda yake tafiyar tangal-tangal. Har rige-rigen wanda zai fara zuwa wajenta suke, da sauri ta tashi ta suri karamin, ta jefa shi sama ta cafe tana dariya. Fairoz ganin yaran sun lullubeta yasa ta basu waje tana murmushi. Kicin ta koma ta cigaba da hada cake din da take kafin isowar su Sheerah.
Har ta gama bata daina jiyo hayaniyar su ba a falon. Gabadaya sun karade wajen da hayaniya kamar gidan biki. Ta kwashi cupcakes cikin tray ta koma falon. Sheerah na zaune a kasa ta cire gyalen kanta, tattausan gashinta ya bazu a gadon bayanta yana ta sheki. Khaleel yaronta na uku yana kan cinyarta tana taya shi hada puzzle pieces dinshi. Tameem yaronta na biyu kuma yayi matashin kai da cinyarta yana wasa da sumar Khaleel. Mahboob kuma ya saka fresh fruits data kai musu yan ci.
KAMU SEDANG MEMBACA
Doctor Sheerah! (SAMPLE ONLY)
SpiritualRayuwarta, farincikinta, damuwarta, tashin hankalinta, komi nata ya ta'allaka ga mutanen nan su biyu ne kacal! Su kadai take kallo taci gaba da rayuwa kamar babu wata damuwa a ranta, her world revolves around them!! Me zai faru lokacin da abubuwa s...