Twenty Three

2.3K 301 39
                                    

®Fikrah Writers Association🖊

                 ©Jeedderh Lawals

                            *DOCTOR SHEERAH!*

                                         •°23°•

Akwai lokuta da dama a rayuwa da zaka ji abu yazo maka kamar a almara, ko a mafarki. A irin wadannan lokuta, zaka ji ka kasa motsi kamar wani statue ko wanda aka tsayar, kaji lokaci da komi ya tsaya maka cak, kamar ana controlling abin da remote. Haka Sheerah taji.

Abinda ta dinga nanatawa a ranta shine, duka-duka yaushe suka gama waya da mahaifinnata? Ko cikakkun awanni biyar ba'a yi ba, data ji muryarshi. Cikin tsananin rawar jiki ta tashi tsaye, sai ta rasa ta ina ma zata tari abin? Daga karshe ta yanke shawarar fara sanar da Sageer tunda yana gidan.

Tun kafin ta bude kofar dakin take jiyo alamun sautin magana da karan TV kasa-kasa. Jin an ambaci sunan mahaifinta da wasu takardu, yasa ta fasa tura kofar dakin, amma ta dan bude kofar dakin kadan ta yadda take iya hango Sageer dake zaune akan kujera da waya dafe a kunnenshi.

Sageer ya cigaba da maganar da yake yi kafin Sheerah taje, "... A'ah, babu matsala. Kawai tunda komi ya kammala shikenan. Ka tabbatar komi ya dawo sunanka?" yayi shiru, kafin yace "Allah ne ya rage mana wahala, da ai har nayi hayar designated driver, wanda zai karasa shi a hanyar airpot, yayi faking abin ya zama kamar accident, sai kuma nake ganin labarin crashi din da jirgin yayi yanzu!". Sheerah taji ya sake saurarawa kafin ya saki wata dariya, "... Ina! Me wannan yan tsakin yaran nashi zasu iya? Ai komi nashi ya riga ya zama namu, mallakinmu. Duk wadda tayi kokarin kawo mana cikas, I'll just finish her!! Shima wancan gaulan, wanda yake auren babbar, naji yana wani ihu da daga jijiyar wuyan ba zai yarda da plan dina ba, that sai inda karfinshi ya kare wajen ganin ya tsayar da plan dinmu, shima zanyi maganinshi idan bai kiyayeni ba...".

Ya sake yin shiru, "come on mana, Dad! Duk da dan'uwana ne, ai bai kamata in barshi ya ruguza mana shirin da muka dauki dogon lokaci muna shiryawa ba. Sai yanzu da muka tsinci dami a akala, kuma yazo yace zai yi bata mana shi? Wallahi karya ne...!".

Dauriyar duniya da takatsan-tsan, Sheerah ta aro shi ta yafa a cikin zuciyarta a lokacin. Ta maida kofar ta rufe, ta koma ta jingina da kofar dakin, idanunta a rufe, tana jin zuciyarta tana wani irin bugu da tsalle, kamar zata fasa kirjinta ta fito waje.

Ko mara tunani, yasan cewa Sageer da mahaifinshi zancen rasuwar mahaifinsu suke yi. Ba jajen mutuwarshi ba, ba bakincikin rasuwarshi ba, ba tausaya musu suke yi ba.  A'ah, murnar rasuwar shi suke yi, da murnar sun tatuke duk wani abu daya kasance nashi, sun maida shi nasu suke yi. What a cruel world!!.

Sai lokacin duk wani guntayen pieces da tambayoyi suka dinga amsa kansu, pieces din na hada hoto waje guda. Haba!, biri yayi kama da mutum. Dalilin da yasa Sageer din yake zaune da ita kenan, duk daya fada da bakinshi cewa baya sonta, baya kaunarta. Saboda kudin mahaifinta ne!.

Wani irin son kudi ne haka, da zasu yi tunanin kashe mata mahaifi saboda su? Har mahaifinta ya mutu, amma su daga baki suce wai Allah ne ya rage musu wahala? Anya, akwai tsoron Allah daya rage a duniyar da muke rayuwa kuwa? Meye kudi? Meye kudin? Kudin da suke masifa ne da bala'i kawai? Amma a kansu har mutum yace zaiyi kisa, ta matar da yake aure har da dan'uwanshi? Subhanallah!!.

Idanunta sun rufe da hawaye, kafafunta na rawa cike da tsoro, tasa kafa ta bar gidan. Ko mayafi bata dauka ba. Kai tsaye gidan Fadima ta shiga. Ashe bata gama ganin tashin hankali ba a ranar.

Hisham tsaye da Fadima suna sa'in'sa mai zafi. Fadimar na kuka tun karfinta, haka taga Hisham din ya bi ta gefenta zai wuce, Fadimar tayi sauri ta riko hannunshi. Bai yi wata-wata ba, ya juya ya zuba mata mari a fuska. Karfin marin yasa ta tafi gabadayanta ta zube a kasan tile din, karan sautin bugewar da kanta yayi har inda Sheerah take, sai da tsikar jikinta ta tashi.

Doctor Sheerah! (SAMPLE ONLY)Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt