Eleven

2K 254 44
                                    

®Fikrah Writers Association🖊

                 ©Jeedderh Lawals


'But you will never be alone,
I'll be with you from dusk till dawn.,
Baby I'm right here.
I'll hold you in this forearms, I'll be with you from dusk till dawn.,
Baby I'm right here~~~
Baby I'm out here....'
         Zayn Malik ft Sia-Dusk Till Dawn

Cikin ikon Allah, Allah ya dafawa AbdulHakeem, kamar a mafarki. Sai gashi shima ya bude kamfani nashi na kashin kanshi a cikin garin Dubai. Babu abinda ba'a kerawa a kamfanin wanda ya danganci fannin kayan ado da kawa. Kwata-kwata sai zaman shi a Nigeria ya ragu nesa ba kadan ba, gabadaya harkokinshi sun koma Dubai.

Shi da dangi da yan uwa ya zama sai dai gani daga nesa, ko ya daga musu hannu idan ya wuce a cikin dankara-dankaran motocin daya saya yake hawa. Dama can AbdulHakeem akwai dagawa da daga kai, balle kuma da yayi kudi ai sai abin ya hauhawa. Musamman yasa aka gina mishi dankareren gida a Kano cikin unguwar Sharada, gini ba na wasa ba. Duk lokacin daya zo Najeriya can yake sauka, idan ya huta sai ya shiga Kazaure yaga mahaifiyarshi sannan ya koma. Bayan nan ya sake sawa an buge gidan dasu Adama suke zaune gabadaya an kankare musu gini na zamani, ya kuma kai musu an aiki ya zube musu. Duk da dai da sashen Adama kadai yaso gyarawa, sai da suka kai ruwa rana sosai da Adamar, har tace idan ba duka gidan zai gyara ba to ya bari bata so, kafin fa ya amince ya gyara gidan gabadaya.

A hankali Al'amura suke kara bude mishi ta kowace hanya, kofofi na samuwa da alkhairi na sake budewa. Dadi na duniya dai Allah ya bashi. Har lokacin bai yi aure ba. Adama da Na'u har ma da Ya Hamza sunyi iyaka kokarinsu. Na'u har hoton yanmata take aike mishi wai ya zaba, sai dai yayi dariya yace lokacin yin auren ne bai yi ba, idan yayi zai yi koda baya so kuwa.

Kawai ranar nan yaje Qatar kan wani kamfani da suke son yin hadin gwiwa dashi, cikin ikon Allah sun daidaita komi saboda gingimemiyar ribar daya hanga zasu ci. A cikin jirgi ya hadu da Hana. Har zuwa lokacin tana nan a yadda ya santa; fara tas kamar ka tsaga jini ya fita, kyakkyawa ta gaban kwatance da dara-daran idanuwanta farare tas kamar madara.

Yace "Hana ce da gaske?" ta daga fararen idanuwanta da suke rikita shi, ta haske shi da murmushi mai kyau tace "kamar dai yadda ka gani AbdulHakeem. Ya kake?". Hira ta barke tun daga tashin jirgin har ya sauka a Bahrain. Nan ta mike tana rataya Jakarta, tace "to ni nazo masauki fa, sai gani na biyu kuma?".

AbdulHakeem yaga cewa babbar dama ce tazo mishi, bai yi kwauron bakin tambayarta ba, "Kinyi aure?" tayi dariya, "what? No, banyi aure ba" yace "saurayi fa? Engaged??" nan ma tayi murmushi, "ko daya" yace "good... Bani lambar wayarki please, zan kira ki idan na sauka". Nan suka yi musayar lambar waya, ya mika mata katinshi. Ta zare ido sosai ganin sunan kamfaninshi, "you are the CEO?". Ya sakar mata murmushi cike da jindadin yadda idanuwanta suke twinkling in amusement. Jin ana sanarwar tashin jirgi yasa ta mishi sallama ta tafi.

                ☆☆

Hana Mas'oud balarabiyar kasar Bahrain ce wadda ta kasance ruwa biyu. Mahaifinta dan Bahrain yayin da mahaifiyarta ta kasance yar Syria. Mahaifanta sun rasu a wani hari da aka taba kaiwa Syria, lokacin sun je musu hutu. Dangin mahaifiyarta suka ki karbarta, don haka aka maida ta hannun dangin mahaifinta, wajen kakarta. Lokacin da kanwar mahaifinta Siddiqa tayi aure, ta dauketa ta maida hannunta taci gaba da kula da ita. Kusan a hannun Siddiqa ta tashi, duk da cewa sauran danginta suna hidimta mata. Da tainakonsu tayi karatunta ta gama har gashi yanzu tana neman aiki.

Taje Qatar wajen sunan wata cousin dinsu data haihu, a hanyarta ta komawa gida ne ta hadu da AbdulHakeem.

Kamar yadda AbdulHakeem yayi alkawari, a daren ranar ya kira wayarta. Bai tsaya wani kauce-kauce ba, ya sanar mata aurenta yake so yayi, ba kuma tare da bata lokaci ba.
Sai yayi sara akan gaba, itama a gida dama an takura mata akan ta fitar da mijin aure, har ma daya daga cikin uncles dinta ya nemi hada aurenta da babban danshi Qaseem, amma Hana ta kekasa kasa tace bata son shi. Don haka suka ce to ta fitar da mijin aure. Don haka babu bata lokaci itama ta amince mishi. Cikin dan kankanin lokaci soyayya ta kullu a tsakaninsu. Yace ta fada a gidansu zai turo neman aurenta.

Doctor Sheerah! (SAMPLE ONLY)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang