💞👱🏻♀HUSNIYYA*
KO
*HUSNAH👩💞By ©UmmySaudat✍
*Inspired by TRUELIFE events🗓*wattpad_ummysaudatt
14_
Aliyu cikin madaidaiciyar motarsa qirar honda yake tuqi ransa fes dukda deep inside hankalinsa na kan husniyya daya baro a gida ba lafiya duk da yasan ordinary fever ke damunta,daidai wata pharmacy dake bakin titi ya paka motarsa ya fito, fuskarsa cikeda fara'a yake kallon samarin dake gun maqil zaman majalisa,"ho ango,ho likita,angon husniyya,likita bokan turai,zaki nagari na kowa" kirarin da samarin ketai ma Aliyu kenan idan wannan ya soma wannan ya amshe,shafa kansa yai da murmushi kan fuskarsa ya qaraso gunda suke suka gaisa dasu cikeda sabo da girmamawa,dan gun duk area'n unguwar su ne,ya dan jima a gun suna taba hira kan ya tashi ya shiga pharmacy'n,ba'a dau wani lokaci ba ya fito riqe da ledar dake cike da tabs da lozenges,hannu ya daga ma samarin dake gun,"buddies,to Allah ya bamu alkhairi" ya fada be saurari maganganunsuba, ya nufi gun daya paka motarsa yasa mata key kan ya zagayo drivers sit ya zauna tareda tayarwa ya nufi kasuwar tarauni,
ba'a dau wani lokaci ba ya fito daga kasuwar riqe da ledodi hannunsa da alama kayan cefane ya sayo sai fruits,kamar me nazari yake kallon digital watch din dake wrist dinsa which spells 11:8 am,kan a hankali ya tada motar ya nufi unguwa uku gidansu husniyya,cikeda ladabi suka gaisa da momy,dan itakadai ce yanxun a gidan,mahaifinta Musa Na'Allah mutumin arziqi dan kasuwa ne na fatauci hakan yasa ba'a fiya samunsa gida ba,sai wanta Abdullahi wanda suke cema Abba shi kuma yana aiki a Nigeria AIRFORCE inda yanxu haka yake airforce base headquarter kawo,kaduna,daga shi sai husniyya,sai kuma yar autarsu fatima da yanxu haka take SS1 a GGSS dala,
kansa na qasa yace,"Abba har ya koma kenan",momy dake zaune kan tabarma tana yanka lettuce murya a sake tace"ai kai da ganin babansu gidannan sai qarshen sati",ta fada tana qoqarin miqewa,"bari ganinan fitowa,saqo zan baka ka kaima dota" ta fada hadi da shigewa dakinta,Aliyu dake zaune kan plastic stool wayarsa riqe hannunsa yaji kirana shigowa, guntun tsaki yaja yana katse kiran tareda maidashi silent ba tareda ya duba me kiranba,ba'a dauki lokaci ba momy ta fito riqe da wata doguwar jakar leather bag ta miqama Aliyu tana fadin,"karna hadaka da aiki kuma,fatima ce yar aiken tawa,gashi ta koma makaranta shys",cikeda da ladabi ya amshi jakar yana murmushi bece komai ba,ledar da ya shigo dashi wanda ke cike da groceries da fruits ya ajje gefe kan ya miqe,"baka gajiya da hidima Ali,to Allah yayi albarka,ai daka tsaya ga abinci nan ya kusa" momy ta fada fuskarta fal fara'a,"Alhamdulillah,sai wani lokacin kuma" ya fada kan ya nufi hanyar qofa,
"ka ringa haquri dan Allah,nasan halin dota,Allah yayi muku albarka"
"Ameen Umma" Aliyu ya fada,
"to shikenan ka gaidamin su hajiya an kwana biyu ba'a hadu ba",
"zasuji insha Allahu",ya na kaiwa nan yai exiting gidan hadi da yima momy sallama,
gidansu dake hotoro ya nufa ya gaida iyayensa cikeda ladabi da kulawa kamar kullum harda hidima,kan ya fice gidan dukda rikicin da yar autarsu fadeelah tai tayi masa na sai ya tafi da ita,da qyar ya sulale mata hadi da tabbatar mata gobe idan yazo zai kaita,unguwar tarauni ya nufa gidansa,zuciyarsa fal tunanin sanyin idanunsa,
**********************
bangaren su husnah da yusif ko kullum jiya i yau,ranar laraba qarfe 12:45 noon husnah ce cikin kitchen dinta duk attention dinta na tattare kan girkin da take,sanye take cikin tsadadden cut lace dinta brown me ratsi ratsin baqi a jiki wanda akaima fitet gown,kayan ba qaramin amsar jikinta yai ba,duk da cewar kallo daya zakai mata kasan cewar she is deeply stressed,green onions din dake hannunta take smashing duk da hankalinta baya gun aikin da take,
hajja ce cikin babban sitroom dinsu zaune kan sofa,da wata yarinya data tattara hankalinta gun baqin hennah'r da take zanama hajja flower,"ja'irar yarinya,ki gogen zanennan nace miki banson irinshi" hajja ta fada cikin fada tana nuna qafarta daya,yarinyar dake mata qunshin cewa tai,"ya riga da ya kama,idan aka goge zai baqinsa zai bata qafar" ta fada a taqaice tana maida hankalinta kan qunshin da take zanawa,mugun kallo hajja ta watsa mata,har ta bude bakinta zatai magana ta fasa sakamakon fiiton da taji anayi,dubanta ta kai gun wanda ke fiiton tana jan tsaki,"ai daman nasan sai kai,asararren yaro,mara kunya kawai" ta qare maganar tana kallon Sultan dake jinjina kansa yana rausayawa kamar zararre duk da haka be fasa fiiton da yake ba,gun dining ya nufa ya bude warmer hadi da rufewa yana jan tsaki,"ke dan uwarki wayace ki girka wannan" ya fada cikin daga muryarsa,me girkinsu indo dake gun tana jera abincin data idda girkawa bakinta na rawa tace,"hajja ce ta buqaci a dafa" tana kaiwanan tai kitchen qafafunta na hardewa,gun hajja yaje yana mata qunquni dan duk iskancinsa yana dan shakkar yimata dan yasan halinta sarai,"wai kai wani irin dan banzan yaro ne ehe,fitina bata taba qare maka,yaran zamani ga abincin kun samu kuce sai kun zaba,shima yusufa ga abinci a gida ana girkawa,tun da yai aure yace sai girkin wancar yar'iskar matar tasa" hajja ta fada cikin sababi,
Sultan dake tsaye gun hararan gefen ido ya watsama hajja,"masifaffiyar mata kawai" ya fada cikin ransa a fili yace,"tunda basona akeba in yaso yunwar ta halaka nima,no one cares dama" ya fada a harzuqe hadi da juyawa zai fice daka gidan,cikin fada ya jiyo muryar hajja na fadin,"dan ubanka ka kuskura ka fita gidannan sai ranka yayi mugun baci,in bazaka bangaren yusifa kaga ko ta idda girkinta ba,baga indo ba,yo me amfaninta" ta fada tana jingina kanta kan sofa tareda jan tsaki,
Sultan ko shu'umin murmushi yai yana cizan lips dinsa kan ya nufi bangaren yusif da hujjarsa,ransa fes,
a kitchen ya tadda husnah tsaye tana wanke wanke ta tap basin ta bashi baya,hadiyar miyau ya shiga yi yana kallon curved figure'nta cikin sassarfa yai saurin cakumota ya rungumeta ta baya a qanqame,husnah da take gabanta ya soma faduwa cikeda mamaki ta juya dan ganin ko waye dan tasan ba yanzu yusif ya saba dawowa gida ba kuma a halin da ake ciki ko bi ta kanta bayayi,ganin Sultan yasa cikin tashin hankali me yawan gaske ta bude bakinta zata kurma ihu,yai saurin rufemata bakin da hannunsa yana kallon idanunta,"shshsh,ba yanxu ba tukunna,calm,me kike ci na qasa na zuba,hold ur breath sexy,ki huta iya son ranki tukun,abinci nazo ci,thats all" ya fada yana shafa qugunta,iya qarfinta tasa gwiwar qafarta ta doki gabansa,hakan yasashi sakinta ya durqusa yana feeling yadda gun ke ciwo,husnah da qwalla ya taru cikin idonta qoqarin maidashi tai cikin tsiwa tace,"kashedi na qarshe ka fita harkata,gudun magana yasa na kai i yanxu ban fadama yayanka ba,dan banson ace nice sanadiyar hada husuma" ta fada tana hararansa idanunta kamar zasu zazzago kan ta cigaba da fadin,"kuma tir da halinka wlh,dan iska asararre kawai,baka ji dadin halinka ba,uwarka tayi asara..",bata ankaraba taga ya shaqo wuyanta,"wahalliya kawai daqiqiya,taurin kanki be isa ba,yayi kadan yarinya,coz this is just d beginning",ya fada yana zare mata jajayen idonsa,qoqarin hade bakinsu yake husnah tai saurin turasa,a rude tai saurin kai hannunta gun wuqar dake gefe ta dauka tana nuna masa,itama idanun ta zare masa tana fadin,"idan ka cika dan halak ka matso kusa,just more closer,kaga yadda akema mutum yankan rago" ta fada tana kuma nuna masa wuqar fuskanta sam ba alamun wasa, idanunta tuni suka kada suka koma ja,sultan dake tsaye gun ko a jikinsa in banda dariya ba abunda yake dan yasan ba abunda ta isa tai masa,sai da yai me isarsa ya tsagaita yana fadin,"haba sexy,me yai zafi kuma,chill,bari kiga tafiyata" ya fada hadi da ficewa yana qoqarin saita kansa,a sanyaye husnah ta sulale qasa hawaye na bin kuncinta,cikin tarin baqinciki take kallon wuqar dake hannunta,yayinda taji abubuwa da dama na mata yawo a ka..........®*Saudat Adam Isah*
SUNNY SMILES
UmmySaudat
YOU ARE READING
HUSNIYYA KO HUSNAH
Romanceam i really in d shoes to say something, as in right now, no pls spare me, am damn happy plus scared at d same time, buh never mind,lemme try my best with dis masterpiece, to fah,ga wata sabuwa wai inji 'yan caca, this is a truelifestory #HUSNIYYAKO...