41~babu tsammani

464 15 0
                                    

🍀****🍀****🍀****
*HUSNIYYA KO HUSNAH*
****🍀****🍀****🍀
 

By  ©UmmySaudat✍
*Inspired by TRUELIFE events🗓*

®*Saudat Adam Isah*

41_

sai da Husnah tai kusan awanni biyu tsaye titin ba wanda ya kulata,
qarshe ganin da tai tsayuwarta gun babu cigaba sai ma qangi da uquba da ze jaju'bo mata,dan sanin yanxun dayan biyu ne,ko azzaluman mutanennan sun gano bata nan ko kuma by now har sun taho bin diddiginta,
ai da wannan tunanin Husnah ta ringa daurewa tana tfy cikin tsananin fitar hayyaci da gajiya,ga qishin ruwa da yunwa datakeji,bugu da qari ga yadda takejin cinyoyinta zuwa guiwanta yadda suke wani irin tsami na radadi dan durgowan datai daga katanga,amman sam a yanxun bata bi ta wannan,kawai ta ganta a gida ne rest of mind,
hk ta cigaba da lallabawa tana tfy,a lkc guda taji wani azababben abu ya danne mata wuya da qirji wanda ya haddasa mata wani masifaffen tari,ta durqushe nan tanata uban tari a wahalce kamar ta amayo yan hanjin cikinta,
dai dai lkcn wasu 'yammata biyu suka bullo daga wani lungun dake kusa da inda take a durqushen,ko wacce da qwaryan nono kanta dan da gani fulanine dan shigarsu,
cikin bazata suka sauke idanunsu kan husnah a halin da take cikin ga yadda take zigidir haihuwar uwarta da ubanta dan tuni kayan jikinnata suka kama gabansu dan dama sunci ubansu,ga yadda jikinta yai daqal daqal da datti,babu ko masakar tsinke,
hkn ya haddasa musu 'yar komawa baya a firgice hannunsu dafe kan qirjinsu suna qwalalo ido dan a zatonsu irin miyagun mahaukatannan ne,husnah'n da tuni ta dago kanta tana kallon su same time qoqarin saisaita tarin da take tai,a wahalce ta iya fadin,"kuzo ku taimakeni dan Allah,mutuwa zanyi" ta qare zancen tana fafutukar miqewa da niyyar tunkararsu,
ai wani gigitaccen qara dukkaninsu suka saki suka ruga da gudu dan taimakon da Allah yai musu din qwaryan nonon dake kansu bata fado ba,
"idan kunaima Allah ku tsaya,ku tausayamin,wlh ni ba abar gudu bace,taimako nake nema",husnah ta cigaba da fada cikin kuka tana zubewa qasa a raunane,
sai a sannan naga 'yammatannan sunyi tsaye gun da suke suka juyo a sanyaye suna kallon husnah data kife qasa,kallon junansu sukai sannan naji suna magana da yaren fillanci muryansu qasa qasa,sai da suka gama gwarancinsu dan ni ba ji nake ba,kan a hnkl suka tako har gaban husnah suka dafata,daya cikinsu ce tai magana cikin hausantan dabe gama qwari ba,"amman baiwar Allah kuma da qoqolwonkin muka ganki hk?",dayar ta amshe,"ki daga kai ki fadi,ko mun iya temakonki",
Husnah dake duqe tana jin su sai a sannan ta iya dago kanta tai qoqarin fadin,
"dan Allah ku taimakamin da suturar da zansa,wlh barayin mutane ne suka daukeni,suka rabani da 'dana da Mijina,bansan a inda nake ba bare nasan hanyar komawa gida,ku taimakeni",cikeda tausayinta daya cikinsu ta koma gida ta dauko mata sutura irin nasu na fulani,har ta samu ta saka,nan  sukai mata tayin nono,du da bata san ko zata iya shan wani abu ba,hk ta amsa ta kifa kai cikin sa'a ta dan ji sa'idah ba kamar da ba,badan abin data sha ba sai dan tasan ta gamu da wa'anda zasu share mata hawayenta,
hk ta ringa gode musu hadi da tmbyrsu nan gun ina ne kuma ta qara da tmbyrsu taya zatai ta iya shiga cikin garin Kano,nan suka ce mata nan din Falgoren Dajine kuma suma daganan din tashar qofar wambai na Kano suka nufa kamar yadda suka saba zuwa tallen fura da nono,cikeda jindadi husnah ta bisu har suka samu wata motar bus suka hau,ganin anzo daidai gadar nassarawa ne yasa husnah tsaida motar da niyyar ta sauka sannan ta juyo tanata wurga ma bafulatanan godiya qarshe tai musu sallama zata fice motan,nan aka hau wani sabon rigima da conductor dan rashin kudin da zata biya kudin mota,hk aka ringa yi har wani cikin motan yace ze biya,ta fita tana tunanin yadda za ai ta koma gida,
tana cikin wannan tunanin ikon Allah kamar daga sama ya jefo yayarta Saudah cikin mota tazo giftawa,a fuzge sight din idonta ya nuno mata Husnah inda take tsaye gefen titi ta jingina da wata motar Daf banda hawaye ba abinda ke bin kuncinta,
juyowa tai a hanzarce ta kalli gun dan tabbatarwa,"kamar HUSNAH TA",ta fada kan harshenta tana jinjina kai da surprise expression shimfide fuskanta,cikin ranta ta cigaba da fadin,"no,am not mistaken,Husnahta ce wannan,buh how comes....",babu shiri ta katse zancen datake cikin ranta,a gigice tai saurin taka birki dan ganin sauran kadan ta bugi motar dake gabanta,
ai 'daga kan da zatai tai ido hudu da wani gardin mutumi gaban glass din motanta, banda masifa ba abinda yake kwararowa du da ba jin abinda yake fada din take ba dan a zuge ilahirin glasses din motan suke,mutumin sai faman qwanqwasa mata glass din yake a fusace kamar ze fasa,
kallon banza ta shiga wurga masa,"aikin banza kawai,kanka ake ji de",ta fada daga cikin motan dan batai gigin bude murfin ba,sannan ta kifa kai da steering tana tunanin abubuwan da suka dameta,sai datai kusan minti 3 kan ta dago kanta ta sauke ajiyar zuciyan samun relief dan ganin har mutumin ya tafi,daga bisani ta bude glasses din motan,ai wasu uban horn din datai taji kamar ana yaqi ne yasata saurin juyowa taga tarin motocin da suka tsaya sakamakon tare musun datai,wani kafirin tsaki taja,a qule taja motar ta paka can gefe tana kallon yadda du wanda yazo wucewa sai ya mata mugun kallo yana tofa albarkacin bakinsa wasu har daquwa suke wurgo mata,"tsinannu,to uwarku kuka zaga bani ba",ta fada tana kallon gun data hangi Husnah daxun,amman wayam taga batanan,"to waya sani ko gizo takemin,dat's telling me just how much i've missed ma sweet sis...",tana tsaka da zancen da take taji muryan Husnah hkn ya sata saurin daga idanunta,"Yaya ki bude min ki maidani gida,ina son ganin Haneef",husnah ta fada cikin dariyan da bata san dalilinsu ba,hararanta Saudah tai ta bude murfin a sanyaye tana kallon Husnah from head to toe,Husnah ta shigo da sauri ta rungume Saudah tana fashewa da kuka,a tuhume Saudah ta dago ta,"what's with all these,just take a good look at ur self mana",
ta qare zancen still sai kallonta take tayi galala,
cikin wani yanayi me wuyar fahimta husnah ta shiga goge hawayen dake zubo mata,muryarta na rawa tace,"pls stop looking at me like dat,ni a yanxun nothing matters to me,kawai ki kaini inga 'dana da mijina shi ne zan samu kwanciyar hnkl",hk Saudah tai ta insisting husnah ta fada mata abin dake faruwa amman tai ta kaucewa itade akaita taga gida tukun,har Saudah ta gaji ta qyaleta,qarshe taja motan ta nufi unguwar nassarawa GRA,yayinda ko wacce keda abubuwanda take saqawa a rai,husnah haka kurum taji gabanta na faduwa tana jin maganganun yusif na mata yawo aka,
_"kuma from now on nake so kisan,na goge sunanki matsayin matata","Yes i dont love u,kuma ni Yusuf Maitama Umar,nace na sakeki Husnah Isah,saki Daya,Biyu,Ukk..."_
"No No No...",ta ringa nanatawa da qarfi tana marin both cheeks dinta da hannayenta,cikin tashin hnkl Saudah ta paka dan har sun iso qofar gidan,
"na shiga uku na yau",Saudah ta fada cikin damuwa tana kallon reaction din Husnah ga yadda take ta kiciniyan bude murfin motan,tana jijjigawa a rikice cikin ihu,amman yaqi buduwa,sai da Saudah ta bude,Husnah ta fita a sikwane,
ganin wani qaton kwa'do jikin gate dinne ya soma tabbatarmata da cewan yau din qarshenta ya zo

SUNNYSMILES,
Ummy_Saudah

HUSNIYYA KO HUSNAHWhere stories live. Discover now