Innalillahi wa inna ilaihi rajiun.....
Cutar Covid19 taa zama Annoba gama duniya,
A wannan lkc mafi dacen abinda musulmi zeyi shine komawa ga Allah,mu fawwala,mu yarda cewan wannan kaddarace,ko meye ya same mu,daga garesa ne,
Kuma shine ze yaaye,mu yawaita istigfari,da zikiri da salatin Annabi SAW,bamu da tsimi bamuda dubara se yadda Allah yai damu....
Ya Rabbi kasa mu cika da kyau da Imani....
Ameen ya rabbussamawati wal ardi....🍀****🍀****🍀****
*HUSNIYYA KO HUSNAH*
****🍀****🍀****🍀
By ©UmmySaudat✍
*Inspired by TRUELIFE events🗓*
®*Saudat Adam Isah*
wattpad-Ummy_Saudah57
Babu abinda ze hana rayuwar duniyar nan cigaba da tfy face ko wani iko na Allah,
Rayuwar da take tfy a yadda Allahu me sama yaso a yadda kuma yaso da bayinsa...2yrs later,
Alhamis,
11:28am,da safe,Hasken ranar data bullo daga karamar taagar dakin ne ke tsaka da sauka a saman santalelen fuskansa,mutumin da ake gani kwance bisa wata yar yaloluwar katifar dana laqana ma sunan kanwar babu,
Tafin hannunsa kaare a fuskar,yake juyi alamar farkawa daga barcin da bisa alama yaa dauki tsawon lokaci a cikinsa,
Bakinsa naa fasa salati yake cigaba da mirtsika idanun da suka kankance,
Zuciyarsa naa ambato sunan husnah ya mike ya janyo jallabiya ya rufe tsiraicinsa yai waje,
Aliyu Lawan Sarki,wanda a cikin kallo guda zaka kirga canzawan dayai tsakanin wa'annan shekarun,
A yanzun yanayinsa yaafi nuna alamar kuzari,irinna matasan karkarannan masu jini a jika,
Kyakkyawan fuskarsa taa fara nuna alamar girma irinna older youths,
Yalwatattun gaashin da suka taaru a fuskansa wanda baa wani gyaran arziki suke samu ba,da kuma 'dan duhun da fuskan yai ne ababen da suka tauye masa kyawu idan an hada da shekarun baya......Later,
12:22pm,'A'uzubillahi.....'
Tai baya firgigit tana watsa idanuwan mujiya ma fuskar mutumin dayasha gabanta,
'Bawan Allah lfy!
Don meye zaka biyoni har nan',ta kawo cike da bacin rai,
'''Yammata tunda har kikaga inata bibiyarki hk...meye yasa bazaki tsaya ki saurare ni ba',ya fada a nutse yana kuma kureta da mayun idanuwa,
Hkn yasata kuma hade rai don babu abinda yake bata haushi irin a ce da ita y'ammata,
yayinda ta tsinci kanta da k'are ma mutumin kallo,da akwai kyawu da kamala amman ita bata ga wani abinda ze birgeta jikin wani d'a namiji ba bayan Aliyu,tana matsawa gefe had'i da maida dubanta ga marikar ledar cefanen dake hannunta wanda yake dab da tsinkewa ta auna tsaki taja da takaicin ita daa taa shina taa tsimayi Aliyu yai mata rakiya daa taa tsira ma uwar wahalar kasuwarnan,bugu da k'aari gaa jarabar wannan aljanin mutumin,
Ko da shike ma tunda surprising dinsa take son yi da abinda ya kaita kasuwan,baze zama surprise d'in ba idan dashi aka tafi sayen abin............
Zantukan da suka iske kunnuwanta ne abinda ya datse mata tunani,
'Haba sarauniyar masu kyawu,babu wani abin bacin rai a nan wurin ai....wlh ni babu abinda ya kawo ni gare ki idan baa alkhairi ba,wlh tun a kallon fark...........''Dakata malam,
Don ni kaa ga tafiya ta'
Ta shige cikin gida fuu ta barsa nan da kada kai yana sakin guntun murmushin,dayafi kala da yake,
Husnah Isah,warce ko da kallon kurillah ka bita tsaf ze yi wuya ka ga wani canji a tattare da kamanninta,kaama daga farin faatarta,fuskanta,zuwa zubin dirinta....'Assalamualaikum',
Duk suka amsa sallamar yayinda Aisha yarinyar da zatakai shekara 9,
tai zumbar daga aikin tsince shinkafar da take cikin azama ta duri gaban husnah,
'Ga Adda,
Ga Adda'
Ta fa'da cikin murna ta na kokarin amsan ledar vivar dake hannun husnah,
ai yin hkn yake da wuya ne hannun ledar ta ida yagewa,
'Subhanallah',
Husnah ta furta,duk suna kallon kayan da suka samar ma kansu masauki a kasa,
'kika kuskura kika bari na iso na iskeki tsaye wurinnan Alquran se naayi mummunan sa'ba maki'
Aishar da tuni idanun sukai zonzono turo baki tai cikin rashin gane takamemen abinda mahaifiyartata ke nufi,
'Bazaki tsugunna ki kawar da ta'adin da kikai a wurinnan ba dan ubanki',a tsawace akejin muryan Asiyah,warce ke gefe guda zaune bisa tabarma tare da wata yar budurwar da take zanama fulawar bakin lalle,
'A'a wlh husnah bazaki tab'a abinnan ba',
ta mike a sikwane ta dauko bahu ta wullama Aisha,
'Husnah zauna ki huta gajiya naa san wahalar sayayya a ranar da kasuwa keci'
Ta ja husnah har se data zauna,ta dibo ruwan sanyin randa ta mika mata,
Asiyah naa tsaye tana kallonta ta shanye ta sauke numfashi ta ajje kofin,
Daga bisani Asiyar ke fadin,
'Ke! in baa ki labari...... yanzu yanzunnan mutuniyarki ta bar gidannan'Husnah na fifita da bakin mayafin data cire ta dubi Asiya da fadin,
'Wai ko baa Asabe ba?'
Asiya tai shewa ta mika mata hannu suka tafa,'ai naa so daa ta iske ki naa bama idona abinci wlh,a yadda ta shigo gidannan naa san dole zaku hau sama ku fa'do....an hada abin maasu zafin kai''Kuma Wlh da rabon bazata bar gidannan da fasashshen jiki ba,don billahi Asiyah ban ki na mika hannu na mari fuskar duk wata yar iskar matar data nemi ta kawon rainin hnkl ba'
Husnah ta kawo cikeda jin haushin matar da ta kira da Asabe,in banda rainin wayau da dakikanci irin na wasu mutanen karkaran wai taya za ai ta sayar ma mutum kaya ya dauki wani lkc harma ya kode sannan mutumin ya dawo yana kurari da magiyan shi baa me kyau bane ba a basa kudinsa kawai ko a canza masa da wani sabon,ubanta....
Ta saki tsaki da wannan tunanin tana sauraren Aisha,
'Adda gaa Naira hamsin din da aka sai lalle da murtalan da aka sayi kurkur'
Cewan Aisha tana mikama husnah kudin dake hannunta,
'Yauwa sannu indodo',ta fada tana bin Aisha irin kallon 'dama ace haneef dinta ne suke tare hk',taasan yanzu yaa girma kaman Aisha,Allah ya raya mata haneef,Allah sa tana da rabon sake ganinsa,
Kawar da tunanin tai da janyo bahon dake gabanta wanda Aisha ta ajje,
Dankalin hausa ne,da bunch din plantain wato agada,da danyen kayan miya,
Se wata kullallen bakin leda a kai,ta kwance ta ciro yankakkun sandunan rake guda ukku,ta bama Aisha don ta wanko,ta faki Asiyar da tuni ta maida hnkl kan zanen lallen da take,sannan ta dauko wata 'yar jakar farin takarda ta bude ta leka tana duban abinda ke ciki sannan ta mayar,Murmusawa tai har ta tsinci kanta da d'aga kai tana kallon kofar dakin Aliyu,babu alamansa a gidan,
tana ayyana,ko har yaa tashi din a barcin yaa fice ne,oho,
yalwata murmushin dake fuskar ta tai da tunanin d'aya daga cikin burukanta ze cika,shine ganin Aliyu a sanye da wani abinda yazo daga gareta,
dukkuwa da cewan baa yau ya fara sanya abubuwanda ta bashi ba,kawai wannan take ganin yaa fita daban don idan ya sanya ba abinda ze ringa cirewa ne ba,har abadan,
Abadan?,b'angarori da dama na zuciyarta suka tmbyeta,
cikin kyaftawa da bismillah fara'ar dake kan fuskanta ta gushe,wasu irin raunannun abubuwa suke neman su ziyarceta,
Da kokarin ta kawar dasu ne ta daddage ta auna wani irin gauron numfashi ta fitar,
Wanda har se da Asiyah ta juyo ta maida hnklnta gareta,
Da husnah ta lura da kallon Asiyah,se ta wayence,
'Ammmm......kaiiiiiii........wlh yau naa gaji dayawa fa,wai Asiyah ba de har yanzun goggo bata dawo ba',
'Hmmmmm....ai kema fa a zaman da kikai damu kinsan irin Goggo idan ta ziyarci taaron yan uwa ......don babu mamaki ma idan baki ganta har gobe ba'
Husnah naa d'aure ledar farin goron dake hannunta take fad'in,'gaa sautunta nan sede a ajje mata',
Asalin ledar data ciro wa'annan tarkacen se ya rage saura wasu beads beads,kala kala masu daukar ido,da kuma zaren strings dinsu wanda take amfani dasu wurin sana'anta,
Ta hada bakin ledar ta d'aure sannan tai dakin kwananta da kayan.........Unedited
STAI LEGGENDO
HUSNIYYA KO HUSNAH
Storie d'amoream i really in d shoes to say something, as in right now, no pls spare me, am damn happy plus scared at d same time, buh never mind,lemme try my best with dis masterpiece, to fah,ga wata sabuwa wai inji 'yan caca, this is a truelifestory #HUSNIYYAKO...