64~Al'amurran Zuciya

232 23 2
                                    

Unedited

****🍀****🍀****🍀
HUSNIYYA KO HUSNAH*
****🍀****🍀****🍀
By ©UmmySaudah✍
*Inspired by TRUELIFE events🗓*
®*Saudah Adam Isah*
wattpad~Ummy_Saudah

64

Wadannan alamuran dake faruwa baa karamin susuta Aliyu sukai ba,cikin 'dan kankanin lkc ya gama fita hayyacinsa,ba kad'ai husnah ba,don hartaa Aliyu ma abin tausayi ne,
Kud'ad'e baa karamin kuka sukai ba,
Har gidansa da gonan da ya mallaka a makarfi ya sayar,kud'ad'en basu tafi ko ina ba,a dawainiyan husnah duka kadaden suka b'ace b'at,
Aliyu shine karban rance a nan yau shine karba acan gobe,BVN number nasa na banki ya iya hadawa a kwakwalwansa da kyar,da yaje banki se yaci sa'a ya samu kud'ad'ensa yadda ya ajje a saving account d'insa,a nanne aka samu ya d'an dawo hayyacinsa,
Amma duk da hk ya hakikance ma kansa cewan lkcn komawansa gida yaayi, ze koma gida ya sanar wa dangin husnah halin da ake ciki,ze tafi ya fuskanci ko ma meye yake jiransa,yadda ze dawo gareta da karfinsa,
~

A yau Lahadi 2:15pm,
Goggo ce a ward din,don dama itace take jiyyan Husnah,
Goggo naa zaune bisa tabarman dake shimfide a gun tana zikr dan da alama bata dad'e da ida sallah ba,
Yayinda kallo daya zakai mata ka gano taarin damuwan dake tattare da ita,'yar karama a cikin damuwar itace,
rashin likitoci a asibitin da rashin samun kulawansu,don hartaa allurar ma da suke wa mara lfyn ba'a mata ba tun shekaran jiya,
Goggo tana tsaka da wannan tunanin ta tsinkayi abinda ya zabura ta,
"Go__g__go",ta jiyo sarkakken muryan husnah,
Mamaki ne ya cikata don tunda suke asibitin,husnah iyakaci sede ta kalli mutum sukuku ta kau da kai,babu uhm bare uhm uhm,
Goggo bata tabbatar ba koh wannan cigaba ne aka samu koh koma baya,
"Goggo ina yake,
Inaa Aliyu yake,inason na ga Aliyu,maza ki tafi ki je ki kiramin shi,ki tafi ki kiramin Aliyu,inason na ga Aliyu yanzunnan,zan mutu idan baki kawo min masoyina ba",kaman zararriya,a hargitse husnah ta ringa kawo maganganu,tana wani irin mimmikewa da fuzgan numfashi me tsoratarwa,
Kawo i yanzun idan hnkln goggo yaa yi dubu,dukka sun tashi,
A birkice ta ringa yawo a asibitin don neman likita,amma babu koh guda d'aya se nurse,sbd weekend,suma tsirari ne,
maganan duniyannan da tai babu wanda ya tanka mata,
Ganin taa dame su dayawa yasa sukace ta tafi zasu zo idan sun ida aikin dake gabansu,
Cikin halin ha'u'la'i ta dawo ta rik'e husnah tana bata baki,duk a firgice,don taasan Aliyu yaa yi nisan kiwon da bazata kirashi ba,
Kwatsam kamal ya fad'o,cikin tashin hnkl take tmbynsa ko Aliyu din yaa kama hanya ne,kamal yake bata tabbacin cewan yanzu yanzunnan suka rabu a tasha,dayai masa rakiya,
"Toh maza maza ka koma ka dawo mata dashi,kamalu ka taimaka mana ka ceci ran wannan baiwar Allahn, likita yaa ce mutuwa zatai idan zuciyanta ya buga",
Goggo taketa b'arin zantukan da suka hautsina kamal har se da ya juya ya koma,Allah ya taimakaa motan da Aliyu ze hau zuwa kano bata gama lodi ba,aka fad'a masa halin da ake ciki ya juyo ya dawo Asibiti gadan gadan,
Kamar kyaftawa da bismillah hk kake ganin yadda husnah ta rikide lkc guda kamar ba ita ba,
take ta nemi ko wani irin kunci ta rasa,tana maida numfarfashi,sa'a guda tana kafe idanuwanta kyam a kansa,da ita da shi babu wanda ya ga daman kyaftawa,yayinda yake tsaye daga bakin kofar,
"Aliyuna",
Ta kyalkyale dariya tana rufe fuskanta da tafukan hannunta kamar wata sabon kamu,
"Kazo ka zaune a nan",
"Kaaji"
"Ka karaso ka zauna a kusa dani",a cikin sanyi tai zancen ta koma ta kwanta tanai masa nuni da kan gadon da take,
jiki babu k'wari Aliyu ya ja kafa ya isa ya zauna a gefen gadon Yana ganin abin tausayi ziryan,har ta fice kamanninta sbd tsananin rama,
"kana sona koh",

A hnkl ya gyada kai,

"Koh naa yi barci ai bazaka tafi ba koh",ya kuma gyada kai a raunane yana tare wani abu daya d'igo daga idonsa,yaasan k'wayoyin da ake bata don ta manta da matsala su ne suka haukata mata k'wak'walwa hk,
"Eh....Kiyi barci bazan tafi ko ina ba"
"Allah bazaka tafi ba.....
Toh toh ka rantse in da gaske kake",ta kuma cewa tana kyakyata dariya,Aliyu ya murmusa yana kura mata ido,"toh naa rantse",hk ya ringa biyema sakarcin Husnah har ta lumshe ido,
Bayan dakikai kadan ta kuma budesu a kansa, Kamar warce takeson ta tuna da abu,hk ta ringa binsa da ido,

HUSNIYYA KO HUSNAHWhere stories live. Discover now