44~Wauta

548 25 0
                                    

🍀****🍀****🍀****
*HUSNIYYA KO HUSNAH*
****🍀****🍀****🍀
 

By  ©UmmySaudat✍
*Inspired by TRUELIFE events🗓*

®*Saudat Adam Isah*

44_

Yau takama Asabar,21st april 2018,
Ranar da yai daidai da ranar da ake wunin bikin qanin Aliyu wato Sadeeq,
har yamma liqis ko ta ina Mata ne tatul abinka da babban gida,du ko da cewan idan za ka furta arziqin gidansu na 'Hannu da Shuni',to da 'yar qaramar murya zaka fada,amman mutunci da karamcin gidannasu,tarin dattakun Mahaifinsu,uwa uba ga yanayin yadda rywrsu ke tfy cikin tsafta,tarbiyya da girmama juna ne abinda yasa suka fita daban da saura,kuma idan kai baqo ne cikin rywrsu qarya kake kace ka gane tsakanin wannan 'dan wannan 'dakinne tsakanin 'yan 'yan Hajiya da na Ammi,dabi'ansu yasa a ko da yaushe suka zamo abun kwatanci da kwaikwayo ga kowa~
Aliyu na hango cikin shigarsa ta dakakken shadda me kyau da tsada kalar mint green,wadda yasha uban aikin hannu,ganinsa nai looking all elegant as always,ga yadda naga shigar da yai ya kuma fitowa da asalin kyau da kwarjininsa ba kadan,banda tashin qamshi ba abinda jikinsa keyi kai kace barin turaren akai,
can a haraban gidansu yake a tsaye jingine da motarsa qirar Benz S63,ya kara waya a kunnensa dan ga alamu amsa qira yake,murmushinsa me cikeda qasaita ne shimfide kan fuskarsa yana sauraron abinda ake fada daka dayan bangaren,"nope....,banson jin blabbering dinki coz it wont work,kawai ki fito gani cikin compound",ya fada a taqaice,ya cije lebe ya cigaba da sauraron abinda husniyya ke fadi,tuni yaga baze iya tolerating wannan shiriritan nata ba,"nd i said baki sake kwana nan ko,stop it there nace....,nd ki sauri ki fito,don't keep me waiting.....",ya fada babu wasa yana jan tsaki kan ya katse kiran,
Ya qara kusan 10mins gun,be ga fitowan husniyya ba,kuma beyi wani mamakinta ba dan yasan kadan daga doings dinta,gashi kallo daya zakai masa ka gane how Pissed off,Bored,Miserable nd LoveSick he is,sai faman rarraba fararen idanun nan yake ko atleast ze ga wani qwaqqwaran namiji amman ina duk sunyi nisan kiwo,banda yadda yaga mata nata kaiwa suna komowa coz daman ranar tasuce,kamar a kan qaya hk yake ji dan sam he is not dat comfortable with strangers musamman Mata,
wani bahagon tsaki yaja ya cije lebe yana tunanin yadda har ze iya gigin shiga cikin wannan hayaniyan na matan,gashi sam bai tunanin ze kuma barin husniyya qara wasu kwanakin dan tun shekaran jiyan daya kawota be kuma shigowa gidan ba bare ya sata idonsa,a yanxun shi kadai yasan yadda yakejin wani azababben so da kewan matarsa,kuma ga yadda ya damu kansa da tunanin ko tana kulammasa da kanta da 'dan dake cikinta dan sarai yasanta da sakaci fannin cin abinci,du ko da cewan a ko da yaushe idan sukai waya yakan jaddada mata,but he cant help it,
yana tsaka da wannan tunanin ya ga giftawan Saleem,almajirin gidansu ta gabansa,qiransa yai,cikin azama Saleem ya qaraso yana gaidashi,nan ya tambayesa ko Alhajinsu ya dawo,Saleem yace be dawo ba tukun,ya qara da fadin suma su Hajiya 'dazun suka fita gaisuwan surukai har yanxun basu dawo ba,
nan Aliyu ya sallami Saleem,a qagauce yai ta qiran lambar husniyya yana ringing amman babu response,cikeda takaici ya ringa jinjina kai dan by now tuni husniyya ta gama provoking dinsa to d extreme,
dai dai lkcn ya hangi Fadeelah qanwarsa da Rahama 'yar wansu Ahmad sun rako wata mata waje,looking all cute cikin ankonsu na wata baby pink lace me dinkin gown ga komai na jikinsu to match,a yanxun basufi 13yrs of age ba,amman zo kaga yadda suke takun qasaita irinna isassun 'yammatannan masu ji da class,
suna ganin Aliyu yalwataccen murmushi ya bayyana fuskokinsu,a cikeda murna suka nufesa da dan sauri saurinsu,du da yadda Aliyu ke burning a can qasan zuciyarsa,hk kurum ya tsinci kansa da sakar musu wide smile,ko da yake it comes genuinely natural sbd yadda duk wani 'dan uwansa ke shiga ransa,bugu da qari dan yasan they might help d situation,
suka iso gun da yake suna gaidashi cikeda sabo da girmamawa,hk ya amsa musu cikin fara'a yana kallon cute look dinsu,"dax ma cute ladies,buh da irin wannan kwalliyan hk,kar fa kusa ai misguiding dinku as d Brides mana",ya fada in a silly way yana qwalo ido,dan turo baki sukai dan sunsan tsokanarsu yake,"daman kai muke ta nema tun daxun",a shagwabe suka fada in chorus,
dan daga giransa yai looking funny ya nuna kansa yana fadin,"as in me!,ok..ok...,buh Allah yasa ba wani laifi nai ma wa'annan damsels din unknowingly ba",ganin look din fuskarsa yasa su qyalqyalewa da dariya,Rahama tace,"ma uncle Aliyu is a control freak,mu fa Mall mukeson zaka kaimu",saurin amshe zancen fadeelah tai,"Clutch nakeson zaka siyamin da jewelleries","ni kuma pair of shoes ne kawai",Rahama ta fada cikin saurin baki dukkaninsu na kallon Aliyu cikin doki da niyyan jiran abinda zece,kallon head to toe yai ma beautiful ladies dinnasa yana tabe baki,"just look at dem,wai a dole su 'yammata",cikin ransa ya fada a fili da marairaita yace,"haba Damsels,why me?,
"ai daman tun daxun muke ta jiran muga wani tsakanin Kai,ko ya Ahmad,ko Ya Mukhtar ko Ya Sadeeq,kuma yanxun kai muka gani ai" inji Fadeelah,
Aliyu ganin da yai tsayawa biye ma surutansu ba solution bane yasashi datse zancen in brief yana tabbatar musu kan by tomorrow tunda bashida hectic Schedule,ze zo ya kaisu duk inda sukeso,even if they want to paint d town red ma,har qarshe ya umarcesu kan su shiga su qira masa husniyya,batareda sun gamsu da alqawarin da yai musun ba,hk suka juya dan cika umarninsa,banda kumbure kumbure ba abinda suke,
in less than 3mins suka dawo suka ce masa tace tana zuwa,Rahama ta qara da fadin,"amman Uncle Aliyu ni de a yadda naga ta amsa kamar ba son zuwan take ba",
nan suka barsa cikin tsananin takaici da jin haushin husniyya,ya fita gidan ransa dagule,dan har an soma qiraye qirayen sallahr magrib,
Misalin qarfe 7:00pm,Aliyu ya shigo gidan,dis time around direct ya nufi ciki du da yadda yake jin haushin kanshin da ya gagara fita harkan Husniyya,
de da cewan da wutan inverter suke amfani 24/7 hasken bulbs qewaye suke a ko ta ina,
har ya shiga general Sitroom ko ina ya gifta da kallo ake binsa,wasu sai idanun,yayinda wasu ke masa magana idan ya gadama ya maida musu martani,idan ko suka hada ido da mutum sai dai ya hade rai,idan babbane ya rusuna yana miqa gaisuwa,sai regretting yake da ya sani ya tmbyi su Fadeelah ko a wani bangaren husniyya take,
hk ya ringa yi har ya shigo sashin Ammi dan anan yake kyautata zaton zeganta,buh to his failure yaga nan dimma maqil da mata anata diban hira,yayinda wasu sukai dirshan suna kaiwa bakkunansu abinci,
furzar da iskan bakinsa yai,cikin sanyin jiki ya duqa yana gaida matan gun,"hala su Hajiyan kake nema",wata dattijuwan mata ta wullo masa tmbya,Aliyu daya rasa abin fadi banda nadamar shigowansa ba abinda yake,matar ta kuma maimaita tmbyr amman kamar malam yaci shirwa kansa a duqe yana shafa kansa bece qala ba,dan tuni yama rasa amsar da ze basu,
"to ko de Asma'u n kake nema ALI?",Yayar Ammi dake kasa Nakiya da Alkaki kan tray ta kuma jefo nata tmbyr,sai a sannan Aliyu ya dago ya gyada kai a kunyace,ai hk ko wacce macen dake gun duk aka kwashe da dariya,sosai dariyan da suke ya sosa ma Aliyu rai,a hk ya miqe rai bace da niyyar fita,"rabu dasu kaji Ali,tafi sashin Hajiyarku tana can",inji qanwar Alhajinsu tana murmushi me sauti...

sunnysmiles,
Ummy_Saudah

HUSNIYYA KO HUSNAHWhere stories live. Discover now