💞👱🏻♀HUSNIYYA*
KO
*HUSNAH👩💞By ©UmmySaudat✍
*Inspired by TRUELIFE events🗓*
wattpad_ummysaudatt15_
ta dauki lokaci tana kallon wuqar dake hannunta so blankly cikin ranta sai saqa take tana warwarewa,"wuqarnan shi zai zame miki katangar qarfe tsakaninki da quncinnan,why dont u end this once and for all,dama zamanki cikin duniyar batada amfani,just give up,it's as simple as ki sokashi qahon zuciyarki",maganganu taji zuciyarta na ta saqa mata ba kai ba gindi,
da qarfi ta rumtse idanunta ta bude,hannunta dafe kan qirjinta tana ambatan,
A'uzubillahi...,
Innalillahi...,
Allahumma ajirniy...,
Wallahu galibin...,
duk addu'ar data zo mata baki take ta ambata tana sauke numfashi a hankali,tuni hawaye suka wanke mata fuskar,kamar mutum haka tai ta watsama wuqar dake hannunta harara kan daga bisani ta wullar gefe,hade kanta tai da gwiwa tana wani irin kuka me cike da rauni,
qaurin dataji ne ya sata saurin tashi ta kashe gas stove hadi da bude tukunyar dake kai tana sauke ajiyar zuciya,"gwanda daka qone ai,dan dama can ba cinka ake ba" ta fada a sanyaye tana goge hawayen dake gangaro mata,"idan kika ci sa'a sai kiga yau yaaci",wata zuciyar ta raya mata,wani murmushi taji ta saki wanda karan kanta bata san dalilinsu ba tai dakinta da gudu tana raba idanunta,wayarta data hango kan bed tai saurin dauka hannunta har rawa yake tai dialing lambar yusif tana karawa a kunnenta,ta dauki lokaci tana abu daya,ba'a daga wayar ba,
a harzuqe ta hada wayar da bango tana sakin wani irin matsanancin kuka,zuciyarta takeji kamar zai fashe,
cikin hanzari cikeda wahala ta tashi tai bayi tana kwarara amai,
ta dauki lokaci tana sauke numfashin wahala yayinda take kallon kanta ta mirror'n dake bayin,
kamar me nazari ta tashi tai kitchen tana wara ido,
a hankali ta sauke idanunta kan wuqar dake can gefe,
hannunta na rawa ta dauki wuqar tana kallo cikin matsanancin fushi,
yunqurin caka ma kanta wuqar tai tayi continiously amma kamar hanata ake haka taji ta kasa,
take ta saki qara ta sulale qasa sumammiya dan yadda ta yanka wrist din hannunta da wuqar,sai jini keta kwarara hannunta,
Yusif dake cikin office dinsa yana latsa laptop,kallo daya zakai masa ka gane yana cikin tension,da qarfi ya rumtse idanunsa ya bude yana resting kansa kan lounge din da yake zaune,
ajiyar zuciya ya sauke hadi da miqewa kamar wanda ake kira ya dauki car keys dinsa ya nufi hanyar gida dan yadda yaji zuciyarsa na kitstsima masa they is a bad omen,dukda dazun be lura da kiran husnah ta waya ba,coz duk sanda yake gun aiki wayarsa is always in Silent Mode saboda distraction,
kawai a lokacin yaji hankalinsa ya koma kanta,
ba'a dauki wani lokaci ba ya isa unguwar nasara GRA,a babban sitroom dinsu ya tadda hajja zaune tana cin lunch,kamar kullum cikeda ladabi ya rusuna yana gaidata kan ya hau sama part dinsa zuciyarsa na harbawa,
jiki a sanyaye ya wuce parlor da sleeping room din husnah be ga alamun mutum ba,cikeda damuwa ya bude bayinta ya leqa shima be ga komai ba banda amai da ya gani kwance cikin bath tube,cikin tashin hankali da rudewa yake fadin,"am here for u,baby ki fito pls,na dena fushin kinji",ya fada yana kuma leqa ko ina,kamar wanda ya tuno abu yai saurin nufan kitchen,me ze gani banda husnah dake kwance qasa cikin jini tayi shame2 ba alamun numfashi tattare da ita,
cikin tashin hankali me yawan gaske ya dauketa cak yana ambaton,"Innalillahi... ya fice da ita sai asibiti duk da yadda yaji Hajja na kiransa ko tankata beyiba dan ko kadan baya cikin hayyacinsa,
a asibitin take aka wuce da ita emergency ward inda likitoci sukai rufdugu kanta,da taimakon Allah aka tsaida mata da bleeding din da take tareda gwajegwaje,jinin da aka qara mata ko,ze kai leda biyar ga drip din da akai ta sa mata,ko data farka ba'a jima ba ta koma barci,
babban likitan gidansu ne ya tabbatarma yusif cewan ya kwantar da hankalinsa, yana kuma assuring dinsa she will be fine,a barta tai isasshen barci inyaso idan ta farka taci abincin,sai ta sha magani tareda allurai,
yusif dake zaune kusa da ita idanunsa taf qwalla ba abunda yake banda girgiza kai,sai da likitan ya gama inspecting dinta,yace anjima yusif yazo office dinsa yana son ganinsa, kan ya fice yanai ma yusif Allah ya sauwaqe,yusif da sai ince ba baka sai kunne,yanzumma kai ya gyada ma likita a sanyaye kamar qadangare yana maida dubansa ga husnah,
be tashi gun ba sai da aka kira sallahr asir,shima ba'a dauki lokaci ba ya dawo riqe da paper bags din dake cike da fruits da takeaways,
yana qoqarin ijje bag din daya shigo dasu yajiyo kukan husnah,
rungumeta yai saurin yi ya qanqame kamar wanda za'a qwace ma ita yana rarrashinta a hankali,sai a hankali yaji tayi shiru,lamo tai a qirjinsa tana sauke ajiyar zuciya kafin daga bisani bacci barawo yai awon gaba da ita,
sun jima a hakan kafin yusif ya kwantar da ita kan gado yana kallon fuskar sleeping beauty tareda manna mata peck a cheeks,ya tashi ya nufi office din likitansa dan amsa kira...
®*Saudat Adam IsahSUNNY SMILES
UMMYSAUDAT
YOU ARE READING
HUSNIYYA KO HUSNAH
Romanceam i really in d shoes to say something, as in right now, no pls spare me, am damn happy plus scared at d same time, buh never mind,lemme try my best with dis masterpiece, to fah,ga wata sabuwa wai inji 'yan caca, this is a truelifestory #HUSNIYYAKO...