29~Jiya i yau

577 24 0
                                    

🍀****🍀****🍀****
*HUSNIYYA KO HUSNAH*
****🍀****🍀****🍀
 

By  ©UmmySaudat✍
*Inspired by TRUELIFE events🗓*

®*Saudat Adam Isah*

wattpad_ummysaudatt

29_

Qawancen dake tsakanin husniyya da husnah,shima ba laifi suna kwatantashi iya gwargwadon ikonsu,dan Alhamdulillah yanxun husnah ta soma sauke dakon son Aliyu,coz ragowar da takeji a yanxun kadanne,
kaf hnklnta ta tattara kan haneef da lamuransa,shima bangaran Yusif ba laifi har yaji wannan kalmar me tsada,wadda yake longing ji daga bakin Husnah,wato love word,dan tuni ya soma jin i love u's ba iyaka,
Husnah tuni tai karatunta ta qareshi,degree fannin Mass Media,har ta soma aiki a wani NewsBroadcasting  Company,
babbar damuwa da matsalarta a yanxun baya wuce Hajja,dan qiri qiri ta dawo kwatanta mata qiyayya,linkin ba linkin ma kuwa,
dan har Haneef bata barshi ba,coz da'ace irin wasu 'ya'yanne da tuni Hajja ta rabashi da uwarsa,a kullum hudubar tsiya take zaunar da haneef ta shiga karanto masa su daki daki duk dan ya qyamaci uwarsa,tir dan idan da mutum zeji sai ya rantse ya walle cewar haneef ya haura adulthood,du da cewar dududu shekarun 'dan basufi shidda ba,
amman aka ci sa'a,lamuran Hajja suka ci tura,sosai haqanta bai taba cimma ruwa,coz bond din dake tsakanin duk wata Uwa da Danta is just something extraordinary unique,its an unbreakable one,
shaquwar dake tsakanin Haneef da Husnah sosai ya zama abar jinjinawa da kwantanci ga kowa,
bangaren Sultan wato qanin Yusif ko,yanxun ya dena takurama husnah,atleast not like before,kuma ba dan ya haqura ba,no,kawai jiran ranar da tarkonsa ze kama kurciya yake,dan confirm cikin ransa akwai alwashin da ya daukarma kansa kan husnah,inde yana raya itama na raye,to,ko ba jima ko ba dade sai ya dandani zumar ta,sai ya sauke sha'awarta da yake dawainiya dashi tsawon shekaru thats a promise,its just a matter of Luck by Chance,and time is d main factor,
Tofaa,
~~~
Ranar wata Talata,
13th march 2018,
husnah na hango kan dining tana jera breakfast din da tai,ga wani canzawa danaga tayi ta kuma zama babbar mace abunta,
sanye da abayarta grey colour,sai faman blushing naga tanayi dan kallo daya zakai mata ka gano tsantsar kwanciyar hnkln datake ciki,juyawa tai ga qofa tana murmushi dan takun dataji tsaf ta gane ko na waye,
wow,shine expression din daya hau kaina yayinda naga Haneef dan husnah,cuteness dinsa is undefinable,tsayayyen yaro,qosasshe ne gashi yaron akwai shiga rai,sanye da uniform din skull dinsa white shirt da trouser army green ba qaramin amsan chubby structure dinsa kayan sukai ba,
"GoodMorning,Mommah",naji ya fada cikeda doki ya fada jikin husnah,ta amsa masa hadi da dagosa ta ruqo hannunsa suna tafe,ta zaunar dashi kan divan din dake parlor ta tsugunna gabansa qasan divan din,tana sakar ma danta murmushinta me cikeda qauna,kan tai pecking cheek dinsa,tace,"Son,wani irin shiri Nanny tai maka haka,huh",ta qare zancen tana qoqarin gyarama haneef rigarsan da akasa gaba a baya,
haneef yace,"i told nanny to rest already,nd i wore it myself,coz in skul,Rasheed told me,wai shiyake sa kayansa yai wanka da kansa not his Nanny,nd his mommah wont stop him,kuma he is also 6 just like me",
husnah bata tankasa ba,hakanan yai ta mata surutai da gwarancinsa ba kai ba gindi,qarshe ta katseshi tana tmbynsa ko yayi sallah da Morning azkar's,babu gardama yai mata nodding kai assuringly,daga bisani ya shiga part din yusif cikeda murna,sun jima ciki husnah na jiyo wasan da Yusif ke taima Haneef cikeda soyayyar dansa,kuma sosai hakan kesata cikin annashuwa tana kuma godema Allah daya basu Haneef,
suka fito all smiles,sama wuyan Yusif naga haneef daure,sai faman wuntsul wuntsul yakeyi da qafa cikin jindadi,Yusif a shirye tsaf cikin shigar office dinsa,kallonsa nai tayi dan yadda naga ya canxa kusan totally,ya kuma tara wasu lafiyayyun qasumba,ga wani bulbul danaga ya kuma yi fiye da da,nesa ba kusa ba,qibannasa kana gani kasan na Naira ne,kuma sai a sannan naga irin kamannin uba da 'dan,is undeniable coz komai na fuskar Haneef irinna Yusif ne,buh shi haneef fari ne irin hasken uwarsa,
a cikeda sabo da shaquwa sukai breakfast,kan duk suka sauko harda husnah dan har mota take musu rakiya,coz kamar kullum a weekdays yusif yake kai haneef skull daganan ya wuce gun aikinsa,ita ko Husnah sai 10:00am on d dot take jan mota ta fita gun nata aikin itama,
take naga mood dinta ya canza,yayinda gabanta keta faman dukan uku uku,
ganin Hajja cikin babban sitroom zaune qasan rug shame shame da ita,gabanta maqil da kayan ci da sha tana breakfast,
husnah cak ta tsaya gun da take kamar wacca ruwa ya shanye,sanin kamar ta sai masifa da kudintane idan har tai gigin qarasowa gun Hajja,
shi kuma Haneef yai saurin fadawa cinyar Hajja,Yusif ya qaraso ya duqa gabanta yana gaidata cikin ladabi,
ta amsa masa can a qasan maqoshi,yayinda dubanta ke akan husnah,tana kallonta cikeda tsana,ganin irin kallon da Hajja ke mata yasa husnah soma takawa zata fice da niyyar ta jirasu Yusif waje,dan sosai take gudun duk wani abu daze dagula mata rai,dan sanin sakamakon da zata samu na tsayuwarta gun baze zo mata ta dadi ba,tana tsaka da tfy ta jiyo muryar Hajja cikin masifa,"yo ai da ba'asan asalin balbela ba qwarai zatace daga masar take,kaji yar matsiyata shegiyar yarinya,mara tarbiyya,wato a jiji da kan naki kike nufin kinfi qarfin ki gaidani ko,munafuka,mayya,to kul,dan kuruwata tafi qarfinku dangin mayu ba yadda kuka iya dani,tarkacen Allah tsine kawai",haka Hajja ta ci gaba da balbalo masifa,ta inda ta shiga batanan take fitowa ba,Yusif tuni ya dafa kai,yanajin zafin maganganun Hajja har cikin ransa,ya hau bata baki amman ina,ai sai da ta amayo duk wata maganar dake cikinta a lkcn,qarshe ta kama bakin tai shiru,
a lkcn ko dana lura da expression din Haneef sosai na gagara bashi fassara,a langwabe naga ya tsaya kamar dasasshen gunki yana kallon Hajja,ya jima a hakan kan naga ya sura da gudu,ya fita gun husnah data hada kai da bangon corridor'n waje banda shessheqanta ba abinda akeji,
Yusif ya miqe cikin dar dar ze fita Hajja tai saurin dakatar dashi da hannu tana nuna masa gun daya tashi alamar ya koma,batareda gardama ba ya dawo ya zauna jiki ba qwari,a fusace Hajja ke fadin,"kaci ubanka nace ko,dan banzan yaro kawai,wato dan cin fuska ina zaune nan zaka tafi gun yar'iskar batareda na baka ison fita ba ko,yo ai daman ba yin kanka ba,tunda an lashe maka kuruwar,shanyayye kawai,irinku barayin na uwar tsintau",tana kaiwanan ta kwankwadi ruwan dake gabanta hadi dayin gyatsa ta miqe a daddafe tsabar masifa ta zura hijabinta,"tashi mutafi ka kaini unguwa,mara tunani kawai",ba musu ya miqe yana jan qafafunsa dasukai nauyi Hajja na biye dashi,
wani kafirin tsaki taja a lkcn dasuka iso gun da husnah ke tsaye bata fasa kukan da take ba,sosai Yusif kejin radadin kukanta har qasan zuciyarsa,yanason yaje ga matarsa ko dan ya lallasheta,sanin halin Hajja yasa shi rashin tabuka komai,
fuu naga Hajja ta funciko haneef tana qoqarin banbarosa a jikin husnah,a zuciye yaron ya hau qoqarin wafce hannunsa amman ya qagara dan ruqon da Hajja tai masa bana wasa ba,haka ya cigaba da tirjewa ze koma gun uwarsa but to no avail sai faman qwala kuka yake,
a cikeda tausayi Yusif ya je ze karbi Haneef Hajja ta watsa masa wani mugun kallon daya sashi daskarewa gun da yake,cikin kuka Haneef ke fadin"i hate her,tunda kullum batason mommah,Dad i hate her,bana son ta,she always make my mommah cry",ya qare zancen yana qoqarin qwacewa,ai nan a gun sai da Hajja ta kuma shimfida wani sabon masifar kwando kwando kamar ta cinye husnah,sai faman hargowa take tana fadin taa rabata da 'Da da Jika,

SunnySmiles
UMMYSAUDAT

HUSNIYYA KO HUSNAHWhere stories live. Discover now