62~..........Adon Tafiya

111 9 0
                                    

Unedited

****🍀****🍀****🍀
HUSNIYYA KO HUSNAH*
****🍀****🍀****🍀
By  ©UmmySaudah✍
*Inspired by TRUELIFE events🗓*
®*Saudah Adam Isah*
wattpad~Ummy_Saudah


62

A yadda labarin mutuwan Aliyu ya girgiza kowa,kaama daga iyalinsa(husniyya),iyayensa,y'an uwa da abokan arziki,
Babu wani abinda suka mayar a matsayin magani idan baa tawakkali ba,
Dukkuwa da cewan har ilaa yauma,baa wai yaa warkar masu da taarin gib'in da rashinsa ya barma zukatansu ba,musamman a bangaren iyalinnasa,
Husniyya,
wadda ikon Allah ne kadai abinda yasa take cikin rayayyu har a wannan lokacin,a sabili da irin wahalallen yanayin data tsinci kanta tun zamanin da labarin mutuwansa ya isa gareta,
a condition na juna biyun da take ciki a lokacin,wanda dakyar  da kuma taimakon Allah likitoci suka iya ceton ranta dana y'ar da suka ciro mata ta hanyan CS,
A tsawon shekara biyu tunda aka haifi Ruk'ayyatu(Imaan),baaabarta tai bankwana da dabi'unta na daa,dabi'un da aka santa dasu na walwala da faran faran,
Babu da mahaluk'in da husniyya take fara'a idan baa da imaan ba,wanda shima akan dad'e ba'a gani ba,
A kullu yaumin da kukan zuci dana zahirin rashin mijinta rabin ranta take kwana take tashi,
Tunda har ta rasa Aliyu matsayin miji ita bata k'i ace duka mazajen duniyan nan naa barzahu ba,bassu da wani amfani,
Bayan Aliyu ita bata hangar ma kanta wani d'a namijin daze iya maye mata gurbinsa ba,
Shys koh da suka so had'a aure tsakaninta da wan su Aliyu,aka ga daga Ahmad d'in har ita husniyya ba su so,maganan be tafi ko ina ba ya rushe,
A shekarun bata samu wani bazawarin ba,bayan isma'il,
isma'il maneminta ne tun saurayi da budurwa,Aliyu ya kasa shi,shine ya dawo yanzu,
duk da yadda husniyya taso ta yakice shi,amma shegen naacin sa be sa tai nasara ba,ganin isma'il yasa a gida suka kunna mata wuta,Da lallamin da fad'an da komai suka cii ta da yak'i aka daura mata aure da isma'il,an saka ranan tariya an d'age yaafi sau goma,
Husniyya bata shiga gidan mijinta ba se da aka mata ta k'arfi da yaji,sede kuma me!,
A washe garin ranan da Abdullahi ya kaita,
isma'il ya dawo masu da ita tareda takardar saki,neman ba'asin duniya babu yadda Abbansu husniyya be yi da shi ba ya fadi abinda ta masa,shi de kawai yace yaa hak'ura zama baze yiwu tsakaninsa da warce take k'insa ba,
Hakanan suka hakura,kawai suke bin d'iyartasu da Addu'a,tunda bataso,sunsan haramunne yi mata dole,
Husniyya kawai ta saka a rai,babu ita babu wani buri,babu ita babu aure,babu ita babu soyayya,wannan soyyayyar da take ma Aliyu se ya had'u a kan d'iyarsu imaan,takejin ita imaan taa isheta zaman duniya har ta koma ga mahaliccinta,taje su hadu da masoyinta a can.......
~
~
~
"Husnahta pls.....kada ki aikata komai,kadaki biyema sak'ar zuciyarki,u might regret it zata kaiki ta baro......",
"Ni yayar ki ce,
gatanki,i only want the best for u",
"Don Allah ki dawo,am here
"Am here for u,am here to listen",
"Liarrrrrrrr......",
"Liarrrrrrrr......",
A bangaren saudah tun b'acewan Husnah,bata tab'a samun wani cikakken sukuni har k'asan zuciyanta ba,
Babu ranan da ze zo ya faad'i,Saudah bata ga scene d'in ranan da Husnah ta bar gida ba,a kwakwalwa da zuciyanta,
Wani irin halin haa'ulaa'i ta shiga,wani irin feeling d'in guilt be barta ba,a tsawon wannan lkcn,
Taasan ta gaza,maybe da ace za a maida hannun agogo baya,she could have been more of a better sister,she could have done enough for her baby sister,maybe da bata rasa kanwarta ba,
Hk tanaji tana gani taa rasata knn!,taa rasa husnah knn a rayuwa!,
Ba tareda tabukawan komai ba,bayan addu'a,
"Saude idan kika tafi neman asma'u ko a bayan raina ne,ko kika sa aka nemota,ko kikai sanadin dazesa ta dawo koh ta hanyan wani ne,enaa rantse maki da asiran dake cikin yaseen,
ban yafe ba,
Baa duniya ta zab'a ba,toh ta tafi naa sallama wa duniyan.........",
Dukkuwa da mutuwan na Malam isah(ya rasu sanadin cutan da yake ta fama dashi na athsma),
Se ta qagara k'etare wannan iyakan daya gindaya mata,
Da hnklnta,babu wai yadda za ai tai fatali da wa'annan kalaman na mahaifinnasu,inde tanason duniyanta da lahiranta sui kyau,

Batasan a hannun da k'anwarta take ba,kuma a kullu yaumin tana tsoron yin wannan tunanin,amma se ta d'auki fata na gari.....,
Tana ji a jikinta cewan k'anwarta ba a hannun cutuwa take ba,shys ma har ilaa yau babu ranan da saudah zata ji an danna odar mota koh doorbell koh kiran waya bata zo dubawa cikin azama da tsammanin ganin koh husnah ce ba,
Sede rana tsaka tai tozali da fuskan mutumin da bazata tab'a mantawa da bak'in cikin daya saukar mata a ryw ba,mutumin da take kallon fuskansa kaman naa bak'in alade,
Yusuf,
A rana tsaka Yusuf ya zo mata,
Kaico!,inama ace husnahta ta dawo,inama ace zata dawo! daa gata ga d'anta,daaa gata ga haneef d'inta,
Da taga Haneef Babu irin cin ran da Saudah batai ba,
Har wannan ranan Saudah bata bawa Yusuf fuska ba,bata tab'a bashi kunnen saurare deda second daya ba,wai ballantana yaji a ina ze ga Husnah?,har ya samu shigan wanke kansa a wurinta,
Saudah take ganin toh ina amfanin sauraronnasa,ina amfanin dawowannasa,tunda be dawo mata da husnah ba...

HUSNIYYA KO HUSNAHWhere stories live. Discover now