Part 7

37 1 0
                                    

Chapter 7

Bayan shekara biyu.

Abubuwan da dama sun faru ciki kuwa harda tarewar Fatima gidan ta bayan dawowar Ahmmad daga course din da ya tafi, bayan tarewar Fatima taci gaba da karatun ta hankali Kwance wanda take gaba da Karewa.

In kowa na aure ya fadi dadin shi ko akasin hakan banda fatima, ita dai tasan tayi aure amma ita da mijin ta ba ruwan kowa da dan uwansa, tana iya nata kokarin taga ta fita hakkinsa sai dai shi a wurin shi bai damu ba hatta abinci in tayi baya ko kallon inda ta ajiye tun tanayi dashi har ta gaji ta daina in ta tashi sai dai tayi iya cikin ta, bata san shigarsa ba bata san fitar sa ba.

Komai na abinci zai saya kuma duk sati akwai kudaden da yake tura mata a account dinta so bata rasa komai ba a gidan sai rashin kulawar mijin ta wanda ta barshi a matsayin sirri a rayuwar ta ko hajja bata taba fada ma ba.

A lokuta da dama tana son daukar mataki akan rayuwar auren ta amma in ta tuna auren ta da Ahmad burin mahaifin tane sai ta hakuri. Idan kuma anyi magannar haihuwa zata ce lokaci ne baiyi ba. Akwai ranar da suka tafi bauchi an taru a sashen inna sai wata matar kawun ta tace mata wai ke fati hala sai yaushe zaki kawo mana jika ne shiru tayi don Ahmad na wurin amma sai Yayi kamar baiji me ake cewa ba ba shiri tace ya Ahmad yace sai na Kare karatu da suri ya dago kanshi yana kallon ta mamaki ne ya cikashi saboda bai taba irin wannan maganar da ita ba, ta kauda kanta kamar ba ita yake kallo ba kafin yace wani abu saijin yayi ance wai hakane Amadu innah ta tambaya cikin rawar murya yace ehnm inna kinsan yadda karatun yake daka fara samun matsala shikenan tunda har ta kusa karewa ai gara ta kare kinga da wane zata ji da karatu, jariri ko kuma gida abun zai mata yawa shiyasa nace haka, shi kanshi bai yadda cewa shine ke kare karyar da Fatima tayi mishi ba.

Da haka ta samu ta tsira daga masu yawan tambayar ta yaushe zata haihu.

***** ****** ******

Zuwa wannan lokacin salima ta kare karatun ta har tayi bautar kasa, Ahmad ya samu baba saleh da maganar su don yaji a ina aka kwana don gaskiya ya gaji yana son ya auri Salima son ta yana wahalar dashi. Kuma kamar anaso a hana shi auren ta kuma wannan abunda bazai yiwu bane Yayi hakurin auren Fatima har na kusan shekkara 3 Ai yanzu ya kamata ayi mishi abunda yake so.

Yau Asabar Don haka Fatima bata zuwa makanta bayan tayi share share tayi wanka ta hada abin kari ta dawo falo ta zauna tana kallon wani shiri da ake nunawa a tashar BBC Brit the Canon ball tana son Shirin kwarai saboda ita mutumce mai son harkar ruwa, hankalin ta ya koma kan TV din Don tana son taga wa zaici, kiran sunan ta da akayi da dan karfi shi ya dawo da hankalin ta Ahmad ta gani a tsaye hannun shi daya a cikin aljihun wandon shi, ina so zamu yi magana ina so zan Kara aure, dam dam taji gabanta ya fadi Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun take fadi a cikin zuciyar ta, zan auri wadda nake so yaci gaba da fadi don haka bana son wani tashin hankali don hakan zaisa baba yace bazan yi auren ba, daga ranar da aka hanani auren salima ranar zan sallameki ki koma gida.

Yana kaiwa nan ya juya ya fita, nafi minti 30 bansan inda nake ba ko me nakeyi. ni fa ba maganar auren ce matsalata ba, aah yadda yake son daura min laifi, in ta tawa ce ko mace 3 zai kawo bani da matsala Amma zama karamar bazawara ne bana so, ba komai zan kira Baffa Ali, in sha Allah komai zai zo cikin sauki fatana Allah yasa bata da matsala ita matar da yake ikirarin yana so.

Bayan min gaisa Baffa nace dama wata magana nake so muyi don Allah, uhmm ina jinki dama akan auren da ya Ahamad zaiyi, abinda nake so dake kiyi hakuri Baffa ya katse ni nasan kinyi karamah da zama da kishiya, Baffa ni ba auren ne bana so ba aah yadda baba saleh ke kokarin hanashi don Allah Baffa kayi magana dashi duk abinda ake ya Ahmad Yayi kun bashi aure na ya amince duk da baya so amma bashi da yadda zaiyi Yayi auren tun bayan auren mu kun taba jin wani sabani ya shiga? Ya rike amanar da aka bashi, me yasa yanzu bazaku cika mishi burin shi na aura mishi wadda yake so ba. Fatima ya kirani Baffa don Allah, to shi kenan zanyi magana da shi Baban naku Allah ya miki Albarka ya Kara hada kanku Ameen nace mukayi Sallama.

wata 2 bayan hakan aka sha biki nidai ban samu zuwa ba saboda exams dina na first semester da na fara kafin bukin. ba yadda baiso ya raba mana gida ba amma baba saleh yaki aminta dole ya hade mu a gida daya sai dai anyi dan gyara a gidan harda Karin dakuna Kuma ko waccen mu da kitchen dinta inda kawai muke haduwa a babban falo ni ban cika zama a ciki ba.

haka rayuwa taci gaba da tafia, duk ranar da naji gidan ya isheni wurin hajja nake yini sai dare in dawo har zuwa yanzu da nake shirye shiryen zana final exams dina.

BAZAN KARE A HAKA BAWhere stories live. Discover now