Part 27

34 1 0
                                    

Bayan ya fito wanka wani kaftan na farin yadi ya dauko dinkin irn na zamani kayan ya mishi kyau kwarai bakin dressing mirror ya tsaya ya taje kan shi ya dauko turare ya fesa kafin ya dauko hula tangaran ya saita ta daidai akan shi

Takalmin batozi ya saka ya ɗauki wayar shi da key din motar shi ya fito hakanan ya samu kanshi da jin fara'a dakin zarah ya nufa

Da sallama ya shiga falon bata falon don haka dakin ya shiga kayan guga take sawa a cikin wardrobe

Black silk Camisole ce a jikin ta kuma daga gani tana da mahaɗi sannu da dawowa, yawwa zarah aiki kike? Kanta ta gyaɗa mishi inda sabo ya saba har abun ya rage damun shi ko kuma maganar bahaushe ce da yace so hana ganin laifi

Ada shi mutum ne dake son idan yayi magana a amsa shi da magana amma ita mutum ce da a cikin magana biyar in kaci sa'a ta amsa biyu ko uku sauran kuma saidai ta gyaɗa ma kai tun yana magana har ya gaji ya kyale ta

Zan samu rakiya kuwa? Murmushi tayi zuwa ina? Gidan abokina yayi sabuwa amarya shine zamu tafi taya shi murna tunda bamu samu tafiya saurin auren ba

Okay bari in chanza tufafi sai in same ka, murmushi yayi ki canza ina nan ina jiran ki
Ya Ahmad kaje falo mana ya za'ayi in canza tufafi a gaban ka da kunya fa

Umhn bafa inda zani kiyi sauri kawai mu tafi, taga da gaske yake yi baza shi falon ba don haka ta fasa canza kayan mahaɗi rigar jikin ta kawai ta dauko da saka masha Allah da yake rigar baka ce me flower gold ta haska ta kwarai

Umhn bafa inda zani kiyi sauri kawai mu tafi, taga da gaske yake yi baza shi falon ba don haka ta fasa canza kayan mahaɗi rigar jikin ta kawai ta dauko da saka masha Allah da yake rigar baka ce me flower gold ta haska ta kwarai

Ups! Gambar ini tidak mengikuti Pedoman Konten kami. Untuk melanjutkan publikasi, hapuslah gambar ini atau unggah gambar lain.

Da yake ita ba fara bace tana da kalar matan Eritrea don haka rigar ta kara fitar da kalar fatar ta.

Ya Ahmad Inyi kwalliya? Kadan ba da yawa ba don haka eyebrows kawai tayi sai foundation da powder tasa highlighter dama ita gwanar light makeup ce bata son hayaniya da yawa

Juyowa tayi ta kalle shi yayi? Masha Allah yayi kinyi kyau muje ko! Jaka ta dauko black da takalmi shima black amma heels ta fito

Bata ganshi a falo ba don haka tayi kiran talatu ta faɗa mata sun fita su kula da gida tana rufe dakin ta taga yana fitowa ta hanyar dakin shi

Fita yayi waje ta bishi a bakin kofar babban falon ta same shi kofar ya jawo zai rufe salima bata nan ne? Kanshi ya gyaɗa mata bata sake tambayar shi ba

Saida ya buɗe mata kofar mota ta zauna ya rufe kafin ya zagaya ya shiga gefen driver ya ja suka tafi, akan hanyar su kusan sau biyu ana kiran shi aji yana ina sai dai yace ina hanya

A bakin wani sabon gida yayi parking mun samu kusan mota hudu ga alamu duk abokanan su ne, ina zuwa yace dani sai da suka gaisa da abokanan nashi kafin yazo ya buɗe mun kofa bismillah yace dani

Hannun shi na kama na fito ya maida kofar ya rufe wurin da ya je dazu can muka nufa daya daga cikin su fuskar shi looks familiar I think shine wanda suka je wurin da ya Ahmad kafin dauri auren mu

Ko shine angon oho ni dai na bishi, bayan mun gaisa cikin gidan muka nufa wasu 'yan mata muka samu zaune akan kujerun roba dake ajiye a cikin wata rumfa mai kama da bukka

A cikin falon muka yada zango masha Allah gidan amaryar yayi kyau akan kujera daya muka zauna da y Ahmad, ashe kuwa shine angon don cikin gidan ya wuce sai gashi da wata farar mace da ka ganta Kaga amarya tasha kunshi da kwalliya

Bayan an gaisa taje tasa aka kawo mana drinks da snacks daga baya ta zo ta kani muka shiga cikin gidan wani falo ta kai ni can ma wasu 'yan matan ne muka gaisa dasu na zauna a wuri daya

Duk hirar da suke saidai Inyi murmushi amma bansa musu baki ba. Ya Ahmad kuwa yana WhatsApp yana jana da hira da tambayar me kuke yi duk after some minutes sai ya taɓo ni

Da yake hirar maza bata wuce ta mata haka ta mata bata wuce ta maza don haka yawanci hirar falon akan maza ne, daya daga cikin 'yan matan ta tashi ta fara bayani harda demonstration yadda zaki kawo hankali mijin ki cikin ruwan sanyi

A cewar ta "wannan zamanin da muke ciki boka ko malam basa iya mana komai, ki zage damtse ki kula da mijin ki ki tabbatar da duk wata bukata tashi kin biya mishi haka duk abunda kika san yana so ki kasance kinyi shi kafin duk ya tambaya, shi namiji wawa ne kula yake so kamar kwai idan kika bashi 99.9% of your attention to kin gama dashi koma gefe kiga yadda komai zai wakana, irin mu masu abokanan zama kada ki taɓa bari sa'insa ta haɗaki da abokiyar zamani a gaban mijin ku duk kuwa yadda ta tsokane ki kyale ta sai ya fita in taku ta sake haɗoku ki cinye mata mutunci tas amma hayaniya a gaban miji is a No no iyakar ki ki tula mata takaici ki barta"

Kwarai na amfana a wannan zaman da muka yi saboda na tsinci abubuwa da dama kiran wayata ya katse mun jin dadi hirar ya Ahmad ne yace in fito mu tafi sallama nayi dasu na fito wasu su ma suka taso tunda shida tayi ya kamata duk su koma gida

Ina isa falon yazo ya kama hannuna yana tambaya ta hope Naji dadin zama gunsu injin basu cika ni da surutu ba, ai kuwa suka azo mishi baki daya daga cikin matan da muka fito dasu tace hala dai amarya ce

Daya daga cikin su yace wace amarya aure shekara uku, aw don aure ya shekara uku sai ta tashi daga amarya in sha Allah har tsufa mu a haka zamu tabbata I will always treat her like one

Zo muje kinji kar su bata mana lokaci a haka muka rabu suna ta barkwanci da abokanan su gwanin sha'awa

A wani babban super market yayi parkin bismillah yace da ni bayan ya buɗe mun kofa bayan mun shiga yace in dauki duk abunda na san babu a gida dama ina bukatar spices don haka gefen naje na debo dai dai

Bayan na kare yace to baki daukar wa kanki komai ba, ni bana bukatar komai kin tabbata yace dani in sha Allah sashen turaruka ya jani ya dauko mun guda uku ya biya muka fito

Baya so magrib ta kama mu a hanya shi yasa bamu ɓata lokaci a super market din ba munyi dai dai don muna shiga ana kiran sallah da sauri ya wuce masallaci ni kuma na shiga cikin gidan

A kitchen na ajiya kayan kitchen sauran kuwa naje dasu daki, alwala na dauro nayi sallah kafin na shiga kitchen nema mishi abinci lasagna nayi da ginger juice

Da a sai bayan isha'i yake dawowa gida don haka na samu damar kammala girkin, ina sallar isha'i ya dawo anan falo na ya zauna ya kunna TV bayan na kare na fito, sannu da dawowa yawwa zarah

In kawo abincin ka nan ne? Eh da ace Don jala na fita zuwa babban falo na kwaso kayan abinci na kawo mishi nayi serving din shi kafin na zauna a tare muka ci yana ta santin abincin bayan mun kare na kwashe kayan na kai kitchen

News @9 ya zauna kallo ni kuwa na shige dakin na karkashe aikin da nake dazu, bayan na kare na shinfiɗa sabon zanen gadon na kunna burner nasa turare wuta ta falon ma nazo na kunna na sa mata

Wanka na shiga don in rage zafin da nake ji Sam na manta yana falon na fito dagani sai towel wanda kadan saura ya kai gwiwa ta.

Bayan ya gama kallon news sai ya kashe TV ya shiga dakin ta juyawa kofa baya bata san da shigowar shi ba saida ya tsaya ta bayan ta tare da zagaye ta da hannun shi.....

Yours always book_addiict

BAZAN KARE A HAKA BATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang