Part 1

59 2 0
                                    

BAZAN KARE A HAKA BA

book_addiict

kyakkyawar ajiyar zuciya ta sauke tare da tashi daga kan kujerar da take zaune a lokaci daya tana mai tunanin daga ina zata fara lallai zama ba nata bane ya kamata ta fara daga wani wurin to amma ina? tambayar Kenan. hanyar kitchen ta nufa domin Neman aabinda zata sawa cikin ta tun da safiya ta waye bata ci komai ba har gashi 12;00pm tayi, ruwan lipton ta hada da zuma sai dan sauran cake din da take da a cikin fridge ta dauko taje kan dining table ta zauna

bayan ta gama kari dakin ta ta nufa tayi alwala ta dauko Al'quranin ta domin shine kawai mafita lokuta da dama in ta rasa mafita takan yi karatun domin samun natsuwar zuciya.

ada bata da niyar aiki amma gaskiya yanzu abu ne mai wuya dama sauran ta semester daya wadda zata kare nan da wata 2. ko ma me zanyi zan barshi nan da zuwa in kare school zan fi samun natsuwar zuciya da kwanciyar hankali dama lokaci baki daya wannan ita ce shawara ALHAMDULILLAH ta fada na samon matsaya da Kuma hanya mafi bullewa a gare ta. Fatima Zahra kenan sunan da kawunta kan kirata dashi.

Fatima ya kamata mu fara karatu kin san final exams din mu na karasowa waallahi na matsu da ban kare ba in huta Maryam ke fadawa Fatima, in sha Allah nesa tazo kusa kedai kawai mu dage muga yanda muka fara mu kare a haka ba wata matsala Allah ya nufa cewar Maryam suna fitowa daga hall din da suka yi lectures kai tsaye Fatima motar ta ta nufa haka Maryam ma suna sallama da juna Fatima gidan kawunta nufa dama rana irin ta yau takan shiga ta gaida su sannan ta yada zango wurin dattijuwar kirki HAJJA wadda Fatima taci sunan ta.

hajja ta ta fada tare da rungumota hajja cikin murmushi da jin dadi tace zahrau kece yanzu a cikin ranar nan haba hajja wacce rana kinsan bazai yiwu in kasa zuwa wurin ki ba in banzo hankalina bazai kwanta ba don ma kin hanani ai da duk kwana 2 sai nazo zahrau ina laifi duk juma'ah ba lifi in dai zan same ki lafia kalau

yanzu nake tambayar mijin ki yace yasan zaki shigo yana yiwuwa makaranta kika tsaya baki iso da wuri ba, shiru tayi da aka kira mijin ta oh ashe har yanzu yakan zo wurin hajja, hmmm to yama akayi yasan tana makaranta, ke ba Magana nake miki bane, naam hajja, bakiji me nace ba, naji kin san yau juma'ah Kuma bana so in fito lokacin masalaci shine na tsaya a can makaran ta har aka taso sai nazo Hajja ga wannan na siyo miki aiko kamar kinsan wanda kika kawo ya kare.

salamatu ki kawowa zarau abinci mana aah hajja sai nayi sallah to tashi kar lokci ya wuce, Allah yayi miki albarka ya baki yaran da zasu kula dake kamar yadda kike mini ameen hajja ta. alwala ta daura bakin fanfo sannan ta shiga falo domin yin sallah azahar wadda ta kamata a hanya.

BAZAN KARE A HAKA BAOnde histórias criam vida. Descubra agora