Part 26

32 2 1
                                    

Da safe da ta tashi shara ta fara ta gyara sashen nata kafin ta shiga wanka saida ta wanke toilet kafin tayi wanka duk da tana da mai aiki mutun ce mai son taga ta gyara muhallin ta don haka mostly aikin talatu gyaran babban falon su ne da harkan kitchen sai ɗan abunda ba'a rasa ba

Talatu ta shigo suka gaisa kafin ta tambaye ta me zata kawo mata Irish da kwai take so don haka shi tace soya mata, kan kujera taje ta kwanta duk wata kasala ta sauka mata bayan ta gama aiki

Yau tayi niyyar zuwa ta gaida ya Ahmad bawai yazo ya same ta ba amma bata sani ba ko suna tare da salima gashi yau Saturday don haka last option din ta kawai kirashi

Wayar ta ta dauko ta kira shi, wayar ya dauko da yaji tana kara ya duba ganin zarah  ce sai bai dauka ba yana so ya kare da salima kafin yaje dakin ta amma kamar salima bata da niyyar bude kofar ta yau, baya so zarah ta fara girki ba tare da sun fahimci juna da salima ba

Baya son gidan shi ya kasance irin gidajen nan da ake fada da miji da kuma kishiya yana so iyalin shi su fahimci juna haka salima ta fahimce shi amma bawai yadda suke yanzu ba amma ya zai fito ya faɗawa zarah haka zata ga kamar bai yaba irin hakurin da tayi dashi ba

Wani kiran ya sake shigowa wayar shi yanzun ma dai itace dole ya amsa don haka ya daga wayar, ya Ahmad tace daga dayan sashen na'am zarah kin tashi lafia, lafia lau ina kwana lafia Alhamdulillah, ya aka yi, kin jini shiru ko? Ba komai dama na kira mu gaisa ne

Zarah in ba ke ba wace mace ke gaida mijin ta ta waya kuma suna gida daya, kana ina ne? Ina dakina, can I come yes you're highly welcome

Dole nayi ta maza na bawa zuciya ta hakuri na tashi mayafi na yafa ma fito kai tsaye dakin na nufa, saida nayi knocking kafin na bude kofar da sallama

Shigo yace dani akan gado yake zaune da laptop din shi ina kwana, lafia lau zarah ya fargaba? Fargaba tame Kuma? Ta girkin da kika ce zaki karɓa yau, nifa da wasa nake yi haba! Ai in har ban gyara tsakanin ku ba bazan ɓata ba beside am not ready to shoulder the responsibility

Aah zarah gaskiya ban yarda ba ni namiji ne a gida na ba macen da zata tsara mun yadda zan sarrafa gida na don haka zaku fara raba girki (kwarai yaji dadin da tace wasa take amma idan ya nuna mata zata gane akwai wata a kasa shi yasa ya fito mata ta wannan hanyar)

Hmmnn ana wata ga wata gaskiya she was joking bata shirya ba duk da taso tayi amma yadda yayi mata jiya da dare kawai yasa ta fara shakkun anya zata iya gaskiya da wuya don haka dole ta lallashe shi

Saukowa tayi daga gadon tazo ta gurfana a gaban shi tare da kama hannayen shi y Ahmad am sorry to say amma kasan jiya nayi ma alkawarin wanzar da zaman lafiya a gidan ka don haka dan Allah ka bani hadin kai in samu cika wannan alkawarin kaji

Amma zarah za'a zauna ayi ta daukar hakkin ki ai ya kamata ace lokacin hakan ya wuce da sauri ta Mike ta rufe bakin shi da tafin hannun ta mun gama wannan maganar plzz

Toh shikenan Allah yasa ta gane, ameen tace tare da kokarin barin gaban shi amma bataci sa'ar hakan ba don jawo ta yayi ya zaunar da ita akan ƙafafun shi, kafin tayi magana ya haɗa bakin shi da nata hannun shi kuma na yawo a jikin ta

Saukar hannun shi akan kirjin ta yazo dai dai da karar wayar shi da sauri ta janye salima ce ke kiran shi don haka yana daukan wayar ta tashi daga kafar shi saboda bata so taji me zata faɗa mishi

Amma hannun ta ya riƙo yana mata alamar ta zauna amma yanzu kam taki sai kokarin kwace hannun ta take am coming yace da salima ya kashe wayar Zarah wait plzz zanje inyi breakfast see you later

Okay yace mata ba don ya so ba dole ya barta ta tafi, tana zuwa daki akan kujera ta zauna tana maida numfashi his touch is something else har dai na yau feels different because bai taɓa kai hannun shi a kirjin ta ba sai yau duk da yake tasha kamashi yana karewa kirjin nata kallo

A wurin bacci ya dauke ta bata farka ba sai kusan karfe uku da sauri ta shiga toilet ta watsa ruwa tare da alwala ta fito sallah ta fara bayan ta kare ta nemi atamfa ta saka ta fito kitchen ta shiga hot chocolate ta haɗa da toast bread ta fito

Akan table taje ta zauna tana ci tana game a wayar ta kwarai take son game ta hidden object shi yasa mostly in tana rike da waya zaka dauka wani abu take mai muhimmanci amma kwarai game ke ɗebe mata kewa

BAYAN SATI BIYU

Kusan kwana uku kenan baiga zarah ba ko akan hanya gashi abubuwa sun mishi yawa ko dakin ta bai samu ya leka ba ita kuma bata fito ba tana a ranshi amma bashi da lokaci

Kasancewar kayan su da hukumar custom ta kama kusan container goma shi yasa ya kasa zaune ya kasa tsaye a cikin kwanakin nan su biyu yana zuwa Lagos duk da baya kwana a can

Alhamdulillah yau ya dawo cikin nutsuwar shi domin sun samu sun yi clearing duka kayan don haka ya dan dauki hutu na kwana biyu don ya huta saboda yana bukatar shi

A office ma yace musu tafia zayyi nan ko ba inda za shi gida zai je ya shige abun shi ya huta, isar shi gida keda wuya coat din shi kawai ya cire yana kokarin cire cufflinks sai ga salima

Ahmad wai ina ka shiga ina ta kiran ka tun dazu amma banji kaba wallahi wata tafiya ta kama ni zuwa kd harda nayi niyyar barin  letter amma yanzu tunda ka dawo na huta

Me zaki je yi kd? Daddy zaizo shine zamu hadu dasu aunty dada muje gunshi plzz don't say no to me I can't afford rashin ganin shi zamuyi magana a waya bye sai na dawo

Imani ma ya cika shi yama rasa me zai ce mata shin wai meta maida shi marar hankali ko kuma mijin tace shi ya kasa gane kanta amma lallai dis time around zata gane wata taɓa ya gaji da hakuri da ita

Dame ya gaza ne a iya sanin shi yana iya kokarin shi ya faranta mata amma ita idan dai harka ta yawon nan ya motsa to shi kenan bazai sake gane kanta ba

Sauri yayi ya ida cire kayan ya daura towel ya wuce toilet Sam bazai bari salima ta ɓata mishi rai ba don lallai ya riga da ya dauko hutun kwana 2 idan an haɗa da weekend kwana hudu kenan don haka zai enjoying hutun da kyau

Amma dawa! Zarah ita ta faɗo mishi a rayuwa lallai a cikin kwana huɗun nan zai shayar da ita zumar aure am coming to you......

book_addiict
 

BAZAN KARE A HAKA BAWhere stories live. Discover now