Part 18

35 2 1
                                    

Kwanakin ta uku tana jinya a asibiti kafin aka sallame ta dole ya kira agun aikin su ya nemi izini akan dalilin rashin lafia, bayan sun dawo gida wanka tayi ta samu tufafi masu sassaucin nauyi ta saka falo ta fito ta same shi cup ya bata da fresh milk a ciki ta karɓa bayan ta zauna, sai da ya matsa ta shanye madarar gaba daya kafin ya bata drugs dinta.

Bayan ya dawo sallah ya same ta  kwance akan doguwar kujera tana waya yadda take magana kawai ya isah kasan da sauran rashin lafiya a tare da ita Sam ba wani karfi a tare da ita ganin shi tsaye yasa ta tashi zaune shi kuma ya matsa dai dai inda ta tashi ya zauna tare dasa hannun shi ya jawo ta jikin shi hakan ya bata damar Dora kanta akan kirjin shi hakan baisa ta daina wayar da take ba

Shigowar sakina tare da mijin ta bayan sunyi sallama ya basu izinin shigowa yayi dai dai da lokacin da ta kare wayar, ganin su yasa tayi kokarin tashi daga jikin shi bai hana ta ba duk da bai so hakan ba daki ta shiga ta sako hijab ta fito hakan da tayi ya mishi dadi kwarai

Kitchen ta wuce ta kawo wa bakin ruwa da lemu tana fitowa sakina ta tare ta Haba Adda fati da rashin lafiyar zakiji koda hidima murmushi tayi sakina wake baƙi ya barsu haka, sun jima suna hira ita dai nata murmushi ne ko kuma can ba'a rasa ba ta kan sa baki amma maganar ba mai tsawo ba sai wuraren 10pm su sakina suka tafi

Bayan sun raka su cikin gida suka shiga suka yi sai da safe dasu umma kafin suka dawo sashe su nan ma magani kawai tasha tayi nafila ta kwanta, akan gado ya same ta ya zauna bayan ya tambaye ta ya jikin nata da sauki ta amsa mishi, ya Ahmad uhmmnn yace da ita salima ta koma ne?

Sai da ya kallo ta kafin yace ta tafi Gombe zasu yi tafiya da mamarta Allah ya kiyaye tace kawai tayi shiru, shi ya kasa gane kan matan sa ita wannan gwara ita duk abunda ya faru shi ya jawa kansa ba wani ba amma salima ya kasa gane kan auren nasu shin ita ke auren shi ko kuma shi ke auren ta mace kullum cikin yawo sai kace tsuntsuwa in ma tana gidan ba wani kula shi take ba sai kuma kishin masifa

Allah ya sani ba dan kar a fara kirga mishi aure ba da ya sallame ta sai yanzu yake danasanin auren kyale kyale ada tunani shi samun kyakkyawar mace ka aura shine burgewa amma yanzu Sam ya yarda ba haka bane amma ko yanzu bawai ya daina son ta bane aah halayen ta kawai ke bashi haushi (abunda bai sani ba shine kowa ya siye rariya ai ya san zata zubar da ruwa) amma ai ba komai zata dawo ta same shi dole zata zabi daya cikin biyu ko aure ko yawo

Alhamdulillah zuwa wannan lokacin ta samu sauki kwarai har ta manta da tayi ciwo sati daya kenan, yau da kanta ta shiga kitchen ta Dora girki bayan ta kare wanka taje ta sake da yake yau juma'a kwalliya tayi mai kyau a cikin wani soft lace mai fari da gold tasa sarka, dan kunne da abun hannu na Gold kwarai tayi kyau haka nan yau take jin wani farin ciki na shigar ta kuma tana so ta farantawa mijin ta ko ba komai ya taimake ta kwarai yayin jiyar ta ita kuwa mutum ce mai son saka khairi da khairi

Sai da ta tsara komai dai dai kafin ta shiga cikin gida Talatu tasa ta kwaso warmers din da ta saka abincin da zata kai cikin gida, koda ta shiga umma na sallah don haka abincin kawai tasa a ajiye mata ta koma don kar ya dawo bata nan abunda bata sani ba ya riga da ya dawo daga irin kamshin turaren wutar da yaji a sashen nasu kawai ya faranta mishi rayuwa

Kamshin yasa shi wani tunani inama yadda gidan ta yayi kamar na amarya itama ya ganta kamar amaryar da lallai ba abunda zai hana shi mata abunda zai faranta mata rayuwa, abinda ya lura dashi a kanta shine tana da abubuwa da dama da takanyi da yake kara jan hankali sa akanta wanda bata san da hakan ba

Yayi nisa a tunani har tayi sallama ta shigo bai sani ba, sallama ta sake yi a lokacin da ta lura da yana falon wannan karon ma bai ji ba ko me ke damun shi oho! Ya Ahmad lafia wannan karon inuwar ta ya lura da a lokacin da ta rage tsawo a gaban shi, masha Allah ya fada lokacin da yayi ido biyu da ita ɗan suman wucin gadi yayi yayin kallon ta saida ta sake magana kafin ya dawo daga duniyar da ya tafi

Kamata yayi ya tashe ta saida mayafin ta ya dan zame, da sauri tasa hannu ta kama amma ina ya riga ta, ida zare mayafin yayi ya Ahmad mayafi na, yana rike da mayafin yana kallon ta ita kuma ta sauke kanta kasa yace Zarah wake kwalliya kuma ya kawo mayafi ya rufe, koba mijin ki kika yi wa ba? Gyaɗa kanta tayi duk kunya ta rufe ta yawwa kinga sai a bari in gani in yaba ko.

Hannun ta ya kama ya jujjuya ta yana kare mata kallo ita kuma ji take ina ƙasa zata tsage ta nutse ciki in ta san haka zaiyi behaving da baza tayi irin wannan shigar ba hannun ta yaja suka shiga daki bakin dressing mirror yakaita ya juyata tana kallon mirror din shi kuma ya tsaya a bayan ta, zarah kinga irin kyawun da kikayi kuwa masha Allah kasa dago kanta tayi ta kalle shi cikin mirror din, Yanayin yadda ya tsaya a bayan ta yasa hannun shi cikin nata kawai yasa tana jin wasu abubuwa na yawo a cikin jikin ta hakan ya sake mata kasala

Ya Ahmad muje kaci abinci badan yasa kanshi a wuyan ta ba a lokacin da tayi maganar da ba zai ji abunda take faɗa ba, kaji Y Ahmad umnnmn yace da ita amma bai motsa ba Ya Ahmad ta sake kiran shi shiru taji hakan yasa tayi kokarin juyawa amma sai ya sake haɗata da jikin sa

Sai da suka dauki kusan 10mnt a hakan kafin ya samu yayi controlling kanshi ya san hakan bai dace ba lallai bazai iya bari zuciyar shi tafi karfin shi ba dole duk abunda zai faru a tsakanin su sai da amincewar ta in ba haka ba sai dai ya hakura

Sakinta yayi tare da komawa kan gadon ya zauna hannun shi yasa ya rike kanshi dake sara mishi, a hankali ta lallaɓa ta isa falo akan hannun kujeru ta zauna tana jiran fitowar shi sai da ya dauki wani lokaci kafin ya fito yanzu da murmushi a fuskar shi, Zarah zo ki bani abinci yunwa nake ji tashi tayi ta kawo mishi abincin wanda ya matsa mata saida sukaci abincin tare

Bayan sun kare cin abincin ta kwashe kayan abincin ta kai kitchen ta gyara wurin tsab kayan da suka bata ta wanke saida ta tabbatar ta natsar da komai a kitchen din ta fito har yanzu yana falo a zaune. Zarah in kin kare aikin da kike kizo ki zauna inaso zamuyi magana, dakin ta shiga ta tabbatar da kai lafia kafin ta fito falon ma haka sannan yazo ta zauna

Zarah inaso inji ra'ayin ki akan auren mu, idan zan iya tunawa tun lokacin da aka fara maganar auren mu baki taɓa cewa bakiso ba haka kuma baki taɓa cewa kina so ba wanda hakan shiya bani dama na tunani kema baki son auren kamar yadda nima bana so, amma yau ina so inji ra'ayin ki a shirye nake da in miki kome kike so koda kuwa haakan zai zama akasin abinda ni nake so so far as zan faranta rayuwar ki to zanyi miki shi

Shiru ya biyo baya bata iya amsa shi ba saboda maganar ta zo mata a bazata bata taɓa tsammanin irin wannan maganar zata iya haɗasu a yanzu ba a tunanin ta ya riga da ya gama aminta da ita a matsayin matar shi wanda ita hakan take so amma yanzu gashi yazo da wannan maganar ko me zatace mishi ita bata sani ba In dai har zuwa wannan lokacin bai aminta da ita ba to sai yaushe option daya take da shine tayi amfani da damar da ta samu yanzu

Ya Ahmad idan na faɗa ma abunda ke rayuwa ta ban sani ba ko zai faranta ma ko kuwa akasin hakan, ko menene ki faɗi ina sauraren ki. Sunkuyar da kanta tayi kasa tana murza 'yan yatsun hannun ta yanayi ta kamar mai tauna maganar da zata faɗa gudun ɓacin ran wanda zaa faɗawa, Ya Ahmad Ina so a raba......




Taku a kullum book_addiict




BAZAN KARE A HAKA BATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang