Part 15

40 4 0
                                    

Bata so komawa sashen su ba amma tunawa da gargadin shi na jiya yasa tayi sallama da umma sakina ta raka ta har kofa sannan ta dawo, a hankali ta tura kofa ta shiga da sallama yana falo zaune da cup na tea a hannun shi yadda ya kallo ta kawai ta san tayi laifi kenan amma na me sai dai yace tayi lattin shigowa wannan kuma ai ya san tana cikin gida

Gaida shi tayi a hankali ya amsa yaci gaba da abunda yake a wayar shi kai tsaye daki ta wuce kayan bacci ta dauka ta shiga toilet acan tayi wanka ta shirya sannan ta dauro alwala ta fito

Abin sallah ta saka a gefen gadon ta tada sallah shafa'i da wutri zata yi tana cikin sallar ya shigo dakin charger ya dauka ta wayar shi ya koma fita bayan ta gama sallah ita ma lipton take son sha don haka ta fito ta shiga kitchen din ruwa kadan tasa kettle din ta dauko cup ta hada yellow label tea a irin wannan lokacin shi kadai take bukata ta dauko cup din ta fito daya daga cikin one sitter din falon ta zauna

A tunanin ta in ya ga ta zauna ya tashi ya koma daki ya bata wurin ta kwanta amma bashi da niyar tashi haka nan ta dauki cup din ta ta koma daki akan wata kujera dake dakin ta zauna har 12:30am bai tashi ba ta dauko cup din ta ta fito zuwa kitchen

Kwance ta ganshi akan doguwar kujera Allah sarki ya dauka ta kwanta akan gado ne ko kuma anan yayi ra'ayin kwanciya yau, idon shi ya buɗe ya kalli inda take a tsaye kallon kuma na menene  yace da ita uhmmnn ba komai bazaka shiga daki bane yau aah kije zan kwanta anan

Amma ai zaka takura anan din ba komai zan iya, in kuma kin aminta inzo mu kwanta akan gado daya toh sai in bar nan, shiru nayi ina nazari taya za ayi in haɗa gado dashi kuma bacci ya dauke ni wannan abu ne mai wuya amma kuma in ya kwanta anan zai wahala in na hana shi kamar da son kai aciki

Ba komai kazo ka kwanta nace a takaice na juya don bazan iya kuma kallon shi ba, tashi yay yace muje na riga shi shiga dakin sai da ya tsaya ya kashe wutar falon kafin ya shigo, a tsaye ya same ni ina dan murza yatsun hannu na.

Zarah bismillah ya nuna min gadon kamar wanda ya san plan dina dayan gefen na zagaya na zauna shi kuma ta inda ya kwanta jiya yau ma ta gefen ya hau gadon ya kwanta bai kara yi mata magana ba sai hannu da yasa ya kashe wutar dakin ta gefen shi

Ta jima zaune kafin daga baya ta yanke shawarar kwanciya bakin gadon wanda dogon motsi kadan zai iya sa ta fadi kasa duk yana jinta amma ya kyale ta a haka bacci ɓarawo ya sace ta. 4:30am dai dai ta tashi kamar dai jiya nafila tayi kafin a kira sallah

Tun lokacin da ta tashi yaji amma in ta lura ya tashi to ba Kuma sauran natsuwa a tare da ita, dole ya jira saida aka kira sallah sannan ya tashi toilet ya fada ya dauro alwala rakaatanil fajri yayi kafin ya fita masallaci

Bayan ta kare sallah kafin ta fara tilawa saida ta sami shi ruwan zafi a flask da kuma kayan tea ta ajiye a falo sannan ta dawo daki ta ci gaba da tilawar ta yau saida ta kai Rahman ta tsaya

Gado kawai ta hau ta kwanta bacci mai dadi ne yayi awon gaba da ita, bai tashe ta ba saida ya gama duk abunda yake ya shiga cikin gida 9:30am ta farka wanka ta shiga acikin toilet din ta shirya ta fito powder kawai ta shafa yau tasa kwalli da dan janbaki

Yauma skirt da riga tasa na atamfa lilac da dan touch of maroon so komai da ta hada da atamfar maroon ne gyalen ta janbaki ta suma dan kunne silver mai stone maroon tasa, medium wedge slippers tasa a kafar ta cikin gidan ta shiga don su gaisa

Basu hadu ba a falon baba yau, a dakin umma ta same shi suna magana da sauri ta juya amma umma ta kira ta zoki zauna, don Allah zarah kiyi hakuri da dan uwanki na san kina yi amma ki kara taci gaba da yi mana nasiha kusan 30mnt kafin tace min in tashi in kawo mishi break fast dinshi, umma akai can sashen zan karya to kinji ki kai can wurin ku

Saida na leka wurin sakina lokacin ma take tashi bacci nace mata bari in je in dawo kafin ki kintsa Talatu na kira ta kama min kayan abincin aka kai mishi can sai da na tabbatar da na haɗa mishi komai da zai bukata akan table kafin na rufe sashen na fito dama su Talatu sun koma tun dazu

Har na kusa isa cikin gida na haadu dashi fuska kawai nayi zan wuce shi hannuna ya kama yaci gaba da tafiya dole na juya na bishi ba zabi yadda yake tafiya yana jana kamar zan fadi gashi straight skirt ne jikina abun kuma kamar da gangan yake

Da yake hannun hagun shi ke rike da nawa hannun hagun tafiyar baza tazo dai dai ba, ya Ahmad please wallahi zan fadi don Allah haka nayi ta rokon shi har muka shiga sashen mu

Akan kujera ya turani sai da nayi hawayen wahala, tsaye yayi akaina yana huci Zarah ki kiyayeni na kula tunda muka zo garin nan kike wasu abubuwa daban a tunani ki kin samu freedom ko! Zaki haɗa kayan ki mu koma Allah Har kin ganni zuwa kika wani basar

Yadda yake fadan ya tsorata ni ko a gida hajja ta san bana son fada don nan take nake tsorata jikina na rawa nake bashi hakuri kayi hakuri dan Allah wallahi bazan sake ba, lura da yadda jikin ta ke rawa ya san ta tsorata wucewa yayi daki ya barta a nan bari kawai yazo ya bar garin nan kafin wannan yarinyar ta dagula mishi lissafi

Ya kusa 1hr a dakin kafin ya fito da jakar shi a hannu a inda ya barta nan yazo ya same ta yayi niyar tafiyar shi sai dai hakan bazai yiwu ba tana bashi tausayi mutum ce mai yawan hakuri fadan da yayi mata bai kamata ba da zaunar da ita yayi ya mata magana cikin kwanciyar hankali da yafi

Jakar ya ajiye gefe ya matso inda take zaune tasa kanta a kujera hannu ya dora a bayanta  kanta ta daga ta kalle shi sai ta maida akan kujera, kamata yayi ya tashe ta tsaye duk da hakan bata kalle shi ba duk wannan fushin ni kaɗai Zarah in kin yi laifi ba'a miki faɗa kai ta daga mishi murmushi yayi

To me kike so ayi miki, yanzu ma shiru tayi to idan an miki fada a hankali yayi kanta ta ɗaga mishi to kiyi min magana kinga tafiya zanyi kallon shi tayi yanzu ko baki so in tafi? Nan ma shiru tayi mishi

Ki bani abinci in ci ko kinaso in kama hanya ban karya ba girgiza mishi kai tayi alamar aah, sai lokacin ya sake hannun ta da yake rike dashi tun lokacin da ya tashe ta tsaye kayan abincin da suka zo dashi daga cikin gida su ta bude ta zuba mishi ta hada mishi tea nan ma ta bashi

Kinsan me nake so dake yanzu? Girgiza mishi kanta tayi baya son yana magana ba'a amsa mishi amma ya zaiyi na yau kawai dole ya hakura, kije ki wanke fuskar ki kiyi kwalliya yadda kikayi dazun kizo ina jiran ki, koda ta kare ta fito ya gama cin abincin murmushi yayi yace koke fa kinyi kyau yanzu bata ce mishi komai ba illa ta sadda kanta kasa

Zan samu rakiya kuwa? Yanzu kam da sauki don ya samu murmushi hannun shi ya bata sai da ta dan dauki lokaci kafin ta kama suka fita tare har bakin motar shi suka je ya saka jakar a mota sannan ya sake kama hannun ta suka shiga cikin gidan

Saida suka kai kofar dakin umma kafin ta ƙwace hannun ta murmushi kawai yayi ya kyale ta yayi sallama da umma amma baba ya fita sai dai ya kira shi, tare suka sake fitowa amma yanzu da sakina sake kama hannun ta yayi suka isa bakin mota

Jawota yayi ya hada da jikin sa zarah ki kula min da kanki kinji bana so in dawo in tarar kin rame kinji, sakina ga amanar mata ta na bari a hannun ki kar inzo inga ta canza banda yawo cikin rana da kuma zuwa kasuwa akai akai kinji ko in sha Allah yaya

Zarah baza kimun magana bako kina so in tafi raina ba dadi ko nan ma shiru tayi mishi to shi kenan nizan tafi duk abunda kike bukata zaki iya kira na a waya ya bude motar shi ya shiga ya rufe ya Ahmad yaji ta kira shi kafin ya amsa taci gaba Allah ya kaika lafia Allah ya tsare hanya

Ameen zarah nagode you made my day badan aiki ba da bazan tafi in barki ba amma in sha Allah zan dawo in the next 2 weeks kinji take good care of your self for me, tana nan tsaye har ya fita gidan kafin ta koma cikin gidan sai yanzu taji ina ma bai tafi ba ina ma ya tsaya ta fara saba wa dashi a kwana 2 kawai.



Taku a kullum book_addiict

Feel free to share with your friends ♥️♥️♥️

BAZAN KARE A HAKA BATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang