Part 14

32 3 0
                                    

Kayi hakuri amma bazan iya kwanciya akan gado daya da kai ba wallahi, ni ba mijin ki bane? Ya tambaya tare da tsare ni da ido ehh ahh ahh kai mijina ne amma.... Amma me? yayi saurin katse ni

A tsorace nace kai yaya na ne, murmushin dai yayi tare da cewa in kin tashi zaki iya neman duk inda yayi miki ki kwanta amma kar ki fita daga sashen nan.

Ni dama gun inna ka barni da yafi min da wannan na faɗa ciki ciki ashe ya jini, daga yanzu kin daina sauka gidan inna in kinzo Bauchi dama can don bani da muhalli ne shi yasa amma yanzu nan ne masaukin ki

Na gaji da saƙawa da warware wa na koma falo akan doguwar kujera na kwanta dagyar bacci ya dauke ni, sai around 4:30am na farka kofofin dake falon na shiga budewa ta gefen hagu kitchen na rufe dayar na san daki ne dayar ta kusa da kofar shigowa na bude guess toilet ne na shiga na dauro alwala

Akan carpet din nayi nafila na zauna yin azkar kafin a kira sallah dama haka nake yi ko a gida ina nan zaune har aka kira sallah na tashi zan tada sallah sai gashi ya fito kallon gefena kawai yayi ya wuce

Koda ya dawo ina tilawa ta suratul Fathi, a falon ya zauna saida na kare karatu nayi addu'a na shafa, ina kwana ya Ahmad lafia ƙalau kin tashi lafia Alhamdulillah nace dashi

Ruwan zafi nake so zansha lipton don Allah, agogo na fara diba wa 7am dakin na shiga na dauko mug din da yayi amfani da dare da flask na fito hanyar fita nayi ya kirani

Yanzu ke in banda abinki wa ke kwana dakin miji kuma ta fita da safe ba tare da tayi wanka ba kuma cikin gidan surukai zaki, subhanallah wace irin magana ce kuma haka ai wannan maganar tayi min nauyi nama rasa me zan ce mishi hakanan nayi tsaye da kayan a hannuna na sadda kai kasa

Zo ki wuce ga kitchen nan akwai kayan aiki a ciki ba sai kinje cikin gida ba sum sum na wuce kamar wata maƙaryacciya ruwan nasa a kettle kafin na wanke cup din, ina tsaye a kitchen din saida ruwan ya tafasa sannan na juye na canza cup na kawo mishi

Har yanzu yana falo a zaune ya kunna TV tashar aljazeerah yake kallo na ajiye mishi naje na dauko sauran kayan tea din jiya na kawo mishi ruwan zafin na zuba a cup masa lipton na fidda zuma da sugar na ajiye mishi

Bacci nake ji kwarai amma ba hali yazo kan kujerar da na kwanta ya zauna, ya lura ina jin bacci yace tashi kije daki ki kwanta da yake ina bukatar bacci mai lafia ba gardama na tashi zuwa dakin kan gadon na hau na kwanta

Ban farka ba sai 11am lokacin har yayi wanka ya shirya da hula a hannun shi, na tashi zaune ina dan murza idanu na ya jiyo ya kalleni da murmushi a fuskar sa na lura kwanakin baya bayan nan ya cika yawan murmushi ko meye dalili oho

Ina kwana nace mishi da harshen fulatanci ashe kin iya fulatanci gyada mishi kai nayi amma ban taba jin kinyi ba, ba abokin yi ne shi yasa amma ai kinsan ni ina ji, sai jiya na sani after all ai kai ba abokin hira ta bane

Zan shiga cikin gida, don Allah sakina ta kawo min kayana zan shiga wanka okay yace tare da fita, da sauri na shiga wankan don Inyi sauri kafin ya dawo

Ina fitowa Naji ana knocking kofar falon hijab dina na maida na fito buɗe kofar nayi sakina ce da talatu suka kawo min kayana aah malama wannan sai kace mai tashi, cewa yai akawo kayan ki gaba daya jaye wa nayi daga kan hanya suka wuce

Bayan sun aje kayan Talatu ta juya ita kuma sakina ta jira sai na shirya mu fito tare, wani voil na ciro an mishi dinkin fited da kuma skirt irin mai bajewar nan daga kasa, kayan sun tsaya das ajikina

Powder kawai na shafa sai lip gloss na dauki mayafi muka fito, a falon Baba saleh muka fara tsayawa da sallama muka shiga daga baba sai ya Ahmad bayan mun gaisa da baba sai muka wuce cikin gida

Acan ma a falo muka tarar da umma anan muka zauna, sakina ki kawo musu karin su shi ma yaynku bai karya ba gaisawa kawai muka yi ya fita gun baban ku aah umma Abarshi a table kawai zan ɗiba Acan

Bayan na zuba abincin muka wuce dakin sakina abincin ma sama sama naci shi muka ci gaba da haɗa kayanta, wanda zata tafi dashi da wanda zata kyautar sai bayan da muka yi sallah sannan muka fito da niyar fita

Umma muka faɗawa muka wuce sashen mu in dauko jakata a falo sakina ta tsaya tunda ya Ahmad na zaune a falo, har na fito sai ya shiga dakin ya kira ni dole na koma zo nan yace dani na matsa kusa dashi kadan cire mayafin ki ya bani izini

Da kunya in cire mayafi in tsaya hakanan a gaban shi amma ya zanyi gashi ya wani haɗe fuska ba alamar wasa, ganin zan ɓata mishi lokaci sai kawai yasa hannu ya jawo mayafin dani da mayafin duk muka zo lokaci daya sai gab dashi mayafin ya cire

Hannu nasa na rufe fuska ta saboda yadda ya samin ido, mamakin me take rufe wa fuska yake ai in kallon ta zayyi jikin ta zai kalla ba fuskar ta ba wadda ko zanata zai iya yi inda shi mai zane ne

In ma kallon fuskar ta zayyi sai dai cute lips dinta da most of the times in tana magana suke tempting din shi wani sa'in ji yake kamar yayi kissing lips din, amma yanzu da take tsaye a gabanshi ba mayafi abunda bata taba yi na tsawon lokaci ba kamar wannan kirar jikin ta ne ya dauke hankalin shi musamman kirjinta abunda yafi sha'awa a jikin mace kenan

Boobs dinta da suka ciko a cikin rigar yake karewa kallo ya lura tana son matsatsen tufafi bai san meyasa ba, motsin da tayi ya dawo dashi daga duniyar tunani da ya tafi, ya Ahmad sakina na jira na a falo tsaki yayi ki canza wannan tufafin ko ki saka abaya amma ba zaki fita haka ba

Wai hala manta kike ke matar aure ce? Ji ya Ahmad da wata tambayar raini matar aure! sai kace ya wani damu dani wai kaida bakayi accepting dina a matsayin matarka ba kaike kishi na, aah aah kawai nace masa na juya na jawo daya daga cikin akwatinan da nazo dasu na bude na dauko abaya baka da dan kwalin ta na saka

Jakata dake aje gefen shi ita ya bude yasa min kudi a ciki ya bani duk abunda zakuyi ku kiyaye banda almubazzaranci kinji ko eh nace mishi sannan na juya na fita

Saida muka je mota sakina ke cewa daman na san da wuya ya Ahmad ya bari ki fita da wannan kayan da kuma mayafi na kyale kine don bansan ya kike fama dashi ba

Hmmn nifa yau ne kawai yace sai na canza mayafi amma ai bai damu ba May be ko don mu zo gida ne ban sani ba koda yake acan gaskiya bana sa irin waɗannan tufafin in zan fita school sai dai in zan tafi gun Hajja kuma kinga ai gida ne manta dashi son rigima ne kawai

Bayan fitar su kwanciya yayi duk wata kasala ta saukar mishi ya jima fitar da yayi niyar yi ya fasa May be in ya samu barci zai dan samu karfin jikin shi gashi gobe zai tafi ya kama ta yadan leka wasu wuraren duk da shima zai dawo nan da sati biyu wurin bikin

Bai farka ba sai bayan la'asar, wanka ya sake ya canza kaya bayan yayi sallah ya fito cikin gida yaje wurin umma Abinci ta nuna mishi baya raayin komai yanzu in dai abinci ne, umma abincin nan bazai shiga ba yanzu zan dan fita may be in na dawo ko kuma in sun dawo zarah tayi min pepper soup, toh Allah ya kiyaye

Umma kwarai taji dadin yadda ta gansu wannan karon kamar sun kara shirya kansu zata iya tuna zuwan su na farko bayan tarewar fatima Sam ba ruwan shi da ita hakan ma a wurin ta wanda sai da suka zaunar dashi ita da baba saleh akan yanayin zaman su sun mishi faɗa daga baya kuma suka haɗa da lallashi ya kuma yi musu alkawari zai gyara tun lokacin kuma basu sake zuwa Bauchi tare ba sai tafiyar ta zama kowa da tashi.

Bayan sun dawo Umma ta sanar da ita sakon shi hakanan ba don taso ba kawai don umma ce ta sanar da ita shi yasa ta dora pepper soup din Bayan ta kare umma tasa ta kai can sashen nasu kafin ta dawo sukaci nasu abincin suka ci gaba da aikin da ke gaban su.


Taku a kullum book_addiict

BAZAN KARE A HAKA BATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang