Part 17

31 1 0
                                    

Zo nan kinsan ai ba ita kaɗai ce amarya ba kema amarya ce kuma gani nazo gunki, shiru tayi tana sauraren shi tana kokarin ta fahimci me yake fadi, ita ai ba yau tayi aure ba da yake kiranta amarya ko bada ita yake magana ba....... Zo mana my beloved come to your husband

Hannun shi ya bata amma bata kama ba sai dai ta matsa zata zauna a kasa ya nuna mata gefen shi akan gado ta matsa ta zauna, saida ya dan dauki lokaci kafin yayi magana, zarah na'am ta amsa shi yanzu an kare biki sai shirin komawa gida ko, Kallon shi tayi amma ya Ahmad yau fa aka kai amarya ko zan koma ba wannan week din ba kuma ma hajja tace zamu shiga Gombe

Murmush yayi ya fahimci bata da niyar komawa dama tun daga lokacin da yaga irin kayan da ta dauko ya san abu ne mai wuya ta koma immediately after bikin dama ya tambaya ne don ya kara tabbatarwa, kwana nawa zakuyi a Gombe? Sai na tambayi hajja inji to shikenan gobe da safe sai ki tambaya muji don inji ko zan iya dawowa daukar ki ko kuma daga nan Baba zai sa a maida ki, kanta ta daga mishi alamun taji.

Hannun ta ya kama Zarah inason irin wannan lalle mai zane zane da kuke yi yana magana yana bin zanen lallen da yatsan shi zakici gaba da yi koda mun koma gida ko? Yadda yayi maganar kawai yasa ta juyo ta kalle shi hankalin sa na kan hannun ta da yake rike dashi

Ita batasan meke damunsa ba, acan baya ko hanya basa haɗawa ba ruwan shi da ita bayan yayi aure sun ɗan fara gaisawa daga baya bayan nan kuwa ya fara kula ta abubuwa na son shige mata duhu. Shin ya Ahmad ya fara son ta ne? Shin ya shirya karbar ta a matsayi matarshi? Ko kuma duk wannan kulawa don sunzo gidane, ita ta kasa gane meke faruwa

Zarahhh ya kira ta ta hanyar jan karshen sunan muryar shi tayi kasa sosai bai jira ta amsa ba yaci gaba na san ba haka muka saba dake ba tun lokacin auren mu har zuwa yanzu, kar canzawar dabi'u da kikayi noticing a tare dani yasa ki shakka, lallai duk abunda na aikata akanki ko na roki alfarma ko na tambaya koma na saka ki har a zuciya ta hakan yake banyi don wani abu ba ko kuma don wasu mutane ba I mean no harm Don haka kar kiyi dogon tunani akai shi komai da kike gani a duniyar nan yana da karshen banda sarautar ubangiji

Zo ki kwanta na san akwai gajiya a tare dake gashi 12am tayi tomorrow is another day, tashi tayi ta shiga toilet ba dan yana da abunda zatayiba sai dan tana son kebewa ita kadai a irin wannan lokacin wanda abune mai wuya, kusan 10mnts ta fito bayan ta wanke fuskar ta zagayawa tayi dayan gefen gadon ta kwanta Sam bata yarda ta sake kallon shi ba

Har yau ta kan tuna irin kalamanshi a kanta da kuma auren su wanda yasa tayi loosing hope akan auren duk da taso kwarai auren nasu yayi karko dan ta cika burin mahaifi ta

"Na san wannan auren yadda bana son shi kema haka wallahi ina da wadda nike so kuma nake mafarkin in aura"

"ina son ki sani wannan auren namu bazai taɓa haifar da wani abun azo a gani ba, nace bana so aka matsa min in aure ki''

Kadan daga cikin abubuwan da yasha faɗa mata kenan akan auren su to me yasa yanzu zai zo mata ta wata hanyar in har ya shirya karbar ta a matsayin matar shi to ya faɗa  mata mana so that ta san me take ciki kawai

Ire Iren tunannin da take tayi kenan ta kasa bacci sai dai juyi da take tayi dama ita mutum ce da abu kadan kan hanata bacci da nutsuwa, shi kuma ta gefen shi da yake yayi baccin rana yanzu baya jin bacci don haka tunda ta kwanta ya koma falo ya kunna TV don haka bai san irin wainar da take toyawa ba karshen ta ma a falo ya kwana

Lokacin da aka kira sallah bai shiga dakin ba a toilet din falon yayi alwala ya wuce masallaci, dagyar ta tashi tayi sallah amma yau ko azkar ta kasa wani irin ciwon kai da sanyi take ji jikin ta har rawa yake ta lallaɓa ta koma kan gado ta kwanta ta rufe jikin ta da blanket dake kan gadon amma duk da haka zaka iya hango yadda jikin ta ke rawa a cikin blanket din

Bayan ya dawo daga masallaci falon ya zauna amma bai samu ta aje mishi kayan tea ba duk da ta san ya kan sha lipton duk ya dawo daga masallaci, ruwan zafi ya sa a kettle kafin ya leka dakin ganin bai ganta zaune tana karatu ba kaman yadda ya lura ta kan yi bayan salla subh cikin dakin ya kara shigowa ganin ta cikin bargo abun ya bashi mamaki ai ba lokacin sanyi bane kuma bata sa AC a dakin ba

Bakin gadon yaje ya zauna sai a lokacin ya lura da rawar sanyi da take da sauri ya yaye blanket din tare da kiran sunan ta amma bata amsa shi ba hannu yasa akan wuyan ta zafin da yaji yasa ya jawo ta akan jikin shi ya dorata ya rasa me zai mata

Asibiti kawai ta faɗo mishi a rai don haka ya dauke ta kamar baby ya fita bayan ya isa mota sai da baba maigadi ya taya shi bude motar ya saka ta baba don Allah ka faɗawa umma na tafi asibiti da zarah bata da lafia tau dan baba Allah ya bata lafia da sauri ya fita gidan shi kuma yayi cikin gida

Emergency yakai ta da sauri suka karɓe ta da yake assibitin kudi ce ba bata lokaci suka bata taimako na gaggawa sai bayan ansa mata ruwa da wasu abubuwan nasu na doctors kafin hankali shi ya dan kwanta a dakin mutum daya aka kai ta don haka kujerar da ke gefen gadon ya jawo ya zauna tare da rike hannun ta

Sai can bayan kamar awa daya da yaji jikin ta yadan sauka ya rage zafin sannan ya dauki wayar sa missed calls din umma da baba ya gani an hour ago don haka ya kira umma bayan sun gaisa ta tambaye shi jikin ta da sauki ya amsa ansa mata ruwa da kuma allurar bacci 

Me suka ce ke damunta? Results din test din basu fito ba amma dai ina ga harda stress ayya baiwar Allah wallahi dole tasha hidima da jama'a Allah ya kawo sauki sai mun shigo anjima, ameen umma bayan sun kare wayar aunty sa'adah ya kira ya sanar mata suna asibiti

Bata farka ba sai around 12pm, tana bude idon ta shi ta fara gani a gefen ta murmushi ya mata tare da tambayar ta ya jikin bata amsa ba sai ta maida mishi da murmushi itama hannu yasa a wuyan ta da ɗan sauran zafi jikin ta amma da sauki kwarai yunkurawa tayi zata tashi da sauri ya kamata zan shiga toilet tace dashi sai da ya rakata toilet din kafin ya dawo ya zauna bayan ta fito ya rike mata drip din bayan ta zauna sai ya maida shi inda yake

Su umma sun shigo kina bacci tace a gaida ki nagode tace dashi a hankali, bayan Doctor ta shigo sun sake duba ta kafin aka cire drip din hannun ta tea ya haɗa ya bata ta dan sha kadan yaushe zamu koma gida? Ta tambaye shi sai an sallame ki, to kace su sallame ni mu tafi gida ba irin lallashin da bai mata ba amma taki ita a dole sai an tafi gida hadda dan guntun hawayen ta

Ba shiri haka ya roki doctor din aka bata magunguna aka sallamota da sharadin zuwa allura da dare da kuma safen gobe haka ya dauko ta suka dawo gida sai dai ya kira aunty sa'adah ya faɗa mata sun dawo gida bayan tayi wanka da kyar ya lallaɓata taci indomie kadan tasha magani sannan ta kwanta, yinin ranar bai fita ba sai dai ya tsaya jinya

Bayan la'asar ciwo ya dawo kamar bai tafi ba ruwa ya samu a bowl ya dauko ƙaramin towel yazo dashi dama ya habi ta shigo sai ya bata ya fada mata yadda doctor tace ayi in sha Allah zata samu sauki a ranar haka suka kwana jikin ba dadi yanzu hadda amai komai taci sai ya fito har ruwa ko da kyar ya hakura suka kai safe ya maida ta asibiti

Ruwa aka sake sa mata saboda yawan aman kwarai ya tausaya mata don taji jiki haka yaki bari kowa ya mishi jinyar ta shine a asibiti da ita da rana kuma ya habi ko kuma wani cikin 'yan uwa da yawa cikin' yan biki da basu watse ba sun dauka ciki ne da ita har dai in anji yanayi rashin lafiyar.

 

BAZAN KARE A HAKA BATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang