Part 19

35 3 5
                                    

@safeenahb  this part of the book is for you personally I made it for you thank you for the love you are showing to this work of mine thank you very much ♥️♥️

****

Ina jinki zarah kinyi shiru kina son a raba me? Shiru ta sake yi zarah ke nake saurare inaso inji raayin ki bana so inci gaba da kuntata rayuwar ki na san ada can banyi miki adalci ba amma a yanzu inaso in kwatanta adalci a kanki a shirye nake da in aikata abunda kike so koda hakan zai zama saɓanin tawa rayuwar

Ya Ahmad ni bani da wani ra'ayi akan wannan auren kamar yadda ka sani ba'a tambayi ra'ayina ba kafin a haɗa wannan auren wanda hakan yasa nayiwa kaina faɗa tare da karɓar shi a matsayin tawa ƙaddarar

Alhamdulillah lallai zarah kinyi kokari wanda ni na kasa yin hakan a matsayina na namiji wanda hakan ya kusa kaini ga aikin danasani, nagode da irin hakurin ki akaina wanda hakan shine yasa auren nan ya kai tsawon waɗannan shekarun

Lallai lokacin kwatar 'yancin ta yazo baza tayi kasa a gwiwa ba gwara ta faɗa mishi abunda ke rayuwar ta kawai a wuce wurin, ta san duk wannan sanyi da yayi da wannan sakewar da yake kawai don matarshi bata kusa ne abu daya da ta sani shine bazai taɓa aminta da ita amatsayin matarshi ta aure ba sai dai a matsayin kanwar sa wacce zai iya kare mutuncin ta wanda hakan yake yi tun auren su, ita kuwa yanzu aure take so tayi don lokaci ba a hannun ta yake ba

'' Auren da ke tsakanina da ita na wucin gadi ne akwai wani dan lokaci da nake jira idan kuwa bukata ta ta biya zan sallame ta kawai taje ta samu wani mijin ta aura amma ni sai salima ita kawai nake mafarkin zama da a matsayi mata ta''

Tun lokacin da ta aure shi duk wani rashin kulawa da yake bata bai dame ta ba amma ranar da ta ji shi a waya yana wannan maganar da bata san dawa yake yi ba tayi danasanin auren shi, tun wannan ranar ta fitar dashi a rayuwar ta da auren ma gaba daya kuma ta zabi lokacin da zata nemi 'yancin ta agun shi yau kuma itace ranar.

Ya Ahmad, Na'am ya amsa ta, Ina so a raba auren mu! Bai san lokacin daya tashi tsaye ba saboda this is the last thing he expect to hear from her, Zarah auren mu fa kika ce why now? Zarah please ki nemi wani abun ba wannan ba dan Allah na san ban kyauta miki ba, na san kinyi hakuri, na san kin rufa mana asiri Zarah na san duk abunda ake kinyi zarah I can't afford in rasa ki yanzu

Ya Ahmad na san baka sona kuma na san baka da ra'ayin zama dani a matsayin matar ka, me zai sa bazaka sawwaka mun ba Kaga ka huta nima na huta

Bani son in takura rayuwar ka daga wannan ranar shi yasa tun zamu zo na baro gidan ka da sunan na bar shi har abada nazo nan da aka daura mana aure a raba shi

Tana kaiwa nan ta tashi ta shiga daki, ya rasa inda zai sa kan shi, why now? Bayan zuciyar shi ta gama aminta da ita bayan duk wani tunanin shi yanzu a kanta yake lallai yaso su shirya kansu kafin salima ta dawo daga yawon zaga kasashe da suka je ita da mahaifiyar ta da sunan ganin likita

Amma kwatsam sai wannan zance da bai taɓa expecting daga gurin taba, shi a ganin shi duk yana mata kallon mai sanyi hali da kuma wani irin hakuri da bai taɓa ganin wani da shi ba

Amma sai ta canza mishi cikin mintina kalilan wato dama tana magana yama rasa wane tunani zaiyi, ya zagaye falon yafi sau a kirga amma ya rasa ta ina zai bullo mata duk wata dubara tashi ta gudu ji yake kamar an mishi wankin kwakwalwa

Shi irin mutanen nan ne dake yi wa so shigar 100% shi yasa abu kadan kan iya dagula tunanin sa ya rasa mafita, irin wannan halin shine yasa ya auro salima duk da ya hango wasu Red light a halayen ta amma ina sonta ya rufe su

Yanzu gashi zai maimaita akan Zarah ya riga da ya tsara irin zaman da zasu yi, kai hatta yaran da zasu haifa ya hango 'yan mata kyakkyawa kamar ta yanzu kawai tazo mishi da wannan zancen

Yaso ya lallaɓa ta su koma gobe don su huta sunday Monday ya tafi office yanzu ta kawo wannan zancen ta ɓata mishi plan ta ina zai bi ya lallashe ta don ta hakura da wannan zancan

Damuwar shi ta karu a yayin da ya tuna dokar Baba saleh akan auren su lallai idan ya bari wannan zancen yake kunnen shi to tashi ta kare, duk duniyar nan bashi da kamar mahaifin shi bazai iya rabuwa da ita ba koda can bare yanzu da ya fara sonta

A can dakin kuwa tana shiga zubewa tayi akan gado tana wani kuka mai radadi da bata taɓa yin irin shi ba, wai me take shirin aikatawa rayuwa ta, me zai sa tace ya sake ta bayan tasan hakan bai dace ba kuma tasan shine mai mulki zuciyar ta

Ya zata iya rayuwa babu ya Ahmad wanda zama dashi yasa sonshi ya karu a rayuwar ta, a shekarun baya a dalilin sonshi ta aminta ta rayu dashi koda kuwa mata uku zai auro amma yanzu ta rufe wannan ta roke shi rabuwar su

Hakan ya zame mata dole tana son tayi rayuwa kamar kowacce mace, tayi aure ta zauna da mijin ta lafiya irn auren da ake so ba irin nata ba, don haka ta zabi wannan hanyar kawai zabi biyu take dashi da zata iya bashi shine ko dai ya aminta da ita a natsayin matar shi ko kuma ya sallame ta

Ya gaji da za gayar falon bai samu mafita ba don haka ya yanke shawarar samun ta a daki ya jaraba bata hakuri ya gani, in kuwa ta kiya duk cikar Bauchi mutum daya ya san zai iya faɗawa wannan maganar kuma tayi kokarin lallashinta ita ya Habi

Dakin ya shiga da sallama akan gado ya hango ta don haka ya kara sa akan side drawer ya zauna, yayi lallashi duniyar nan amma ta ki ko dago kanta bare ta amsa shi inda ya kara bata haushi da yace baya son baba ya san da wannan maganar in ba haka ba yashi ta kare

Wato akwai ma dalilin da yasa yake rike da auren kenan da ba dan baban shi ba to bazai ma iya rikon auren har zuwa wannan lokacin ba, kawai ita su rabu ta hakura da sonshi don shi dama son maso wani koshin wahala ne shekara 3 aiba kwana 3 bane don haka ta hakura.

BAZAN KARE A HAKA BATahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon