Part 36

28 3 1
                                    

Cikin daki ta koma ta rasa me ke mata daɗi a duniyar nan zarya kawai take a dakin duk shawarar da ta faɗo mata a rai sai taga Sam bamai ɓullewa bace sai ta zubar, Lallai bazai yiwu Fatima ta riga ta haihuwa ba a gidan ina! Sam, Aunty dada kawai ta yanke shawarar kira

Anty dada ina cikin damuwa Please kizo gida na yanzu, faɗamin menene salima hmnn Anty bazan iya magana a waya ba kawai ki zo to shi kenan gani nan zuwa

Da sallamar ta ta shiga falon ba kowa don haka dakin salima ta wuce kai tsaye a tsaye ta same ta amma da Kaga fuskar ta kasan akwai damuwa

Salima meke faruwa? Mu shiga daki wallahi bazai yiwu ba, wai menene bazai yiwu ba hmmnn wai ciki ne da Fatima ta ya ma za'ayi hakan ya faru nasan ban shirya haihuwa ba amma kinsan al'adar mu kuma ba'a taɓa yi wa kowa ba sai ni ina!!

Ciki fa! Amma laifin wa? Naki saida na faɗa miki ko ɗa ɗaya kika aje zaki iya tsarin iyali amma Sam kika ƙi ke a dole kar ki ɓata shape dinki to yanzu wa gari ya waya

"al'adar gidan su itace basu cika auren mai mata ba saboda suna so 'ya' yan su su kasance sune manya a gidajen su idan kuma har suka yi to zasu sake jiki su haifa ma yaran da ita matar ka ta farko bata da sannan daga baya suzo suyi gyaran jikin su"

Idan har kuwa Fatima ta riga ki haihuwa a gidan nan kin shiga uku kina ganin tunda suka fara shiri kika rage fada a gurin shi amma Sam hakan bai sa kikayi hankali ba ke kawai kin maida hankali da yawon kasashe

Wallah tun wuri kiyiwa kanki faɗa shi yafi miki ko dai ki manta da tafiyar nan ki zauna ki samu ciki ko kuma ki nemi hanyar da zaki zubar da cikin nata in ya so kuyi sabon aji

Haba! Aunty dada yarinya da bana shiga sha'anin ta taya za'ayi in zubar mata da ciki beside ma ina zan samu wanda zai mata allura cikin ya zube

A nemi wata shawarar dai amma ba wannan ba ta faɗa tana girgiza kanta, in dai ta zubar da cikin ne karki damu akwai hanyoyi da dama kuma in sha Allah ba za'a gane ke kika aikata ba

Aah ahh Anty dada kinsan dai ina son Ahmad kuma bazan iya aikata wani abu da zai cutar dashi ba amma in Ina son mutuwa ta ina son cikin jikin zarah ni salima me zanyi meye mafita

Rufe bakin ta tayi da hannayen ta biyu don kar wani yaji karar kukan ta, rungume ta dada tayi tana lallashi kar ki damu salima zanyi miki maganin matsalar ki in sha Allah

Kina ganin akwai mafita? Akwai da yardar Allah yanzu ki tashi muje wurin doctor ɗin da kike gani muga in akwai yadda za'ayi da planning din da kika yi lokacin

Bari in kira shi kawai ba sai munje ba unless yace sai nazo ba matsala, to shikenan ki kira shi muji. Bayan ta kira doctor appointment ya bata Don haka Anty dada ta wuce gida ta kuma jaddada mata cewa tayi kokarin boye damuwar ta kar ta nuna mishi cewa bata murna da cikin har su samu wata mafita.

Dadi ya mishi yawa har umma saida ya kira ya faɗa mata ita ma taji daɗi ta musu addu'a Allah ya raya bayan nan ya kira Anty Habi itama sun jima suna waya

Ita kam zarah kunya ta ishe ta wannan shela haka ya Ahmad ya isa haka mana bazaka bari in cikin ya fito a ganshi ba ai haka sai ka hanani shiga jama'a

Saboda me zaki ƙi shiga jama'a gareki aka fara kuma ai da auren ki, duk da haka ni dai don Allah ka bari saura sa gani in ya fita

Murmushi yayi to Naji amma ya zamuyi gashi baki jin dadi ni kuma zanyi tafiya salima ma za tayi tafiya bazan barku ku kadai a gida ba

Za muje gidan hajja har ka dawo ko kuma Bauchi wurin umma ba, Haba! Haka zan je Bauchi ina laulayin ciki gaban umma Allah da kunya

Wai meye abun kunya a ciki, ya Ahmad don kana namiji ne shiyasa Naji yanzu bari in kira hajja in sanar mata zan kawo ku, tashi tayi zuwa kitchen taga yanayin aikin talatu  shi kuma ya kira hajja

Bayan ta dawo yake faɗa mata yadda suka yi da hajja cewa zata yi tafiya gobe ina kuma zasu ta tambaya Gombe zasu tafi ya amsa ta hmnn ta lura tunda baba Ade tazo shike nan hajja ta fara yawo bini bini sun tafi Gombe

To yanzu sai yaya kenan yana murmushi yace mata Bauchi mana tace ya zanyi ai dole inje can din, to sai ki fara shiri zuwa weekend in na kai ku na dawo ni kuma sai in wuce Tuesday night

Sai dare ya samu damar kiran umma lokacin yake fada mata shawarar da ya yanke na kawo zarah in ya dawo ta dawo tunda tafiyar kusan wata daya 28 days ne

To kai in banda abu ka wake sa mace mai sabon ciki tafiya hanya ai sai ta wahala  amma kuyi magana da likita kuji in zata iya in kuma ya hana sai a nemi wata a turo muku to shikenan umma duk yadda muka yi zakiji a hakan suka yi sallama

Lallai umma ta kawo shawara zai kira one of his friends doctor ya tambaya yaji gaskiya hankali shi zai fi kwanciya in tana Bauchi da ya barta nan tare da wani in dai ba hajja ba ko umma ji yake kamar ba wanda zai iya kula da ita da kyau

****'**

Assalam alaykum my people it's been a while hope everyone is staying safe

We are back and back for good in sha Allah

Hope you are ready coz I am 99.99% with you

Enjoy

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 03, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

BAZAN KARE A HAKA BAWhere stories live. Discover now