Part 30

59 2 2
                                    

Salima! Salima! Wai me kike yi ne? Aunty dada wallahi hankali na ya koma gida kinsan yau  Friday gobe weekend Ahmad na gida baya fita kuma bana so in bashi damar sake wa da matar shi domin hakan wata babbar barazana ce  a rayuwar aure na

Ke dan Allah manta dashi da wata matar shi enjoy yourself namiji ne fa kuma Ahmad kin riga da kin kwaceshi a hannun ta don haka kar ma kisa damuwa a rayuwar ki

Haka ne kuma don weekend daya ai sai ya hakura, kin gane kenan to yanzu ya zancen tafiya Paris zai barki kuwa? Wannan karon Daddy zansa ya mishi magana bazan ma wahal da kaina ba

Suna cikin hira ne ta kai ga message din da Becky ta aiko mata "see what I just saw" sakon kenan kafin pic din yayi loading tayi tsaki wai ita Becky bata san an wuce zamanin yawan gulma bane fita tayi WhatsApp din baki daya.

Karfe goma ta farka daga bacci da ya dauke ta yana kan kujera zaune da laptop din shi gyara kwanciyar ta tayi daidai ta gefen shi tana kallon shi, jikin shi ya bashi ana kallon shi don haka ya dago kanshi suka yi ido biyu da zarah

Tashi yayi yazo bakin gadon ita kuma ta tashi zaune dan ƙaramin kiss ya mata a gefen fuskarta kin tashi Lafia "Alhamdulillah" ya jikin "lafiya" ba lau ba kenan? Murmushi tayi tare da sadda kanta kasa

Hannun ta ya kama am sorry my Zarah na san I was a bit rough with you amma in sha Allah next time zan kiyaye da sauri ta kalle shi cikin zare ido da alamu tsoro da suka bayyana a fuskar ta, No ya Ahmad please

Ba yanzu nake nufi ba kwantar da hankali ki "not any time soon" da sauri ya kalle ta amma yanayin fuskar ta yasa kawai ya aminta Naji shi kenan da gaske kanshi ya gyaɗa mata

Yanzu tashi muje kici wani abu don na san kina jin yunwa, saukowa tayi daga kan gadon ta gyara shi kafin ta bishi a baya a falon bai bari taci abincin da kanta ba shi ya bata bayan sun kare cin abincin dakin ta ta wuce, wanka ta shiga shi kuma ya je daki ya dauko laptop din shi ya dawo falon yaci gaba da aikin shi. 

Bayan ta fito daga wankan atamfa ta dauko dinkin riga da skirt ne tasa amma bata daura dankwalin ba rufa shi kawai tayi a kanta ta dauko tsinke da comb ta fito falon

Zaunawa tayi nesa dashi kadan tana tsifa shi kuma yana aikin shi da yake tasa wa kanta ruwa sai gashin yana nannaɗewa yadda ya nannaɗe kawai sai ta fasa taje shi ribbon kawai tasa ta kama shi taje daki tasa setting spray sai yayi kamar tayi coiling gashin

Tunda salima ta tafi bai dauki waya da kanshi ya kira ta ba sai dai in ita ta kira shi kuma ko shi maganar bata tsawo shi yanzu yasa mata ido yaga iya gudun ruwan ta saboda abun ta ya wuce harkan hankali

****   ******

Sunday yau ya kamata ta shirya ta koma gida hutun ya isa haka ko don ta samu next month ya barta tafiya Paris zata yi kokarin rashin tafiya na zuwa sati uku don ta samu biyan bukata

Pictures din wayar ta take diba wa kawai kwatsam sai ga pic din da Becky ta tura mata na ranar tayi mamakin ganin Ahmad to ai wannan yana iya yuwuwa daga wurin aiki ne suka yi wani taron details din hoton ta diba sai taga daga WhatsApp ne

Don haka sai ta koma WhatsApp ta tuna Becky ta turo mata wani hoto last two days Don haka chat dinsu ta bude kamar yadda tayi tsammani haka ne Becky ce ta turo mata anan ne taga sauran pictures din

Tashin hankali wato ta tafi ta basu wuri shine suka samu damar sheƙe ayar su wallahi bazai yiwu ba to ina ma ne nan suka je Becky ce kawai zata iya faɗa mata gaskiya labarin, amma kusan kira biyu tayi wa Becky amma bata dauka ba

Ta rasa yadda zata yi a haka Anty Adda ta same ta ke lafia waya taɓa ki amma bata ko saurare ta ba kayan ta kawai taci gaba da zubawa a akwati cikin sauri, rike ta dada tayi wai lafiyar ki ƙalau kwacewa tayi daga hannun ta wayar ta ta dauko ta buɗa picture din ta gwada mata

Kinga abunda nake gudu shi yasa nace miki zan koma ranar Friday amma kika hanani yanzu ta ina kike so in fara maganin wannan matsalar wallahi yau Ahmad bazai ji dadi na ba, saurara salima shin kin manta Ahmad da Fatima 'yan uwa ne? Kika sani ko wani biki ne suka je na' yan uwa su ki fara bincika abu kafin ki dau zafi akai

Aunty dada ba wani biki akwai wata a kasa sai yayyaga wa Becky rashin mutunci ni zata ki daga wayata bata rufe baki ba sai ga kiran Becky na shigowa, Becky sai yanzu zaki dauki wayata ina kika shiga

Bani kusa me ya faru Naji ki haka, a ina kika samu pictures din da kika turo min na Ahmad "I snapped them" a ina ne? A capitol ne na gansu da dare, su biyu kawai ko tare da wasu? Aah su biyu just like a date, okay thank you for calling my attention 

Kinji ko Anty dada da na tafi ai kinsan da hakan bazai faru ba amma ko yanzu zanyi maganin su bari in isa gidan, salima kibi komai a hankali kinsan maza don Allah banda garaje Kinji ko, Naji karki damu

BAZAN KARE A HAKA BAWhere stories live. Discover now