Part 12

37 3 1
                                    

Suuuu na tafi zan fadi ba dan ya Ahmad ba Dana sha ƙasa yayi saurin taro ni ta hanyar haɗani da jikin sa, yadda na fada jikin sa ido na a rufe ban bude ba sai can wani lokaci

A hankali na bude idanuna sai a cikin nashi da sauri nayi kokarin raba jikina da nashi amma hakan bai samu ba saboda shi ke rike dani, na sake juyowa na kalle shi still ni yake kallo

Ya Ahmad thank you, sai a lokacin yaɗan rufe idon shi ya bude be careful next time yace sannan ya duka ya cire rigata inda ta makale

Bayan na kwashe kayan abincin na kai kitchen saida na dawo na gyara wurin kamar yadda na same shi, na koma kitchen na wanke kayan shi ma na gyara naja kofa na rufe na shige daki abuna

Wai me ke damuna  a 'yan kwanaki nan yarinya nan ta shiga kaina da yawa in ina zaune ni kaɗai na kan yi tunannin ta akai kai in kuma na ganta to nakan shagala da kallon ta, yau ga girkin ta na ɗanɗana yayi dadi, uwa uba Dana haɗa jiki da ita wannan bazan iya misalta ya Naji ba kuma banso ta katse min wannan lokacin ba zanso mu tabbata a hakan amma ina!

Zanso ace zata dawo nan ta zauna kan dakinta da ta shige da zata dawo nan ta zauna kusa dani in sa ta a jikina da zanfi samun kwanciyar hankali

Key din motar shi ya dauka is better ya bar gidan kafin zuciyar shi tasa ya aikata abunda bai shirya ba, zuciyar shi na azazzala mishi cewa matar shi ce ba wani abu bane koya same ta dakin ta wanda hakan baya cikin tsarinsa a yanzu

Amma ai laifin sa ne ya san halin shi to me zai sa ya bar salima tayi tafiya mai tsawo haka kusan 2wks gaskiya zai kira ta ta dawo gida hakanan Haba! Ai ta san bashi da wata matar bayan ta da zai iya zuwa a taimaka mishi

******        *****         *****

Salima kome kike yi na baki zuwa Wednesday ki shirya dawo wa Allah na gaji, Ahmad ya zanyi ka dai san tafiyar nan bani kadai nayi ta ba kuma bazan zame ni kaɗai In dawo ba shi yasa nace ma ka shirya muje kaki wai kai aiki to baga irin ta ba nan

Ni dai na kare magana ki shirya ki dawo gida idan kika kai rana I ta yau baki dawo ba to duk abunda nayi karki zarge ni ko kiga laifina na faɗa miki, me kake nufi da hakan?

I will accept Zarah as my wife Wanda nasan sarai ba zaki so hakan ba, Naji I will try my best in ban samu zuwa Wednesday ba Friday zan dawo in sha Allah

Wannan ya rage naki sai anjima, Ahmad plz don't do that to me kasan I can't share you with any other person.

Duk da ya fita amma ya kasa natsuwa dole haka ya koma gida ya shige dakin sa toilet kawai ya shiga ya sake wa kan shi shower for 3omnt kafin ya fito

Sai da aka kira magrib sannan ya fito zuwa masallaci. Bayan sallar isha'i ya dawo Fatima tazo ta tambaya me zata tanadar mishi pepper soup na kaza kawai yake so sai tea bayan ta tanadar mishi ta koma daki

Haka rayuwa taci gaba da tafiya zata yi mishi girki ta Dora a table in yazo zaici shima yafi son hakan don ya lura in bai nesanta kan shi da ita ba wata rana zai iya bata damar zamewa matar shi wanda har yanzu bai shirya hakan ba

Yau saura 3wks bikin Sakina komai tayi har dinki da ankon ma tace Sakina tasa ayi mata dama cikin satin nan take son tafiya Bauchi don ida sauran shirye shirye su haka ta matsu taga inna

Akwati biyu ta shirya da kit duk wani abu da take bukata ta tabbatar da ta dauka saboda wannan tafiyar tana da wata manufa acikin ta

Lallai in ta tafi baza ta dawo ba ta tafi kenan sai iyayensu sun gaji sun saka baki acikin maganar auren su wannan dama itace shawara da ta yanke

Bayan ta gama abincin rana tana jerawa akan table sai ga salima ta fito, malama lafia  waki ke dorawa abinci a wurin? Mai gidan na amsa ta a takaice waya baki izini

Ni ne nan na bata ko ban isa bane, yaushe kuma aka fara wannan a cikin gidan nan bani da lokacin sauraren shirme su kawai na juya na tafi abuna

Saida na daidaici ya kusa kare cin abincin tukuna na fita akan table din na same shi da ita ko kunya babu tana cin abincin, kunci na yau amma in na tafi sai ku samu mai girka muku

Matsawa kawai nayi kusa dashi ban zauna ba sai dai na rike kujerar da ke kusa dashi din wadda kuma ke kallon salima spoon din da yake cin abincin ya ajiye ya kalle ni ke baza ki ci abincin bane, girgiza kishi kai kawai nayi

Why? Ba komai, zauna kawai ya bani izini kujerar na jawo na zauna spoon din da yake cin abincin dashi ya dauko ya kai bakina kauda kai kawai nayi uhmm kici nace ya Ahmad Allah bana jin yunwa kayi hakuri

Naji amma sai kin ci wannan, fuskar salima na kalla ta cika kamar zata fashe For the sake of abinci na da taci bada izini na ba bari in dan suƙata kadan, zarah kinsan bana son gardama ko

Hannu na kai zan karbi spoon din amma sai yasa hannun shi na hagu ya rike nawa ya koma kawo dayan dai dai bakina wato nufin shi dai sai ya bani abincin a baki bani da zabi kawai na bude bakin ya bani abincin

Still bai sake hannu na ba, y Ahmad gobe nake son in tafi Bauchi ko jibi dago kan shi yayi ta kalle ni bikin har yazo kusa ne gyda mishi kai kawai nayi na san baya son yana magana ana gyada mishi kai amma hakan na riga dana saba

Wayar shi ya dauko yayi checking date din saura sati uku fa zarah amma ai akwai shirye shirye da zamu yi gaskiya yayi sauri don Allah ya Ahmad don't say no to me please

Ohh no yarinyar nan na kokarin dagula masa lissafi, daga yana yin da take mishi magana kawai ya isa, hannun ta da yake rike da ya murza tare da rufe idanun shi na dan lokaci salima ta gaji da hakuri

Hannun ta tasa ta raba hannaye su cikin hasala wanda yayi sanadin bude idon shi kallon yadda tayi tsaye akan shi tana huci kamar kububuwa yake da idanu shi da suka fara canza kalla

Zarah tafi ina zuwa umarnin da ya bani kawai, na tashi na wuce daki koba komai nima yau na rama kiji yadda ake ji kuma na san ma abin da wuya ya tsaya a nan oho ku dai kuka sani

Ci gaba da haɗa kayan nayi harda su kari ni adole zaa barni in tafi, takalmi ma Dana dauka sun fi 5 jaka daice ni ba gwanar rataya ta bace amma itama na dauka guda 3

Salima ki kiyaye ni, wallahi akan yarinyar  nan sai na saɓa miki Ahmad bazan iya dauka ba wannan ai cin fuska ne yaya zaka wani rike hannun ta kuna wani magana kasa kasa harda wani bata abinci a baki wannan ai cin amana ne

Wai in na tashi kula yarinyar nan kin isa ki hanani ne ko kuma kina iko dani ne wallahi bazai yiwu ba, irin waɗannan halayen naki shi zai sa in kula ta ada da baki damu da ita ba kinga na damu da ita ba ruwana da ita haka ba ruwan ta damu

Na fada miki hukuncin mahaifi na akaina akan wannan auren ai na dauka zaki kokarin taya ni inyiwa mahaifina biyayya, wani abu na roka mai nauyi kawai ki fita harkar ta shine ya miki wuya haka

Bazan iya hakuri cin zarafinta da kike yi a gidan nan ba ranar da zata gaji ta fara maida miki ba zaki ji dadi ba haka nima zaku maida mun gida kamar kasuwa bazan dauki wannan ba

Bayan ya dawo daga salla isha'i dakin zarah ya wuce yayi knocking sau biyu tare da tura kofar bata falo sai ya wuce dakin kai tsaye a bakin dressing mirror take tsaye batasan da shigowa shi ba

Da hijab a hannun ta kamar yanzu ta kare sallah sallama yayi, da sauri ta ware hijab din ta saka sannan da juyo ta gaida shi tare da nuna mishi kujera tace ya zauna

Idan kinje Bauchi yaushe zaki dawo, sai an kare biki an watse mun daidai ta komai sannan, murmushi yake yana kallon yadda take bayani sannu uwar biki wannan bayani

Ya Ahmad ina bukatar chanza muhalli wata daya kawai zanyi gidan nan ba dadi wallahi na fadi tare da sauke kaina kasa waini aji tausayi na, me ake miki a gidan da baya miki da din zama, ba komai

Ki shirya sai muje in kaiki Friday ya miki? Ehh yayi nagode

Nima nagode.

Taku a kullum book_addiict

BAZAN KARE A HAKA BAOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz