Part 35

41 3 2
                                    

........ Am six weeks pregnant

Jin yayi shiru bai amsa ta ba yasa ta juyo ta ga ko lafia amma ga mamakin ta bacci yake, yaushe ma baccin ya dauke shi hannun ta ta Dora akan shi ganin bai motsa ba ta juya dama itama baccin take ji

Ta riga shi tashi don haka wanka ta shiga koda ta fito shima ya tashi amma yana zaune akan gado yana waya tana tsaye bakin wardrobe kayan da zata saka take nema

Zarah zanyi tafiya next week in sha Allah kuma zan kwana 2 kafin in dawo, Allah ya kaimu lafiya ya Ahmad, Murmushi ya yi dama ai ita nata mai sauki ne sai uwar rigima amma zai san yadda zaiyi da ita, Ina zuwa zarah

Wallahi ina son zuwa a kawai nema min visa itace matsala in sha Allah I'll find a way dazan convincing din Ahmad ya barni tafiyar duk da na san da wuya, ta saurara daga dayan sashen kar ka damu unless bai aminta ba bana son kowa ya mishi magana.....

Ke dawa a waya ya katse ta uhmmnn uhmmnn... Ki min magana mana uncle Musa ne ta shirga mishi karya saboda bata son ya san da PA din daddy take Waya saboda zai iya gane cewa akwai wani abu da take shirin aikawa

Dama nazo muyi magana ne are you busy? Aah ba komai ai na kare wayar amma kamar akwai abunda ke damun ki ko zan iya sanin menene, Alhamdulillah ga dama ta samu kawai bari ta faɗa mishi

Dama akwai family trip da daddy ke planing  shine yake tambaya ta ko zaka je sai muje tare tunda da wuya ka bari in tafi ni kaɗai ba da kai ba, murmushi kawai yayi shi dai mai hali baya barin halin shi wannan yawon dai ya zame mata kamar ibada idan bata yi ba bata jin dadi

Ya gaji barin ta tafi shine kwanciyar hankali shi don ko ta zauna faɗa kawai zasu dinga yi akai kai gashi shima zaiyi tafiya, saida ya nisa kafin yayi magana zaki iya tafiya amma ni da wuya

Akwai tafiyar da zanyi daga office kuma zan dau lokaci kafin in dawo don haka bazan tsaida ku ba may be next time, wani irin dadi ne ya mamaye ta amma a fili sai ta nuna mishi rashin jin dadin ta na kin tafiyar sai da ya lallashi ta ya nuna mata bashi da zabi kuma daman maganar ce ta kawo shi gun ta

Bayan ya bar dakin salima dakin shi ya shiga ya watsa ruwa ya shirya kafin ya fito dakin zarah ya wuce kafin ya isa a falo ya same ta tana jere kayan abinci akan table don haka a wurin ya tsaya

Ya lura ba karfi a tare da ita sai dai karfin hali she ya kasa gane kan wannan rashin lafiyar tata, don haka koda suka zauna cin abinci bai tsaya ta zuba mishi ba shi yayi sauran

Abincin ma sama sama taci saboda tashin zuciya da take ji wani sabon abu da bata saba ji ba ga wata irin kasala kawai yana yin ta ya canza bayan sun gama cin abincin ma talatu tasa ta kwashe kayan akan kujera ta koma falo ta kwanta

Wani irin tashin zuciya ya zo mata da amai ai tashin da tayi da karfi kafin ma ta isa toilet ko kitchen sai dai ta duka a wurin ta fara amai da sauri yazo ya kamata saida duk ta amaye abunda taci

Talatu tazo da sauri da ruwa ta cire dankwalinta tana yayyafa mata akai da karfi hakan ya taimaka mata wurin saukar da aman a toilet din da ke falon ya kai ta ta wanke fuskar ta

Koda suka dawo talatu na gyara wurin bayan ta kare zarah tace kije daki ki dauko turare kisa a wurin kar yayi karni, am sorry.... Hannu yasa a baki alamun tayi shiru

Ƙaramin towel dinda take goge gashin ta dashi talatu ta kawo ga wannan anty kiyi hakuri a wurin mu haka mukeyi in mutum yana amai mukan zuba mishi ruwa akai saboda amai din ya soka ba komai talatu na gode

Bata sake kwantawa ba saboda tana gudun wani aman, Zarah ya kamata mu koma asibiti na kasa gane wannan rashin lafiyar, aah ba sai mun koma ba kasan ina shan magani dole sai na gama treatment kafin nan

Badon yaso ba sai don ta matsa dole ya hakura amma gaskiya baya son ganin ta haka rike hannun shi da tayi yasa ya juyo ya kalle ta am so sorry please, me ya faru? Ya Ahmad am pregnant, what!!!

Come back again banji ki dai dai ba yes abun da kaji shi nace am six weeks pregnant kanta na kasa take maganar come zarah you are pregnant? Kanta ta gyaɗa mishi you are pregnant with my baby, yes Haba daga ta yayi ya jujjuya ta kafin ya sauke ta ya kuma rungume ta

Alhamdulillah kawai ya karantowa, zarah kina da ciki kuma baby na? Eh tace dashi tare gyaɗa kanta kusan sau uku yana dago ta yana mata wannan tambayar, zarah yanzu zaki haifamin baby kenan karab sai a kunnen salima

Baby kuma? Yaji salima na tambaya juyowa yayi gunta zoki tayani murna zarah is pregnant, wata nawa? Six weeks am going to be a father wani takaici taji ya zo mata duk da bata shirya haihuwa ba amma Bata so Ya haihu da wata mace ba ita ba bare kuma ma ace za'a rigata haihuwa a gidan da sake.....

BAZAN KARE A HAKA BAWhere stories live. Discover now