Part 20

47 1 0
                                    

Barkan mu da sallah🐑

***********

Tunda ya fita ya barta tana nan inda take yau ko cikin gidan bata koma ba har dare, yanayin fuskar ta kawai ya isa ya tona asirin zuciyar ta kuma lallai umma ta ganta a haka sai ta tambayi meke faruwa

Kuma bazata iya faɗa mata meke faruwa ba saboda wannan tsakanin su ne koda bai roki alfarmar kar iyayen shi suji ba baza ta iya bari su san meke faruwa a tsakanin su ba

Lallai har a zuciyar ta bata son ravuwa da Y Ahmad amma dole ne ta bullo mishi ta wannan hanyar don haka ta jefi tsuntsu biyu da dutse daya

In har ya Ahmad yana son zaman lafia da iyayen shi to lallai dole zai accepting dinta a matsayi matar shi koda baya so in kuma yaki dole ya raba auren su

Tun tana jiran shi har tsoro ya fara kamata kusan karfe daya yanzu bai dawo ba ko lafia amma bazata iya kiran shi ba saboda hakan zai sa yaga kamar ta damu dashi

Abunda bata sani ba ya dawo amma yana falo bai leko dakin ba saboda shi yanzu bai san me zai ce mata ba, shi gaskiya yanzu da take son ravuwa dashi yanzu yake son zama da ita kuma ko ana ha maza ha mata bazai sake ta ba

Wannan bazai yiwu ba, zai jira Habiba yaji saboda dazu gidan ta yaje kuma ta mishi alkawari shawo mishi kanta

"Ahmad wai yaushe zaku san annabi ya kau a tsakanin ka da Fatima don Allah auren shekara 3 Ace kun kasa hakura ku zauna a matsayi mata da miji don Allah sai kace a gunku aka fara auren Hadi

Ka sani Fatima yarinya ce amma tana da hankali da kuma hakuri in ba haka ba da wallahi tuni anji kanku shin kai a matsayi ka na namiji bazaka hakura ba a wuce wurin?

Hmmmn lallai Zarah ta aminta dake don tunda muka yi aure ba wanda ya taba taro na da irin wannan zance sai yau kuma daga bakin ki

Fatima nada hakuri na sani amma itama taja jikin ta daga gare ni din haka kinga itama bata son zaman mu ya dore don haka karki damu

Shin kana da labarin Fatima na sonka tun kafin auren ku kuwa?

So na fa! Haba dai koda muka yi aure fa ita karama ce kwarai

Amma a hakan take sonka da bakinta ta fada min ranar da aka yi meeting na hada auren ku amma da alkawari kar in bari kowa ya sani

Hmmmn kawai yace tare da canza akaalar zancen na su, wannan shine dalilin da yasa ya same ta akan bukatar Fatima ta yau, kwarai ya habi bataji dadi ba amma tayi mishi alkawarin zata shawo mishi kanta

Bai shiga dakin ba sai da ya dawo daga masallaci zaune take tana karatu ya shiga toilet, bayan ta kare karatu bata bi ta kan shi ba ta hau gado ta kwanta

Sai wuraren 10am ta tashi daga bacci, shara ta fara kafin tayi wanka ko breakfast bata yi ba ta shiga cikin gida duk kokarin boye damuwar ta sai da umma ta gane

Fatima lafia kuwa kike? Umma lafia ta ƙalau  kaina ke dan ciwo kuma ina ga don na jima ina bacci ne da Allah ya sawwaka kawai umma ta bita ba don ta yadda ba

Amma ba kyau shiga harkar yara don ta lura ko Ahmad haka ya shigo yau amma tunda sun zabi sirranta lamarin su gwara hakan iya dai addu'a take musu Allah ya daɗa haɗa kansu

Sai kusan 3pm ta koma sashen su indomie daya ta dafa amma da kyar taci rabi da taga damuwa zata dame ta karatun Kur'ani ta kunna a cikin kira'ar minshawi tana bi a hankali

Sallamar ya habi ta katse mata karatun da take bi a sannu bata jira komai ba ta hau ta da faɗa, Fatima kin ban kunya ban dauka zaki aikata hakan ba kin manta hukuncin matar da ta nemi saki agun mijin ta?

Cikin kuka tace ya habi ya zanyi baya son zama dani a matsayin matar shi haka zan tabbata hakuri ba uwa ba riba shin hakuri da nayi baza ku diba ba

Wallahi na gaji ina so nima yau in kalli mijina inyi tutiya dashi haka nan Inyi bautar aure in samu lada da kowacce macce ke samu a matsayi matar aure, ya habi don Allah kuyi min adalci

Ya habi kinsan ina son shi bazan iya rayuwa bashi wallahi ni kaɗai na san irin zafin da zuciyata keyi, wallahi in har ciwon zuciya ya kama ni hakki na akan ku yake keda ya Ahmad

Da sauri ya habi tazo ta rungume ta tana lallashi, na sani Fatima na sani in sha Allah komai zai dai dai ta amma kiyi hakuri akan zancen raba auren nan kinji duk wanda yayi hakuri baici riba ba kadan yayi


BAZAN KARE A HAKA BADonde viven las historias. Descúbrelo ahora