Part 24

40 2 2
                                    

A falon na bar shi yana sauraren news na shiga daki wanka nayi nasa kayan bacci hijab nasa akai kafin na koma falon yana nan a inda na bar shi yana kallon news nima na zauna har aka kare news din

Ruwan zafi ya bukata zai sha lipton bayan na haɗa mishi lipton din na bashi nake tambayar shi ya Ahmad wai lipton baya hana ka bacci? aah ko kadan wani lokacin ma in ban sha ba ciwon kai nakeyi

Murmushi nayi na ce shi lipton din kwarai kuwa hmmn kowa da abin da yake so wasu goro kesa su ciwon kai in basu ci ba amma kai lipton dariya yayi ai gara lipton da goro don na shaida da ina cin goro Sam ba zaki iya zama dani ba a matsayin mijin ki

Murmushi nayi koba haka ba ya sake tambaya ta girgiza mishi kai nayi ki bani amsa da bakinki mana, ba haka bane nace zo nan yace na tashi kamar wata marar gaskiya na isa kusa da shi

Zauna ya nuna mun gefen shi matsawa nayi na zauna amma sai da na bar space a tsakanin mu, uhmnn ina jinki kika ce ba haka bane eh na amsa, kenan ko yanzu zaki iya zama dani a yadda nake bayan abunda ya faru?

Ya Ahmad abunda ya faru a tsakanin mu ya faru ne a bisa wani dalili kuma ni aguna ya wuce wallahi ban riƙeka a zuciya ta ba don haka stop feeling guilty about it kaji

Rungume ni yayi tare da fadin na gode zarah wallahi na dauka a Bauchi kince kin hakura ne kawai dan a ƙyale ki amma yanzu na yarda Allah ya sawa rayuwa ki albarka ya bani ikon kyautata miki

Kusan 11:30 amma ya Ahmad baya da niyyar komawa dakin shi gashi gobe akwai aiki idan nace yaje ya kwanta zai ga kamar ina korar shi ya zanyi?

Wata dabara ta Faɗo mun hamma na fara harda dan guntun hawaye na alamun bacci yazo kenan zarah bacci yazo ko? Uhmnn nace na dauka zai ce mun sai da safe yaje ya kwanta

But to my surprise kafar Shi ya nuna min zoki kwanta, a ina? Na tambaya, a nan mana in har ina kusa dake baki bukatar pillow, Haba dai sai kace wata karamar yarinya, zarah in banyi kuskure ba you are just 22 da 'yan watanni ba kiyi 23 ba

To ai na girma na fada ina bata fuska kamar zanyi kuka Naji kin girma yanzu dai zoki kwanta gobe zamu ci gaba, bani da zaɓi tunda anfi karfina haka na kwanta nasa kaina a kafarshi

Sai da baccin ta yayi nisa sannan ya dauke ta ya kai daki akan gado addu'a yayi mata ya tofa kafin yaja bargo ya rufe ta tare da rage mata sanyi AC sannan ya fita a falon ma ya kashe komai yaja mata kofa

Kwarai yaso ya kwana a dakin amma wata zuciya ta bashi magana in dai har zai fara kwana dakin ta to saida izini ta don haka ya hakura ya koma dakin shi

**********

Da safe ma shi ya tashe ta da ya shigo suyi sallama zai tafi Kaduna amma ba can zai kwana ba amma da can zai kwana ba abunda zai hana shi tafiya da zarah

Zarah kafin in dawo ki tabbata kinyi kitso yau kinji ko zan kira hajja in faɗa mata na turo ki kitso kuma kar ayi manya, zaman kitso fa da wuya hakuri kawai mukeyi shi yasa ban cika kitso ba

Saloon ma zani ayi mun Bob Mali, meye kuma haka? kalaba Ƙanana duk yadda kika yi ni dai kitso nake so ayi. Shi kenan sai ka dawo, Allah ya dawo min da kai lafia ameen yace kafin ya fita

Sai karfe biyu na fita gun hajja na fara tsayawa kafin na tafi Saloon kitson baby face aka yi mun daga kasan twisting mutanen Saloon din sai yabon kyan kitson suke ribbon nasa na kama shi a tsakiya na sake shi har akan kafaɗa ta

Ina hanyar komawa gida maryam ta kira ni kina ina ne? ba gaisuwa wannan tambayar haka saboda ina gidan ki ohh girl friend sorry ina kan hanya naje kitso ne ki jirani dan Allah

A cikin mota na same ta maryam ya baki shiga cikin gidan ba sai ki zauna a mota sai kace bakuwa ai tunda kindawo sai mu shiga tare bismillah muje, ya aka yi bakizo da intisar ba yau? tana gun kakar ta, Allah sarki

A falo muka tarar da salima sallama da muka yi ma bata amsa ba I don't know why Don haka ban tsaya mu gaisa ba kawai na wuce abuna ɗakina na buɗe muka shiga nida maryam

Alwala ta fara daurowa me zan kawo miki kisa wa bakin salati bari Inyi sallah har biyar da rabi duk mune shi yasa nake ta sauri inzo gida

Bayan mun kare sallah noodles na dafa mu kaci Talatu nasa tazo ta kwashe kayan, aunty da baki nan an kawo kaza da nama da kifi, waya kawo? saleh ne yace uncle yace akawo na gyara duka nasa freezer, yawwa Talatu kin kyauta nagode

Yawwa na manta in gaya miki an kawo mun kaya daga Sokoto muje mota ki duba in akwai wanda kike so kuma karki cemun aah  aah

Muna fitowa daki y ahmad yana shigowa  ban san lokacin da na furta kalmar habibi ba maryam ta turani ta baya kije mana da ɗan sassarfa na isa gunshi hannun shi ya bud3 mun alamun in  karaso da sauri na faɗa jikin shi ya rungume me ni

Is this how you missed me dagowa nayi tare da raba jikina da nashi sannu da zuwa ya Ahmad zarah ta ya gidan lafia lau sai lokacin maryam ta gaida shi but still yana rike da hannu na zan dan raka maryam zata wuce ina zuwa

Ba komai mun gode da ziyara a gaida yara yace da maryam kafin ya sake min hannu duk abun nan da ake salima na falon but am sure bata ji ba don ta saka earphones a kunnen ta

A mota maryam ta kwaso mun wasu tarkace  wasu kamar gumba ga dai sunan tace in zaɓa maryam ni ina na san amfani su da zaki ce in zaɓa ohhh to bari ni in zaɓa miki masu kyau

Haka ta haɗoni dasu ko wane da yadda ake amfani dashi haka nan na kaisu daki na boye sai na samu mai so zan bada kyauta don bana tunanin zanyi amfani dasu ko waɗan da ya habi ta bani da bata tsare ni ba da bazan shaba

Sai wuraren karfe tara ya Ahmad ya kirani ta waya inzo in same shi falo na riga nayi wanka don haka ƴar saman rigata kawai na dora da yake dogon hannu ne hula kawai na  saka tare da sake kitsona ta gefen dama

Falon na shiga da sallama bayan na zauna nace ya Ahmad gani dama na tarar da salima a falon nayi mamaki haka wace irin magana ce so serious haka da baza'a bari har da safe ba

Maganar da ya fara ita ta dawo da hankali na, ina so inji ya zaku tsara zaku tsara ranakun girkin ku da sauri na kalle shi, girki kuma Ahmad kamar ya kana nufin zamu raba kwana da ita yadda ta nunani kamar wata kashi

Eh hakan nake nufi, ina so in san dalilin hakan saboda itama mata ta ce ohhhh yanzu kasan da hakan for over a year ina gidan nan baka taɓa cewa hakan ba sai yau Sam ban yarda ba

Wancan lokacin ya wuce kuma ko menene ya faru wannan tsakani na da ita ne ba ke ba don haka ki fidda kanki a ciki, bazan fidda ba wallahi bazai yiwu ba I can't share you with anyone Don haka asan tayi

Banyi niyyar sa baki na a cikin rigimar su ba amma ya kamata in maida ta akan hanya in ta manta in tuna mata cewa bafa ita kadai ce mace a gidan ba

Salima na kira ta, duka su biyu suka juyo suka kalle ni, ina so ki tuna ba ke kadai ce matar aure a gidan nan ba kuma da kike cewa bazaki iya sharing din shi da kowa ba kar ki manta mijina ajiya na baki kuma na dawo in karɓi ajiya ta

Ina so ki sani gobe zan karɓi girki kuma zanyi kwana biyu kafin kuma ki karɓa don haka girkin mu zai zama na kwana biyu biyu is left to you in zaki iya in kuma ba zaki iya ba tsakanin ku

Ya Ahmad sai da safe, Allah ya tashe mu lafiya yace don haka na juya na tafi abuna bazan iya sauraren rigimar su ba don wannan lalurar su ce ba tawa ba don zama da ya Ahmad yanzu na fara





Enjoy dis I think dis is d longest chapter I've ever wrote

book_addiict 






BAZAN KARE A HAKA BAWhere stories live. Discover now