Part 10

33 5 1
                                    

Tunda na dawo bamu hadu da ya Ahmad ba haka salima saboda ranar Thursday gaba daya ina daki na, haka kawai Naji bana son fitowa abinci ma sai dai na kira Talatu ta kawo min daki.

Yau Friday haka kawai na tashi ina jin wata tsabta na hau gyaran dakina har falo ko ina na gyara tsab har kitchen bayan na kare gyaran na fito a falo muka hadu da salima.

Kallo ta bini dashi irin kallon raini nan ganin tana kallona yasa na ce mata sannu da gida, tsaki kawai tayi ta juya ni kuma na kama hanyar dakina amma abun da mamaki irin wannan bai taba shiga tsakani na da ita ba, ba ruwan ta dani nima haka amma me ya faru yau, Allah ne masani. Nayi shige wata daki.

Wuraren 12 na kammala share share na saboda ta yau ba irin ta kullum bace ko ina yayi haske kamar dakin amarya har wani fresh air nake ji ta ko ina. Na kunna diffuser nasa wasu oil perfumes a ciki haka kuma na kunna bunner nasa turaren wuta abu sai kace mai karɓar girki yau.

Wanka na shiga shima dai ba baya ba, yau nayi abunda na jima ban yiba kwalliyar kwarai su eyebrows, eyeshadow da komai amma I tried making it nude ni kaina na san nayi kyau, wata super na dauko a cikin sababbin kaya na na saka dinki yayi kyau sosai kayan kamar a jikina aka yanka saboda yanda suka zauna ɗas.

Gown ce fitted amma kamar riga da skirt sai in ka kalli baya na da kyau zaka gane ba skirt bane. Daurin ture Kaga tsiya nayi ya mun kyau kwarai, dama kitson baby face nayi a kd sai na sake tsorayen a baya. Suratul kahfi na kunna a falo na ina bin karatun.

Bayan karatun ya kare nayi sallah sai na dauko counter ina tasbih na jima wurin a zaune sai kusan karfe uku na fito daki da niyar zuwa kitchen

salima na zaune a falo na wuce ta kamar dai dazun tsaki ta sake yi yanzun kam abun ya mun ciwo ashe ba shikenan ba.

Fati kike ko waye miye ma'anar wannan kwalliyar sai kace mai shirin tarar miji mamaki da imani suka taru suka rufe mun baki gashi ni dama ba gwanar sa in sa ba kafin in samo amsar bata kuma Naji ta sake jeho maganar.

Hmnn ina mijin nayi dake da yau sai Ace miki sarauniyar mata Allah sarki wat a pity amma matsayin ki kawai 'yar tsaron daki  sai ci da kashi kawai kika aje. Da nice ke da tuni na kama gabana in je in nemi meyi dani ba dai in makalewa wanda baya Sona ba.

Zuwa wannan lokacin ban san me nake tunani ba a tsaye kawai nake na kasa tunani komai. Sallamar ya Ahmad ta dawo dani hankalina Idon sa kyam a kaina sannu da zuwa nace da shi yawwa Zarah. Juyawa kawai nayi na wuce daki, maganganun salima sun yi min tsauri.

Allah ya sani ban son tashin hankali, ina iya kokari na in kiyaye hakan shi yasa ni bani da abokin fada. Amma yana daya daga abunda ke saurin bata mun rai a dinga jifata da maganganu wallahi ban son hakan hakan ya kan kawo raini a tsakani na da mai yin shi zuwa gare ni.

Ruwan ma da naje daukowa haka na dawo, ni banyi kwalliya don kowa ba sai don ra'ayina amma me yasa zata yi min irin wannan maganar.

Me zarah keyi nan a tsaye? Yaji a Jikin sa kamar wani abu ya faru a tsakanin su daga expression na fuskar ta ya nuna akwai damuwa

Tun lokacin da salima tayi maganar nan ya san da wuya ta kyale ta kuma wannan ai shi zata kira wa ruwa, yawan damuwar ta matsala ne a gareshi saboda ko yaushe baba saleh na kan jaddada mishi, hakan yasa har yake dan kula ta.

Kuma ya lura bata da matsala ya yaba irin hakurin ta da kawaici irin nata wanda salima bata da shi. Haka kuma take taken salima na kwanaki nan a kanta baya son su

Koshi da take zaman shi bai takura ta ba ba ruwan shi da ita haka a wurin ta. Kyale salima tayi wa zarah yadda take so zai kawowa zarah damuwa wanda hakan matsala ce a wurin shi.

Bayan ya fito daga daki kai tsaye akan dining table ya wuce ya zauna ya kira salima taxo ta zuba mishi abinci, yace kira min zarah first, me zata yi ma? Wai meye matsalar ki ne salima babu to ki kira min ita

Nifa ban taba zuwa dakin ta ba dai dai nan Talatu ta shigo, Talatu kira zarah kice ina neman ta, wai neman me kake mata ka wani damu a kira ta.

Kamar ba dashi take magana ba ya kyale ta dama ya lafiyar kura bare an taɓa ta, hakan ya ɓata mata rai amma itama ta tsaya ganin neman me yake mata

Ko da Talatu ta fada min sakon kiran daki na shiga na dauko mayafi saboda dazu Naji kunya kwarai da irin kallon da ya bini dashi  sai nake ganin kamar tufafin da na saka ne kamar sun bayyana surar jikina

Akan dinning na same yana zaune ita kuma salima a tsaye, na lura tunda na fito yake kallona ya Ahmad gani, yaushe kuka dawo daga kd din? Wednesday da na fada ma

Amma ai ban ganki ba sai yau, eh eh koda na dawo ranar kun fita har nayi bacci Baku dawo ba jiya kuma ban samu haduwa da kai ba na fada murya ta na rawa

Baki san hanyar daki na bane da sauri na girgiza kai aah aah, aah aah me? Bam sani ba. Dis should be your last time of doing this don't repeat it again! Jikina na rawa nace in sha Allah don gaskiya ma tsorata

Kusan minti 5 sannan yace salima ke nake jira ohh sorry tazo zuba mishi abinci har lokacin da ya fara cin abincin ina tsaye sai da ya dago ya ganni yace kina iya tafiya

A hankali murya ta ta fita ya Ahmad don Allah kayi hakuri in sha Allah bazan maimaita ba. Ba komai ya wuce. Nagode nace tare da juyawa na koma daki.

Salima taji dadin fadan da akai wa Fatima ko ba komai an nuna mata matsayin ta. Duk wannan gayun bai dame shi ba bai ma nuna ya gani ba woww har suka kare cin abinci murmushi take.

Shi kadai ya san me yake saƙawa akanshi amma ta birge shi yau, kwalliyar ta mai natsuwa kayan jikin ta sun karbe ta kuma kunyar ta ma ta birge shi.

****      *****       *****

Bayan sallah magrib a waya ya kira ta zan tafi gaida Hajja in zaki ina falo, okay to ina zuwa. Yaushe ya fara faɗa min zai tafi gun Hajja sai dai in ya tafi inji a bakin Hajja wasu lokutan.

White powder kawai na dan kara dama ban gode kwalliya ta ba sai turare versace mai sanyi kamshi dana fesa nasa takalmi na mai dan siririn tsini 3inch. Ban dauko jaka ba wayata kawai na dauko sai mayafi na dana ɗora akai.

Na jawo kofar dakina na rufe, karar takalmi na kawai zai sanar da kai ina zuw, ina isowa ya tashi daidai lokacin Salima ta fito kallon mamaki ta bini da shi

Ya Ahmad ya riga ya fita ke kuma ina zuwa, mamaki ya cika ni wai me ke damun matar nan? Anya lafiyar ta ƙalau kuwa? Gaskiya akwai ayar tambaya a behaviours dinta

Bayan shi kawai na bi ban tsaya kula ta ba ina zuwa bakin motar nayi tsaye bismillah yace dani saboda ni na fara isowa bakin motar na kama kofar baya Naji murya shi wa zaki maida driver. Aah salima na zuwa baice komai ba ya shiga motar itama ta zo ta shiga sannan ya tada motar muka fito.

Kwarai hajja taji dadin ganin mu munyi hira, bamu bar gidan ba sai kusan goma na dare. Kwarai Naji dadin zuwan mu gidan hajja ta hado mu dasu kayan yaji, kuka da sauran su.

Hi my lovely followers so far we're in chapter 10 don't forget to vote and vote and vote I love you 😘😘😘

And for those that are not following me on Wattpad please click the username👇 and follow don't forget to vote again comments I like to see your comments let me see how far have we gone love you

book_addiict

BAZAN KARE A HAKA BAWhere stories live. Discover now