Part 11

37 2 1
                                    

Kaɗaici ba dadi, ni kaɗai a daki ba abokin hira ni ba fita nake ba gashi ni ba gwanar kallo ba abokai bare Ince akawo min ziyara yaran Aunty Hadiza ne suma suna school yaran kawu su basu cika zuwa ba dama, In dai ba Fridays da nake zuwa wurin hajja ba.

Nayi hakuri har hakuri na ya kare, duk da an ce hakuri baya karewa amma wallahi na gaji. Last option zanje muyi magana da ya Ahmad kawai asan tayi.

"Kiyi hakuri Fatima na san kina yi, amma kar ki manta wannan auren naki wani buri ne na mahaifi ki kika cika. Amma karki manta don na baki hakuri ba ina nufin ki zauna haka ba dole ki tashi tsaye ki kwaci hakkin ki a cikin gidan nan in ba haka ba a haka zaki tabbata. Ki kwaci hakkin ki ga mijin ki haka kuma ga aboki yar zaman ki har dai yanzu da ta fara raina ki in har bai shirya karbar ki a matsayi matar shi ba a yanzu to bansan yaushe hakan zai faru ba bayan kusan 3yrs da auren ku shekara daya da rabi da tarewa to akwai matsala"

Amma maryam ta yaya hakan zai faru bayan ko girki bani da a gidan nan?

"Tsaya maryam ruwan sanyi bazai yi maganin wannan matsala ba ni yaushe na taba gani aure irin wannan wallahi bazan iya hakuri da kika yi ba, ni dai tawa shawara itace ki same shi kuyi magana kiji ya matsayin auren ku yake in bai amsa ki ba ki bashi kamar sati biyu ki jira amsar amma ki sani sai kin haɗa da dabara lallai zai amsa miki har dai in kince zaki haɗa shi da Baban shi, daga nan zaki ji matsayin ki. In har ya baki amsa zamu ɗora daga nan"

Gaskiya shawarar zainab itace abin dubawa for now, in sha Allah gobe Saturday zan same shi inji matsayi na shikenan.

******       *****          *****

Girki nake yi a kitchen ina sauraren wata waka a mp3 dana yi connecting da waya ta ina bin wakar a hankali ta maher zain acikin wakar sa ta in sha Allah, natsuwa ke shiga ta a hankali daga yanda yake zaro baitukan wakar

Ya jima tsaye a kofar kitchen din yana kallon ta yanda take bin wakar da kuma aikin ta cikin nutsuwa, bai san me take dafawa amma komenene zaiyi dadi har yawun shi sun tsinke abu ga mai jin yunwa daman

Kwarai ya shagala har yaso ya manta da abunda ya kawo shi gunta, a hankali ya sauke ajiyar zuciya. knocking kofar yayi har sau biyu kafin ta juyo

Tadan tsorata da ganin shi a wurin volume din wakar ta rage tare da gyara dankwalin ta da ke kokarin zamewa wanda ya bayyana gashin ta kadan

Sannu ya Ahmad kana bukatar wani abu ne bai san lokacin da ya daga mata kan shi ba, Abinci nake so yunwa nake ji kwarai, okay zaka jira plz da ɗan saura kadan in kare

Falo ya koma ya zauna sai a lokacin ne ya tuna abunda yaje faɗa mata saƙon umma ansa date na auren sakina, amma bari ta kawo mishi abinci sai ya faɗa mata

Acan kitchen kuwa Biryani rice take yi da chicken curry dama tana da kunun aya a  fridge don haka samosa ta dauko ta soya mishi ta haɗa da kunun aya ta kai mishi

Ya Ahmad kaɗan ci wannan kafin na kare main dish din kallonta kawai yayi tare da daga mata kai, ta juya zuwa kitchen

To ko ina salima ta tafi? Amma ai da Talatu ta tanadi wani abu kafin ya dawo daga masallaci ohh manta da wannan ki kai mishi abinci kawai duk inda suka tafi su suka sani wani sashe na zuciyar ta ke wannan zancen

Sabon warmers dina na dauko nasa abincin a ciki, akan dinning naje na jera kayan abincin na jera komai dai dai

Tunda ta fara fito da kayan abinci yake kallon ta, wai ita me yasa bata da matsala ne he can still recall tana sabuwar amarya haka zata yi abinci ta jera mishi amma yaki ci, baza tayi fushi ba gobe ma ta sake but still jiya I yau har ta kai ranar da ta mishi maganar abinci ya bata harsh warning kar ta sake ajiye mishi abinci tunda shi a dan yunwa bane kuma ba yaro bane ya san inda zai je ya samu abinci in yaji yunwa.

Ranar ya lura har kuka saida tayi don ta tsorata matuka yanda ya taso mata da fada amma duk da haka bai ji tausayi ta ba ya lura tun ranar bata sake ajiye masa abinci ba haka kuma ba ruwan ta da shiga harkar shi allurar gaban ta kawai takeyi

Ko Saturdays da yake zama gida bata damuwa dashi wani lokacin ma yinin ranar gaba daya bazai ganta ba sometimes ya kan tambayi mai gadi ko ta fita in yaji shiru yayi yawa amma bazai iya zuwa ya diba ta ba, bai san ciwon ta ba haka bacin ranta da farin cikin ta Sam wannan ba matsalar shi bace

Amma yanzu magana daya tayi mashi abunda yake so duk da ya san bada shi ta dora abincin ba amma hakan bai canza komai ba. Ya Ahmad bismillah na kare yawwa thank you.

Juya kawai nayi zan koma daki ina tunanin yanzu ne ya kamata muyi magana dashi don ina son sanin matsayin aure na dashi this is the perfect opportunity for me

Zarahhh! Can you serve me please?

Chak na tsaya daga baya na juya zuwa table din ban cika son tsaiwa a kusa da shi ba saboda kamshin turaren shi na jan hankali na da yawa (Fatima zarah masoyiyar turare)

Bayan nayi serving dinshi yace dani zauna ba musu haka na jawo kujera na zauna, a hankali yake cin abincin shi, chan ya dago umma tace in gaya miki ansa date din bikin sakina

Da sauri na dago kai, yaushe ne ya Ahmad? Nan da wata biyu yace a takaice wowww ashe zamu sha biki Allah ya basu zaman lafiya da zuriya dayyiba, ameen ya amsani.

Ina so in mishi magana amma nauyin baki ya hanani na rasa ta ina zan fara, har ya kusa kare cin abincin ina zaune sai saƙawa da warwarewa nake amma na kasa samun mafita ga dama na samu amma zata zama ta banza

Zarah na gode, har zai tashi kan table na kira sunan shi a sani yayi tare da tsayawa shiru nayi na kasa cewa komai kuma kusan 15mnt na kasa cewa komai shi kuwa ya samun ido yana sauraren me zan fada

Hakan ya taimaka kwarai wurin hanani magana, zarah ina sauraren ki yace, mekike son fada min? Ya Ahmad ba komai, ahh ahh Fatima akwai tunda kika zauna a nan na lura kina son yin magana amma kin kasa ki faɗamin koma menene ina sauraren ki

Ba komai ya Ahmad a yanzu amma idan lokaci yayi zan faɗa ma in sha Allah, ko menene ba wata matsala bace, bazan matsa miki ba amma naso jin damuwar ki amma a duk lokacin da kika shirya a shirye nake in saurare ki

Ina tashi daga kan kujerar na juya zan tafi sai Naji an jawo ni ta baya da karfi na dawo kawai runtse idanuna nayi ina jiran inji meke shirin faruwa dani.......

*****
Meke shirin faruwa ne?

Waya jawo Fatima ta baya?

Meyasa Fatima ta kasa tambayar Ahmad matsayin ta?

Shin ina mutuniyar ta shiga ne (salima)?

Shin Ahmad ta shirya kabar Fatima a matsayi matar a yanzu?

Amsar waɗannan tambayoyin dama wasu bayanan na tafe a shafi na gaba da sauran su ku biyo ni a hankali kusha labari.

Taku a kullum book_addiict

BAZAN KARE A HAKA BATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang