Part 13

41 3 0
                                    

Yau Alhamis dole inje muyi sallama da hajja da kuma zainab dama jiya naje gidan maryam, acan na yini mun tattauna ƙwarai akan hukunci da na yanke kuma nake ganin shine dai dai, tayi na'am da hakan amma ta ƙara da lallai in faɗawa hajja cewa ba yanzu zan dawo ba In na tafi Bauchi ko kuma in bari in ta tafi wurin bikin sai muyi magana.

Ban jima wurin hajja ba na fito gidan zainab naje itama muka yi sallama sauran labari kuma sai mun haɗu Bauchi wurin biki, dama zamuje Gombe dama mun kwana biyu bamu je ba (Gombe can ne asali su hajja amma zama ne ya kawo mahaifi su nan garin suma suka yi aure anan suka zauna da iyalen su)

Ban iso gida ba sai kusan six, dama yau bani da niyyar girki rabin da in mishi girki ma tun ranar, na riga na sawa rayuwa ta bazai yiwu in zama mai girki ba a gidan nan in girka shida matar shi suci, in har suna jin yunwa to matar shi na nan ta girka musu ko kuma sabuwa mai aikin da na gani ta kawo ba san me ya faru da Talatu ba kuma ban tambaya ba.

Bayan magarib sai ga Talatu dakina nayi mamaki kwarai, Talatu ina kika shiga ne wallahi Anty da Amarya zata yi tafiya tace mai gida yace in tafi sai ta dawo nace mata kefa tace tare zaku tafi, amma sai kika tafi ba sallama ba haka ba Anty a lokacin kin fita kuma tace ranar zaki wuce baki da number ta? aah Anty bani da shi

Yanzu ta san kin dawo ehh na kira maigadi ne yace min ai ta dawo, shine na dawo dazu kuma na tarar ta kawo sabuwa mai aiki shine nace bari in jira ki ki dawo inji in har zaki bari in zauna wurin ki

Ki jira a dakin ku in ya Ahmad ya shigo zan mishi magana in ya aminta sai ki zauna, yowa Anty ina godiya fa, ba komai Talatu zaki iya tafiya

A falo na same shi shida gimbiyar don haka ba halin magana a gaban ta. Har na juya ya kira ni ya dai kinzo kuma kin koma baki ce komai ba, uhmm fasawa nayi murmushi yayi menene fadi ina jin ki

Inna faɗi kayi alkawari zaka yi? Eh nayi fadi  ina jin ki, okay shawarma nake so maizafi shikenan? ehh to bari ayi miki order, No kaini zakayi in siyo, kuma! Ehh to shi kenan muje

Dama doguwar riga ce a jikina dakina kawai na rufe na dawo muje nace mishi, key ya dauka muka fito saida ya tada mota nace mishi matar ka baza ta ba aah yace

Saida muka fito gidan gaba kadan nace mishi kayi parking zamuyi magana, ina jin ki Talatu ta same ni akan maganar sallama ta daga aiki da kayi, yaushe? Tace salima ta faɗa mata da zata yi tafiya cewa kace ta tafi sai ta dawo.

Shiyasa ta tafi kuma yanzu ta dawo tace mata ta tafi ta samu sabuwar mai aiki shine tace tana so in har zan karbeta ta zauna dani, to me kika ce mata? Nace ta bari sai na faɗa ma duk yadda muka yi zata ji

To ai dama Dana sa a kawo ta ku duka aka kawowa in har taji bata son zama da ita in kina so ai zaki iya zama da ita ba matsala, nagode zan iya tafiya da ita Bauchi gobe? Ehh

Baki faɗa min abubuwan da kike bukata na tafiya ba, Alhamdulillah so far bana bukatar komai har tsaraba duka nayi. Okay ba matsala zan saka maki kudin ki da kika kashe zanyi magana yace kinsan bana son gardama, godiya nayi mishi

******          *****         *****

Mun isa Bauchi lafia a nata mana barka da sannu da zuwa, gidan baba saleh muka fara sauka, anan dakin sakina nayi wanka na shirya bayan munchi abinci sannan nace zan tafi wurin inna saida ya Ahmad ya gama jamin rai kafin ya fito muka tafi.

Naji dadin ganin inna kwarai da gaske ina son wannan baiwar Allah kamar yadda take so na koda yaushe ta kan ce kina kama da mahaifiyarki kin dan fita haske kadan.

Anan ya barni ya tafi na shiga cikin gida muka gaisa da jama'ar gidan har gidan Baffa Ali naje gidan ya habi kawai ne banje ba nace sai gobe

Wuraren 9:30pm ya dawo ina kwance kusa da inna muna hirar mu mai dadi wai yazo dauka ta, ai na dauka nan zan kwana to ki sauke inji tashi kibi mijin ki inna ni ba anan na saba sauka ba In mun zo to me yasa yanzu kuma zaki ce sai na bishi

Kinsan ki tashi kafin in aika kiran Baffan ki yanzu kiji ba dadi wai inna kora ta kike yi gobe ma ba zaki ganni wurin ki in nazo gidan baffa zan tsaya in ma kin iya karki zo koma ki koma goben

Haka na fita ko sake juyo wa banyi ba, a motar ma haka na zauna ina wani kukkumbura fuska a dole an cilastani muna isa na fita motar na wuce cikin gidan shi ma ban waiwaye shi ba

Umma bata falo don haka dakin sakina na wuce mayafina da wayata na aje a gefe na dan kwanta kan gadon, sakina na kan kujera tana waya. Allah banji dadi ba ya zaa wani ce sai na dawo bayan ba'a saba hakan ba mtseewww nayi zaki na sake juya wa

Madam waya taba ki Naji sakina na tambaya ba ya Ahmad bane na saba in mun zo wurin inna nake sauka shine wai yau yaje wai in fito mu tafi, aahh don kin biyo mijin ki shine na wannan bacin ran to yaushe rabona da innar kusan fa wata 8 uhmm madam aure fa kikayi

Hmmm ba aure ba ai zakiyi kiji in da dadi a raba ka da gidan ku kana ji kana gani 'yan uwa ka suyi ma nisa, baka da ikon kanka mtseewww bar wannan maganar kawai ina umma? Tana wurin baba ina jin barin in watsa ruwa ko zan ji dadin bacci

Bayan na fito wankan na shirya ciki. Pyjamas masu taushi na saka hijab akai. umma ta shigo dakin mun dan taba hira sai ga wayar ya Ahmad wai sakina ta kawo mishi kayan tea

Haka ta haɗa ta kawo min wai yace abani in kawo mishi, umma na zaune ya zaayi in tashi zuwa kai mishi kayan tea, tashi mana Fatima kinsan mijin naki yanzu sai ya damu Mutane haka nan na tashi cikin kunya na karbi kayan

Toh muje ki raka ni tunda bansan inda yake ba na cewa sakina kasa ksa yadda umma baza ta jimu ba, dariya tayi muje Anty Amarya hararar ta nayi wacece amaryar ke mana baki san sabon gini mijin ki yayi acikin gidan nan ba don haka ni yanzu raka amarya zani

Wallahi kin dauki bashi ai jibi ne bada nisa ba duk abunda kika min zan miki ninkin shi, Naji dai bari Inyi kafin ayi min. Can daga gefen hagu ne sabon gidan dan ƙarami mai kyau self contained ne bansan wa zaisa Aciki ba a tsakanin ku cewa sakina

Nidai binta kawai nake na ƙagu in ajiye mishi kayan tea din in dawo in kwanta saboda gobe nasan da wuya sakina ta barni dole akwai abubuwan da zamuyi, muna zuwa bakin kofa tace min to bismillah ni na tafi ki tsaya mana mu tafi tare dariya kawai sakina tayi ta wuce abinta

Knocking nayi tare da murɗa kifar na shiga da sallama a bakina daga daki ya amsa a centre table na aje kayan tea din na nemi kujera na zauna, shiru bai fito ba toko a daki yake nufi in kawo mishi don haka kawai na dauki tray din na nufi dakin

Shima saida nayi sallama ya bani izini kafin  na shiga, dakin kamar zai fi falon girma akan bedside drawer ya nuna min in ajiye kayan Tea din zan juya yace zo nan wa zai haɗa min tea haka na shiga haɗa mishi na kare na kika mishi kofin jira kawai yace yaci gaba da shan Tea dinsa

Yau naga isa ni Fatima ya Ahmad bacci nake ji gefen shi ya nuna min da sauri na zare ido ina kallon shi a nan zan kwana kanshi ya gyada min, don Allah ka barni in koma wurin sakina bazan iya kwanciya gado daya da kai ba....

BAZAN KARE A HAKA BAOnde histórias criam vida. Descubra agora