BARKIN'DO part 1-2

7.3K 300 4
                                    

🌷 *BARKIN*'DO*🌷
                
*[ very interesting story ]*

*Story & Writing -By AUFANA*✍

✨✨ *Dovoted to - ALL FULANI'S IN THE WORLD* ✨✨

*Page 1- 2*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*'Dan tsokaci*

*M* asarautar [JAMNAZ] babbar masaurata ce, babbar daulace wacca tashahara wajen gudanarda gaskiya da adalci agun talakawanta, tsohuwar Sarautace wacca akagada tin kakannin kakanni, burin kowanne sarki, bawa, ko d'a yakasance ak'ark'ashin masauratar JAMNAZ  wacca sarki ABDUL-K'ADIR ke gudanarda sarauta acikinta bayan saukar mahaifinsa, hakazalika burin kowanne sarki yasamu magaji saidai wannan sarkin Allah baibashiba, ganin Sun kwashi shekaru basu sami haihuwa ba saikawai ya yanke shawarar yak'ara aure, cikin ikon Allah kuwa bayan yak'ara auren saiyasami haihuwar d'a namiji hakan kuwa bak'aramin bak'in ciki yayiwa gimbiya LAILA ba, yayinda taci burin ganin bayan jinjirin da gimbiya JIDDAH uwa ga magajin sarki ABDUL-KADIR jika agun sarki ABDUL-MALIK wato [ ABDUL-JABBAR ] tahaifa,,, wanda yaci sunan kakansa sarki na shida amasarautar [JAMNAZ ], yanayin  kunya irinta Fulani yasa mahaifiyarsa tamasa inkiya da *BARKIN'DO* wato mai albarka kenan,,, kimanin shekarunsa uku gimbiya jiddah tasake haihuwar tagwaye meerah da meesha tofa nan masifa hassada kishi dakuma mugun nufi sukak'ara tasowa gimbiya Laila azuciya, BARKIN'DO nada shekara goma sha uku maimartaba yakaisa k'asar Australia karatu,,,

Meerah da meesha nada shekara daya da haihuwa gimbiya laila tasami ciki ta haifi 'ya mace maisuna FAINUS haka maimartaba yaci gaba da basu kulawa yana Masu tarbiyya iri d'aya yayinda gimbiya laila keyiwa 'yarta Mai irin halinta tata tarbiyyar daban,,,..

K'aton gidane Mai d'aukeda part hud'u, gimbiya laila d'aya gimbiya jiddah d'aya maimartaba d'aya saikuma sarki mahaifin mai martaba d'aya tareda matarsa,, Lambu uku gimbiya laila d'aya gimbiya jiddah d'aya sai tsohuwa matar sarki d'aya,, ak'allah akwai ma'aikata guda 35 Masu hidima mata da maza kowanne danasa 'bangare bayan jakadiya da jakaden mai martaba akwai shugaban gida wato nahannun daman sarki da mai martaba wanda komai nagidan yake ahannunsa tindaga abinci har izuwa sitiru na sarki da mai martaba shiga da fice nakomai baayi saidasaninsa, shekarun da yakwashe acikin gidan yasashi samun wannan matsayin,,,...

Dikda haihuwarda gimbiya laila tasamu amma batai godiyar Allah ba gani take maimartaba yafisan gimbiya jiddah da 'ya'yanta wanda kuma bahaka bane yana nuna adalci atsakaninsu bairaba 'ya'yansu ba dik abunda yayiwa 'ya'yan jiddah shi yakeyiwa na laila,, adik kwanan duniya burinta baiwuce taga bayan jiddah da 'ya'yanta ba, badanda yawan ibada da yawan azkar ba da tini hak'arta tacimma ruwa akan gimbiya jiddah yaranta,, dikda sarki yahad'a aurensu amma sam basa santa saboda mugun hali irin nata hakan yasa suma tasakasu alayin mak'iyanta da 'yarta dandai bayanda ta iyane dasu kawai amma suma tace idan tagama da maimartaba da gimbiya jiddah da yaranta kansu tayo,, Kusan dik k'arshen wata saitaje gun bokanta kar'ban magani tazo ayi binne binne da shafe shafe, wasu kanyi tasiri akan maimartaba wasu kuma basayi kunsan shi maganin tsafi d'ankwan arba'in ne,'....

_Allah ka shiryardamu da zuri'armu baki d'ai ka ganarda Masu 'bata domin su dawo hanyar gaskiya kozasu samu rabo agobe k'iyama ameeen_

         ************

*GUNDARIN LABARI*

Gimbiya jiddah ce zaune akatafaren falonta yayinda kyawawan yaranta ke zagaye da ita wato meerah da meesha, meerah nayanka mata 'ya'yan itatuwa tanasha meesha kuma namata tsefa kawai saiga fainus tashigo bako sallama tawuce tazauna,, kallonta meerah tai sannan tace waike wace irin wawuya ce dazaki shigo bako sallama angaya maki nan falon kafirai ne hararanta tai sannan tace hankalinki yana ina danai sallama bakijiba,  cikin 'bacin rai meerah tamik'e tsaye zatai kanta ummi tadaka mata tsawa tareda dakatar da ita ""barta kawai kyaleta""  ganin ta aikata abunda yakawota kawai ta mik'e tsaye tafice tareda yin tsaki, nan ran meerah yak'ara 'baci kawai tafice daga falon dama meerah akwai zuciya Ummi takyaleta saboda tasan halinta idan ranta ya 'baci, meesha takalli mahaifiyarta tace ""Ummi wlh rayuwar fainus nabani mamaki irin wad'annan halaye nata kullum mugun ranta k'aruwa yake"" murmushi tai tace hakane kudinga mata addu'ah Allah ya shiryeta meesha tace munayi kam saidai mucigaba da yi amma ni inaganin anya kuwa zata shiryu dik halayyar mama ce tad'akko harma tana neman tafita, murmushi Ummi tai tace hakane insha Allah bazasu ta'ba cin galaba akanmu ba kudage da azkars insha Allah bazasu iya komai akanmu ba, to Ummi zamucigaba da yi insha Allah, shikenan Allah yak'ara karemu daga dikkanin mai sharri suka amsa da ameeen tare,,,...

Kimanin k'arfe 10:30am mai martaba yasaka akirawo kowa nacikin gidan, nan aka hallara à fada nan yake sanarda kowa cewa gobe Magajinsa zai dawo wato *BARKIN'DO* farinciki agun kowa baya misaltuwa tindaga bayi fadawa har izuwa mutan gida, a'bangaren mama kuwa haushine kamar yakashe wato dama dan wannan maganarce yawani tarasu kamar wani abun yafaru saidai fa ba halin nunawa afili amma dikda haka fuskarta babu walwala,,,...

Maimartaba yasaka ayi shela ashaidawa talakawansa gobe idan andawo daga sallar juma'ah akwai k'asaitacciyar liyafar ci ak'oshi ta murnar dawowar magajinsa jinin jikinsa, masarautu goma ke ak'ark'ashin masauratar kuma dik maimartaba yasaka ashaidamasu dawowar magajinsa tareda k'asaitacciyar liyafa,,,...

Bayan maimartaba yagama magana saikowa yakoma sashensa, murna agun meerah da meesha ba'amagana sai tsalle suke d'anuwansu zaidawo, Ummi ma haka saidai bata nunawa saboda kunya irinta fulani amma zuciyarta fall take da farinciki, hakama su sarki da hajiyarsa sai murna suke d'an jikallensu zai dawo,'...

Gimbiya laila nashiga sashenta tawuce k'uryar d'akinta tareda rufe k'ofar, wayarta ta d'akko takira wata Number kira d'aya aka d'auka cikin hanzari tafara magana ""gimbiya sailuba hak'armu takusa cimma ruwa gobe *BARKIN'DO* zai dawo dan haka anjima ki shirya zansan yanda zanyi nasaci hanya nazo muje gun boka laflaftau""  banji abunda d'ayan 'bangaren akaceba sai tace ""to shikenan sainazo ""  tai dariyar mugunta sannan takashe wayar,,,...

Around 8:00pm bayan su maimartaba da sarki tareda sauran ma'aikata Sun shiga sallah à katafaren masallacin masarautar gimbiya laila tasaci hanya tabi tabayan gida zata wuce kawai saiga meerah taganta amma ita sam batakula da ita ba burinta kawai tasamu fita,, meerah nakallonta har shiga mota suka wuce kasancewar dik zatayi irin wannan fitar da driver d'aya take fita, wannan shine karo na biyu da meerah taganta Ummi kawai take gayama,,bayan ta wuce meerah tafito daga ma'boyarta tsintsar mamaki ne fall afuskarta Allah ya kyauta kawai tafad'a tawuce 'bangaren hajiya wato kakarsu,,,...

Around 8:15am maimartaba da jakade tareda sarkin gida had'e da fadawa takwas k'arfafa tareda dalla dallan motoci guda shida sukaje tarban magajin maimartaba ABDUL-JABBAR wato *BARKIN'DO* saikusan 9:00am sannan jirginsu yasauka,,,...

Cikin tafiya irinta Masu ji dakansu yake saukowa daga jirgi, kyakkawane ajin farko.............


🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀'''Muje zuwa '''

'''AUFANA for life '''🌷🌷

BARKIN'DO Where stories live. Discover now