[10/8/2018]
🌷 *BARKIN'DO*🌷
*[very interesting story ]*
*Story & Writing -By AUFANA*✍
✨✨ *Devoted to - ALL FULANI'S IN THE WORLD*✨✨
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*📚®
*{onward togarher}**Page 9~10*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Wata 'yar kyamusasshiyar tabarma ce tad'akko ta shimfid'a masa ya zauna sannan suka gaisa da Abban ta tareda tambayar lafiyar jikinsa yace yajisauk'i sosai nan yamasa godiyar taimakonda yamasu jiya BARKIN'DO yai murmushi yace ""ai bakomai Abba yiwakaine Allah dai yak'ara baka lafiya suka kar'ba da ameeen,'....
Abban ta yakalle ta yace "" 'Bingen amin umma ya nokkonommo cutan oyara"" cikin sauri kuwa ta tashi dasauri BARKIN'DO yadakatar da ita dacewa wallahi Abba nak'oshi Alhmdllh cikin murmushi yafad'a nan tadawo tazauna,,,....
Abban ta yakalle sa yace ""gaskiya yarima yau kafara goge bak'in fentinda mukashafawa gidajen masarautu dakuma su kansu masu mulkin, Sam halayyarka tai daban data sauran 'ya'yan sarakuna"" murmushi yai batareda yace komai ba saboda yasan inda zancen nasa yadosa,,,.....
Yad'an jima suna fira da Abban ta daga bisani yatashi zai wuce nan Abban ta yasa tabashi nono kindirmo a kwarya, ba yanda ya'iya dole ya kar'ba amma yace saidai tarakasa harsuje gun shago yasiyi leda yazube saitadawo da kwaryar haka kuwa akayi,, tafiya suke ajere ahankali ya kalle yace har yanzu kink'i kifad'aman sunanki koh yafad'a yana kallonta cikin murmushi,, itama murmushin tai tace ai bakatambayeniba dana fad'amaka,, to yanzu na tambaiki fad'aman dariya tai tace sunana *HUNAYYA* amma abbana yana kirana da 'BINGEL wato d'iya woww nice name HUNAYYA binsa tai dakallo alamar bata fahimci me yafad'a ba, yafahimci haka amma yakyaleta yace waya saka Maki wannan sunan murmushi tai sannan tace Ummi na amma tarasu lokacin ina k'arama,,Eyyah Allah yajikanta yagafarta mata tace ameeen,'.....
Kallonsa tai tace amma kai kamar ba yariman k'asar JAMNAZ ba kallonta shima yai shima yace mekikagani hala,, tace Sam bakada halayya kamar ta sarauniya Marwa da mahaifiyarta,, wane irin halayyane kegaresu ya tambaita d'auke idanunta tai daga kallansa tafara magana,'....
Sarauniya MARWA muguwace halayyarsu d'aya da mahaifiyarta zan iya cemaka suke gudanarda mulki a wannan garin yanda sukagadama haka sukeyi, idan iyayenmu sukai noma saisuce dole saika raba biyu fada itakeda kaso d'aya kaikuma d'ayan nakane suna kar'ban haraji ba akan k'a'ida ba,dik shekara saimunkai ladar tatacciyar Zuma da madara had'e da nono,, basu maida rayuwar bawa komai ba face bayinsu mak'ask'astansu bayi maza da mata ba adadi wad'anda suka rasa rayukansu saboda tsananin azabar hukuncin sarauniya Marwa kuma sarki bayacewa komai,, wannan yankin namu zaniyacemaka bamusan komai ba na cigaban rayuwa muna rayuwa né cikin wahala azaba dakuma k'uncin rayuwa sau d'aya nata'ba zuwa k'asar JAMNAZ naga yanda talakawan k'asar ke rayuwa cikin jin dad'i nace inama mune harnayi kwad'ayin mukoma can dazama abbana yace aa kuma yaman kashedi da karnabari kowa yaji maganar saboda tsoron hukuncin Marwa,, tana kawowa nan tai shuru kanta ak'asa,,,....
Kallonta yai cikin 'bacin rai yace ""kuma haryanzu ba'asami wanda yagayawa Sarki ba"" d'agowa tai tana murmuahi tace wama zaiyi yarda yai wannan d'anyen aikin koma angayamasa bakomai zaiyiba kuma idan Marwa ko mahaifiyarta sukaji wallahi ko kasheka zasuyi,, hmmm.....!!! ya nisa Allah shi kyauta takar'ba da ameeen,'....
Sunzo gun Mai shagon danhaka yasayi ledar ta juyemasa nonon sannan ta juya zata wuce gida HUNAYYA yakira sunanta sai tadawo yakalleta yace ""to kinbani labarin Marwa amma bakibani naki labarin ba"" murmushi tai tace ""gobé kazo zanbaka"" tana fad'ar haka tajuya tawuce abunta,, tsaye yai yana kallonta har ta'bace masa sannan yajuya yawuce gida saifaman murmushi yake shikad'ai ahanya a'bangare d'aya kuma haushi da takaicin hali irinna Marwa da amminsa yake kuma tabbas yad'auki alk'awarin gyara mulkin kama karyanda suke gudanarwa a wannan yankin, '....
Yana isa sashensa yawuce yai wanka yacanja kaya sannan yafito yaci abinci kuma yasha nonon da HUNAYYA tabashi,, zaune yake à falo shikad'ai yana waya da k'annensa inda suke fad'amasa irin mulkinda mama keyi agida da tsafe tsafen da takeyi, sunjima suna waya daga bisani sukai sallama nan yatashi yawuce d'akin humair,, koda yashiga himair na zaune yanashan 'ya'yan itatuwa k'arasawa yai yazauna sunasha atare humair yakallesa yace ""yarima wai inakaje yau ne sarauniya Marwa ta aikomaka da zuma bakanan kuma tazo da kanta bada jimawa ba amma bata gankaba"" murmushi yai yace mezanmata take nemana inacan ruga,, jin yace ruga yasa ya juyo ya kallesa yace ""badai gidansu yarinyarnan ba"" Eh can miye kainifa Allah santa nake kuma aurenta nakeso nai,, wani kallo humair yamasa sannan yace ""BARKIN'DO kasan mekake fad'akuwa to idanma santa kake marwa kuma ya zakayi da ita karfa ka manta Marwa 'yaruwarka ce kuma itace za'bin iyayenka sannan gata jinin sarauta ce ita sa'banin waccan datake baiwarka kuma"" juyowa yai yakalleshi yace kamardai yanda ka fad'a Marwa za'bin iyayenace wannan kuma za'binace sannan idandai har bazaka tofaman yawun albarka ba to kawai kaman shuru,, hmm shikenan Allah ya sanya alkhairi yace ""ameeeeeen haba kokaifa"" yai dariya sukacigaba da shan 'ya'yan itatuwansu suna fira,,,......
******* ******
Sarauniya MARWA ce tsaye sai kai kawo take acikin lambu wani hadiminta ne a durk'ushe agabanta shine wanda ta aika yakaiwa BARKIN'DO zuma bai ganshiba,, cikin tsananin 'bacin rai takallesa tace ""yau kimanin kwana biyu kenan yarima baya zama gida narasa ina yake zuwa sannan ku kuma kunkasa ganoman ina yake zuwa to miye amfaninku"" yaron dake durk'ushe agabanta yace ""Allah ya huci zuciyar sarauniya yarimafa Ruga yake zuwa saidai bansan gun wa yakezuwa ba"" dasauri ta kallesa tace tabbas inabuk'atar sanin inda yake zuwa daga yanzu har izuwa lokacinda zaikoma inasan kudinga bibiyarsa amma à 'boye fatan kaji abinda nafad'a ""angama sarauniya yanda kikace haka za'ayi"" shikenan tashi ka wuce,, nan yaron yawuce itakuma ta zauna tana tana tinanin mafita akan yarima BARKIN'DO,'....
Around 8:15am Hunayya takammala aikinta suna zaune falo à k'asa tana jiran fitowar BARKIN'DO domin tashiga tak'arasa aikinta,, saikusan 8:45am sannan yafito nan suka duk'a sunakwasar gaisuwa cikin sakin fuska yake amsa Masu nan yawuce domin karyawa,, dasauri Hunayya taje domin zubamasa kallonta yadingayi yana murmushi shidai komai nata birgeshi yake hartagama zuba masa baimasaniba yananan yana kallonta saida tace ""Allah yajima da ranka yarima angama komai zaka iyafara ci"" sannan fa yadawo hayyacinsa,, ahankali yad'auke idanunsa daga kallonta yafara cin abinci hartafara tafiya zuwa uwar d'aki domin kammala aikinta d'agowa yai ahankali yakira sunanta tajuyo sannan yace ""idan kinkammala aikinki kizo inasan magana dake"" to tace sannan tawuce, '....
Bayan takammala tafito ta tarardashi a falo yana waya,, zama tai tanajiransa har yagama sannan yajuyo ya kalleta cikin sakin fuska sannan yace......
🏃♀🏃♀🏃♀'''Muje zuwa '''
'''AUFANA for life '''🌷🌷🌷*
*I.W.A*🖊