[13/8/2018]
🌷 *BARKIN'DO*🌷
*[ Very interesting story ]*
*Story & Writing -By AUFANA*✍
✨✨ *Devoted to - ALL FULANI'S IN THE WORLD*✨✨
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*📚®
*{ onward togather}**Page 15~16*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
BARKIN'DO nazaune a falonsa sai humair yakirasa awaya banji abunda yafad'a masa ba kawai ganinai BARKIN'DO yamik'e tsaye dak'arfi yace WHATT.....!!! humair dagaske kake shikenan je kafito da moto ganin zuwa yanzu,, cikin sauri yasaka rigarsa da takalma sannan yad'auki wayarsa yafita,'.......
Abakin gate yasameshi nan yabd'e marfin drinving sit inda humair yake azaune yace ""fito nai drinving dakaina"" ba musu yafito yazagaya yashiga shikuma yashiga ya tada suka wuce,, masarautar DUMNA suka dosa gudu yake tamkar zasu tashi sama ne har suka isa garin direct Rugarsu hunayya yadosa,'....
Koda suka isa magrib takawo jiki humair yaso yajira sui sallah amma dayai masa magana ko kallonsa baiyiba belle yakar'bamasa,, gabansa ne yafad'i dibb alokacinda ya hango gidansu hunayya gabad'aya yakoma turd'aya dasauri yai parking sannan yafito yanak'aremasa kallo tamkar ma bagida bane à da,,,.....
Zagayawa yai inda yahango wani mutum nan yamasa sallama sannan yatambayesa inasu Baffajo suke yanzu nan mutumin yashaidamasa yana gidan d'anuwansa,,kasancewar baisan gidan ba yasa yace dan Allah yakaisu gidan idan baitakurasa ba mutumin kuwa yace bakomai suje nan suka shiga mota yana nunamasa hanya har suka kai k'ofar gidan,, fitowa sukai mutumin yashiga yai sallama da modibbo k'anen baffajo atare suka fito nan suka gaisa BARKIN'DO yadubesa sannan yace ""Abba nasan bakasanni ba sunana Abdul-jabbar yariman masarautar jamnaz"" sunajin yafad'i haka sukai sauri suka risina suna gaidashi cikin murmushi yace su tashi nan yacigaba da magana ""Abba nine wanda sarauniya Marwa tadaki Abba da hunayya akansa,, dan Allah kuyi hak'uri wallahi bansan haka tafaru ba"" kwallah yaga nazuba acikin idanun modibbo hannun BARKIN'DO yaja suka shiga cikin gidan wani d'aki yashiga dashi,, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un....kalmarda yafad'a kenan ganin irin halinda baffajo yake ciki,, kwallah naga nafita acikin idanun BARKIN'DO ahankali yad'ago yakalli modibbo yace ""Abba yanzu marwa ce tayiya Abba haka"" kwallah nafita à idon modibbo yace ""Wallahi itace itace agaban kowa inakallo hunayya na kallo bahalin mucecesu,, hunayya tai kuka tai kuka kamar ranta yafit..."" kuka yaci k'arfinsa yakasa k'arsawa,, BARKIN'DO yashare kwallarda suka zubomasa yace ""kunje asibiti"" aa bamuje saboda rashin abunda zamukaisa dashi amma dai anamasa na nan gida,, ""Abba mutum yanacikin irin wannan hali za'atsaya yin wani maganin gargajiya"" murmushi yai sannan yace yarima bamuda halin da zamuje birni harmukaishi asibiti na gargajiyan shima dakyar akeyinsa,, hmm...!!! yanisa shikenan Abba nizankaisa dakaina zamuje masallaci sai kushirya kamin mudawo"" cikin tsananin jin dad'i baffajo yarisina yanafad'in mungode mungode sosai yarima Allah yabiyamaka dikkanin buk'atunka,, cikin murmushi BARKIN'DO yace "ameen" nan suka wuce masallaci domin yin sallah,'.....
Bayan dawo daga sallah ne suna zaune à k'ofar gidan sunajiran fitowarsu modibbo saiga hunayya da k'awarta sunzo zasu shiga gida,, kallon kallo sukai ita da BARKIN'DO dasauri tajuya tasha kunu suka wuce cikin gida,, mamaki ne yakamata ganin anfito da mahaifinta akawuce dashi waje binsu tai dasauri saitaga ansakashi acikin motarsu BARKIN'DO,, cikin masifa tazo gun BARKIN'DO tace inazaka kaimin mahaifina bayan kungama wulak'antamu agaban jama'a yanzu kuma so kake tazo tarabamu da duniyar baki d'ai cikin kuka take magana narok'ek'eka kafita acikin rayuwata kakyaleni kamanta dani dan Allah narok'ek'e,, kwallah yake zubarwa yakasa cemata komai tsawa modibbo yadakamata ""haba bingel wannan wane irin shashanci ne kinacikin hayyacinki kuwa idan laifine ai bashi yaimaki ba maza wuce cikin gida"" badan tasoba tawuce,, BARKIN'DO kasa cewa komai yai saibintama yai da kallo,, bayan anahirya komai su modibbo suka fito domin suwuce, ja'b'bo matar modibbo da hunayya da k'awarta nasare ne suka rako su har gun mota hunayya kuka take inna ja'b'bo na rarrashinta,, modibbo yashiga tareda d'ansa bommawa nan humair shima yashiga gaba sannan BARKIN'DO yashiga yatada sukabar rugar,, saida suka'bacemata tadaina hangosu sannan takoma cikin gida,,,....
Sai 12:00pm sannan suka iso garin Jamnaz,, wata shahararriyar hôspital suka wuce ganin yanayinda baffajo yake ciki yasa nantake akabashi taimakon gaggawa,, ganin komai yazama normal yasa BARKIN'DO yafita abinci yaje yasiyowa su. Modibbo aifa nan suka dinga zuba k'auyanci humair sai dariya yake,'....
Saikusan 12:15am sannan akafitoda baffajo izuwa d'akin hutu,, bayan sunje sungansa nan doctor yace yanasan ganin BARKIN'DO à office d'insa baiko tsayaba yaje,, sallama tareda shiga office d'in yazauna bayan Sun gaisa ne doctor yace ""yarima azahririn gaskiya bazan 'boyemaka ba bawan Allah nan fa k'afarsa tasami matsala wallahi bazamu iya aikintaba aikin yafi k'arfin mu amma akwai wani consulter dayakezuwa nan baturene d'ank'asar jamany idan yazo shi zai'iyayin aikinta amma mukam nan gaskiya bamuda kwararrun likitocinda zasuyi aikin"" hmm...!!! BARKIN'DO yanumfasa shikenan doctor yaushene shi consulter d'in yakezuwa saboda muzama ready dayazo kawai opération d'in zaayi ""eh to yanzuwa ne dik k'arshen wata yanzu kaga yau muna 27 saura 3days kenan Amman idan yagadama gobé ma saiyazo dikdai sanda yazo zansanardakai karka damu yarima kai ai namune mukataimakawa banza belle kai"" murmushi yai yace nagode sosai dan Allah doctor kutaimaka kubashi kulawa kan doctor d'in yazo,, "karkadamu yarima insha Allah zamuyi iya namu k'ok'ari"" shikenan nizankoma,, nan sukai musabaha sannan yafita,'....
Dakin yakoma haryanzu bacci yake zama yai kusa da humair yanafad'amasa abunda doctor yace saiyaji wayarsa na k'ara hannu yasaka yacirota yana duba kan screen d'in atsorace yazaro idanunsa tareda fad'in yaasalam,, kallonsa humair yai yace waye yakiraka ""mai martaba ne"" yafad'a tareda amsa kiran,, cikin ladabi da biyayya yai sallama jin balbalin masifar da yakemasa yasashi yin shuru yana saurarensa can saiyace ""Allah ya huci zuciyarka ganinan zuwa"" jin shuru alamun yakatse wayar yasa shima yad'auke tasa daga kunnensa,, humair yakallesa yace mekefaruwa ne ""mai martaba ke buk'atar ganina yanzu danhaka yanzu kai zaka tsaya anan kamin nadawo sannan kawuce gida"" shikenan saikadawo,, tashiyai yaje gunsu modibbo yacemasu zaije gida yadawo sannan yawuce,'.....
Yana isa gida direct falon mai martaba yawuce,, koda yashiga kuwa gimbiya laila nazaune agefe tana rik'e da marwa daketa faman kuka falon yai tsitt sai sheshekar kukanta kakeji yayinda maimartaba kefaman zagaya tsakiyar falon sai yaje yadawo,,,....
Sallama yai tareda shiga ciki jikinsa dik yai sanyi ganin tsananin 'bacin rai afuskar mahaifinsa.........
*Da babu gwanda akwai kuyi manage da wannan banida lafiya ne 😫 idan na warke zanmaku dayawa insha Allah*😔
🏃♀🏃♀🏃♀'''Muje zuwa'''
'''AUFANA for life'''🌷🌷🌷
*I.W.A*🖊