[ 5/9/2018 ]
🌷 *BARKIN'DO*🌷
*[ very interesting story ]*
*Story & Writing - By AUFANA*✍
✨✨ *Devoted to - ALL FULANI'S IN THE WORLD*✨✨
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION* ®
*[ onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of bests,, our inks are melodious and dropping a kinder lights to readers }*
'''THE PEN OF LOVE 😘HERT TORCHING 💖TEAR OF SORROWS 😭CURDLES 😊GIGGLES 😁AND MARRIEGE THINK 💑'''
*JUST GIVE US FOLLOW.....*✔*Page 19~20*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Fada ta cika fall da mutanen gidan tindaga hadimai bayi har izuwa masu gidan kowa jiran yake yaji abinda yasa aka kirashi,'....
Jakadiya tafito tsakiyar fadar tana dariya nan ta rangad'a gud'a sannan ta d'aga rigar tasake rangad'a gud'a ""Ahayye nanayee dole ne nai dariya narangad'a gud'a, yaudai Sarauniya MARWA 'ya agun sarki Hamid takawo budurcinta gidan mijinta wato Yarima ABDUL-JABBAR d'a agun sarki Abdul-k'adir jika gun sarki Abduk-malik wato BARKIN'DO"" tana gama fad'a nan sauran jakadiyoyin dake gidan suma suka d'auki gud'a,,murna agun Mai martaba baamagana nan shima yatashi tsaye yafara magana "hak'ik'a wannan abun farinciki ne agaremu kuma kamar yanda kuka sani al'adace ta wannan masarautar dik yarinyarda takai budurcinta gidan mijinta sai anmata gagarumar kyauta dan haka ni sarki nabawa 'yata sarauniya Marwa kyautar dawaki guda biyar had'e da hadimai Mata goma sha biyar saikuma Manyan alkyabbu guda hud'u tareda gidan gona domin shuka dik wani kalan 'ya'yan itatuwa datake buk'ata" yana gamawa jakadiya tad'auki gud'a, nandai sukaita nuna farincikinsu daga bisani kowa ya watse aka koma bakin aiki,,,..
Yau kwanan marwa hud'u a asibiti tawarware sosai dan haka suka sallameta tareda kafa mata dokoki,'...
Kwance yake yana bacci sai yaji kamar ana kiransa acikin baccin, bud'e idanunsa yai cikin magagin bacci Marwa yagani tsaye agabansa tana faman masifa "haba kaikan wannan wane irin bacci ne tin d'azu yaran nan suke jiranka ka farka su gyara d'akin amma kak'i narasa gane abunda kake nufi ko nice kake nufin nagyara maka ne to wallahi inma haka kakenufi kama sauya tinaninka dan wallahi bazaiyiwu ba ga hadimai birjit sannan kace ni zanmaka aiki" kallonta yake cikin mamaki kamar yamata magana kawai sai yakyaleta, tashi yai yashige toilet yabarta nan tsaye, wani uban tsaki tai sannan tafita tace da hadimanta su shigo sufara aikinsu,,,...
Koda yafito kawai yaga yaran suna aiki ransa ya'baci sosai wato shidai d'akinsa bayada sirri, fita yai yawuce sashen Hajiya acan yakarya Hajiya sai tsokanarsa take wai girkinta akwai dad'i dikda yayi aure amma yakasa hak'ura dashi hhhh Lol, '....
****** ******
Yau kimanin sati uku kenan da bikin BARKIN'DO da Marwa,,,...
Zaune suke shi da humair suna tattaunawa akan matsalar ciwon Baffajo Abun yana damun humair sosai ganin irin halinda yake ciki gashi kuma har yanzu consulter d'inda akace zaizo baizoba nandai sukaita jimamin abun dagabisani suka wuce cikin gida kasancewar cikin gidan gona suke,,,...
Bayan sunshiga cikin gida BARKIN'DO baishiga sashensu ba saikunsan 8:15pm amma koda yashiga kuma baiga Marwa ba ganin haka yasa yatambayi hadimanta nan suka shaida masa ta fita tin da rana tareda k'awayenta dasukazo, mamaki ne yacikasa hartanada ikon da zata fita batareda ta nemi izinansa ba lallai yarinyar nan inbai d'auki mataki akanta ba rainasa zatayi,,d'akinsa yawuce yanata zancen zuci,'..
Saikusan 10:30pm sannan Marwa tadawo yaji shigowarta amma yakyaleta yai kwanciyarsa, dasafe Ma hadimanta suka had'amasa breakfast sannan suka gyara d'akinsa da gidan gabad'aya,, bayan yai wanka yashirya yafita batareda yace da'ita komai ba,'..
Ahalin yanzu zan iya cewa zaman doya da manja akeyi tsakanin Marwa da BARKIN'DO sai idan tana buk'atarsa sannan take kulasa shikuwa ko kallo bata isheshiba daya biyamata buk'atarta shima yajishi daram shikenan, fitarda takeyi kuma bata fasa ba atinaninta BARKIN'DO baisaniba,, yauma dai kamar kullum kasancewar baya fita ko'ina zaune yake a sashen Ummi suna fira dasu meesha kawai yatasha yafita izuwa sashensu,'...
Shiga yai tareda bud'e k'ofar falour kamar kullum hadimai na aikinsu Marwa kuma nazaune tanashan iska wasu mata su hud'u suna gefenta kayan dake jikinsu kad'ai sun'isheka amsar tambayar ko suwaye,,kallo d'aya yaimasu yajuya yakama hanyar d'akinsa, ganinsa yasa sukai saurin d'aukan riga abaya suka rufe jikinsu tareda gaidashi shikuwa ko kallonsu baiyiba balle yakar'ba masu har yashige ciki,,,...
Tsaki d'aya daga cikinsu tai wacca naji Marwa takira da sweet khady sannan tace ""amma Marwa wannan gyaii d'in yamugun raina mutane me yake ji dashi me yake tak'ama dashi har agaidasa yai banza damutane"" hmm...!!! ta nisa wallahi khadyy kema kinsan badanda nake sansa ba da tini nai maganinsa, wata uwar harara suka zabga mata lallai kuwa kinada aiki babba to mema yafi sauran mazan kinada fa dubunsa wad'anda suka fisa komai zaki wani tsaya kina wahalarda kanki,, hmm bakwa ganewa ne mucigaba da abunda yatara mu mu ajiye wannan zancen,,,...
BARKIN'DO ne zaune acikin lambun Ummi yana hutawa sai wayarsa tai k'ara nan yasaka hannunsa yaciro sannan yad'aga yakara a kunnensa,,cikin murmushi yafara magana ""Likita bokan turai nan suka gaisa yake shaida masa doctor d'inda suke jira wato cinsulter yasauka jiya gobe insha Allah zai iso JAMNAZ"" jin wannan maganar bak'aramin farinciki BARKIN'DO yai ba nan yafad'amasa dik yanda tsarin likitan yake nanyai godiya sosai sannan sukai sallama,'...
Bayan sunyi sallama sai yakira humair yafad'amasa sannan yace yazo yakar'bi ATM card d'insa dik wani abu da za'abuk'ata yacira kawai yayi, murmushi humair yai yace ""angama ango asha amarci lafiya"" yafad'a cikin tsokana hararansa yai kamar afili yake yanaganinsa ""wallahi d'anuwa natakura sosai wai ni zaayiwa kulle kaman wata Mace"" murmushi humair yai yace kayi hak'uri d'anuwana iyaye dole amasu biyayya kuma ma ai lokacinda ya d'ibarmaka yakusa zuwa ka k'ara hak'uri nesa tazo kusa ai,, shikenan yanzu kai k'ok'ari gobe ku gana da likitan saboda asamu ayi aikin da wuri, "insha Allah zanyi iya nawa k'ok'ari Allah dai yasa adace saboda gaskita bawan Allah nan yanajin jiki sosai"" ameen ya kar'ba sannan yai murmushi yace d'anuwa gaskiya nayi missing d'in my HUNAYYA inaso naganta nasan itama tai missing d'ina saidai tanada kunya sosai nasan bazata iya nunawa ba saidai tai ta 'boyonsa acikin ranta,, murmushi humair yai yace "karka damu ai kakusa ganinta idan anyi operation d'in angama yaji sauki zanje rugarsu nad'aukoma ita insha Allah"" murmushi yai cikin jin dad'i yace Allah yasa adace yasa ayi a sa'a suka kar'ba da ameen sannan sukai sallama, '....
Bayan sunyi sallama nan yacigaba da zama harkusan magrib sannan yawuce masallaci,,,...
Aranarda doctor d'in yazo aranar suka sami ganinsa harsukai magana ganin irin halinda Baffajo yake ciki yasa ya tausaya masa kuma yace ashirya gobe zasu shiga tiater dashi,,,...
Dik wani abunda za'a buk'ata humair yasiya harma Norse's d'in gani suke kamar ma abun harda 'barna,, around 12:00pm aka shiga tiater da Baffajo aikwa tinda aka shiga su Abba modibbo suka duk'ufa suna kaiwa Allah kukansu hakama su HUNAYYA tinda aka Kira aka shaidamasu anshiga tiater d'in sukafara nafilfili musamman ita wacca kullum cikin rok'arwa mahaifinta sauk'i take gun ubangiji,'...
Alhamdulillah anfito da Baffajo d'akin tiater izuwa d'akin hutu yanzukam farkawarsa kawai ake jira,, cikin ikon Allah kuwa ya farka ganin ya farka yasa humair yaje yakirawo doctors d'in,, dik wani abu daya dace sunmasa Alhmdllh komai normal bawata matsala Sun dudduba ko'ina lafiya bamatsala aikwa murna agunsu Modibbo harma dasu Hunayya bata misaltuwa sunso abashi suji muryarsa amma hakan bazaiyiwu ba saboda baigama wartsakewa ba,'...
Yau kimanin kwana biyar kenan dayiwa Baffajo operation Alhmdllh yasamu ssauk'i sosai likitocin sai murna suke sunci nasara dikda bashine nafarko dasuka tta'bayiwa irin wannan aikin ba amma nashi yafi basu tsoro da wahala,,,...
Yaudai humair yace zaicikawa BARKIN'DO alk'awarin da yamasa na d'akko Hunayya,,,...
Wani Abun birgewa kuma yaune BARKIN'DO zai fara fita, tin da humair yafad'amasa yana kan hanyar masarautar Dumna izuwa rugarsu Hunayya domin d'aukosu ita da Inna yafara shirin tarbanta,'....
Wanka yai namusamman cikin shiga irinta alfarma yai kyau matuk'a nan yasaka su meerah sumasa girki had'ad'd'e irin na alfarma......
🏃♀🏃♀'''Muje zuwa '''
'''AUFANA for life'''🌷🌷
*I.W.A*🖊